Tuesday, 28 May 2019

Akwai Abin Al'ajabi da ban Mamaki Mai Tarin Yawa game da Rayuwar Wannan Dabba Wato Tururuwa

Tura Wannan Zuwa Ga
Akwai wani gidan zuma ko gara ko cinnaka (ko tururuwa) ba kawai a birkice suke rayuwa ba, a'a suna da tsari da bangare-bangare daban-daban. Suna da sarauniya, sojoji, maza, da kuma ma'aikata.

Tururuwa



Marubuci: Farouk Abdullahi Tukuntawa

Watakila ka taba ganin wata gara ko cinnaka mai girman baya ko kuma wata zuma dake gaba sauran garken na biye da ita, sarauniya kenan. Ita ce ta kafa gidan, aikin ta saka kwai. Idan sarauniya ta mutu akan zabi daya daga cikin ma'aikata ai ta bata wani irin abinci na sarauta har ta canza.


Mazan gidan basu wani aiki face idan ana bukatar kwayaye suyi ma sarauniyar barbara. Shi yasa ma a gidan zuma akan kore su daga gidan in abinci yayi karanci, sai su fito su salwanta gaban teburin mai rake ko abarba ko wani wuri can.


Ma'aikata su suka fi yawa,  kusan duk cinnaku, ko zuma ko garar da kake yawan gani to su ne. Mata ne da ba su haihuwa kuma duk suke aikace-aikacen gidan kamar nemo abinci, kula da kwayaye, ciyar da sarauniya da kananan yara. Ma'aikatan gara da wasu cinnaku sukan yi noman wasu kananan abubuwa da ake kira fungi da turanci.


Su ko sojoji aikinsu shine kare gida daga farmaki, sukan kula da kofar shiga gidan don gudun kada wani abokin gaba ya shiga. Akan gane duk wanda ba dan gida ba ta kamshi, don sarauniya kan fitar da wani turare da kowa ke shafawa.


Su kanyi magana da juna, cinnaku na magana ta fannin hada kansu (kana iya ganin haka in ka lura da su), zuma kuma takan fita ta gano wurin da abinci yake ta dawo ta ma 'yan'uwanta bayani ta fannin wani rawa da ke bayyana nisa da bangaren da abincin yake.


Hausawa na cewa idan gara ta nemi ta lalace sai tai fuka-fuki, a zahiri kuwa duk gara ko cinnaka mai fiffike matashiyar gimbiya ce dake fitowa don tayi barbara ta kafa sabuwar alkaryarta.


Wannan ilimi masana kimiyya sun fahimce shine bayan dogon bincike da bin kwakkwafin wadannan kwarin, amma in ba mu manta ba a Alqur'ani an kawo zancen wata tururuwa da tayi yi wa 'yan uwanta magana akan su kauce don kada rundunar annabi sulaiman ta taka su (sura ta 27 aya ta 18).


Wannan shine yadda abun yake.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user