Jarumi Adam A. Zango tare da Matar sa
Jarumin dai ya rubuta sakon "Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana da rai da lafiya".
Sharhi
Bayan fitar wannan sakon a karkashin hotan nan take wasu daga cikin mabiyan jarumin su fara yi masa sharhi akan hotan.
Matar Jarumi Adam A. Zango
Wasu daga cikin masoyan nasa sun taya shi murna da kuma yi masa fatan Alkhairi.
Sharhi
Yayin da wasu daga cikin mabiyan nasa sukai caa akan hotan matar jarumin , suna cewa "Bai dace kana saka hotan matar ka a kafafen sadarwa ba , anya kana kishin ta kuwa".
Sharhi
Wadannan wasu ne daga cikin hotan jarumin da matar sa.
Jarumi Adam A. Zango da Matar sa
Kamar yadda ɗaƴa daga cikin wakilan Muryar Hausa24 ya shaida mana Cewa "An ɗaura auren Jarumin da Matar sa a watan da ya gabata, sai dai auren bai samu damar halartar wasu daga cikin jaruman Kannywood da kuma sauran ɗimbin masoyan jarumin".
Hakan ya faru ne sakamakon abin da jarumin yayi kafin Auren nasa.
Jarumi Adam A. Zango da Matar sa
Kwatsam sai akaji labarin an ɗaura auren jarumin , sai dai hakan bai yiwa mutane da dama daɗi ba , musamman waɗanda suka ƙwallafa rai akai ciki harda Mawaƙa, 'yan film , Hip Hop da sauran masoyan jarumin .
Sai dai kuma an samu halartar wasu daga cikin makusantan jarumin ciki harda 'yan uwa da abokanan arziki da kuma abokanan sana'arsa.
Ana hasashen cewa "Ɗage bikin jarumin hakan baya rasa nasaba da yanayi na tsaro kasancewar sa jarumi, Mawaƙi kuma shahararre a masana'antar Kannywood".
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode