Tarihi
Korau an ce Musulmi ne wanda ake yi masa laƙabin Muhammadu Korau. Ya fito ne daga ƙabilar Wangarawa da ke rusasshiyar daular Mali. Shi Korau, tare da jama'arsa, sun mamaye ƙasar 'Yandoto, wadda ke Katsina-Laka, a farkon ƙarni na goma sha biyar. Daga nan kuma suka gangaro Katsina-Jigawa, suka yaƙi Sarkin Katsina da ke birnin Katsina mai suna Jibda Yaƙi Sanau. Bayan cin nasara yaƙi, sai Korau ya ɗare karagar mulkin Katsina ya zama Sarkin Katsina na farko a tsatson Wangarawa.
Kamar yadda bayani ya gabata cewa, Korau ne ya gina gidan Sarkin Katsina na yanzu da ke Cikin Gida, ya zauna a ciki har ƙarshen rayuwarsa. Haka 'ya'ya da jikoki waɗanda suka yi Sarautar Katsina a daular Wangarawa, su ma a nan suka zauna tun daga shi Korau wanda ya yi zamani daga 1348-1398, har dai a ƙarshen mulkin Wangarawa a shekara ta 1807.
An yi Sarakunan Katsina na Wangarawa waken guda ashirin da tara, kuma duk a nan Gidan Korau wanda ke Cikin Gida, suka yi Sarauta.
Muhimmai daga cikin waɗannan Sarakuna na Haɓe zuriyar Wangarawa, da suka yi mulkin Katsina, daga nan Gidan Korau da ke Cikin Gida, akwai Korau shi kansa.
Akwai Ali Murabit, Ali Karyagiwa, Ibrahim Maje, Uban Yara, Janhazo, Gunawa Agwaragi, Sarki Gozo, Bawa Ɗangiwa, Maremawa, Magaji Halidu, da sauransu.
A lokacin mulkin Korau (1348-1398) aka gina gidan Sarkin Katsina da ke Cikin Gida, a lokacinsa ne aka tabbatar da kafuwar ƙasar Katsina wadda ta haɗa da Karofi, 'Yanɗaka Durɓi, da sauran su, mai babban birni a Katsina, mai fada a Cikin Gida. Ali Murabit (1452-1475) da ya biyo baya, shi ya sa aka gina ganuwar Ƙofar Soro, wadda ta zagaye Gidan Korau, wadda aka yi wa ƙofofi guda biyu, Ƙofar Soro ta shiga fadar Sarki, da Ƙofar Bai, ta bayan gidan Sarki.
Tun daga zamanin Ali Murabit ne aka fara samun kafuwar Cikin Gida. Daga baya kuma, Ali Murabit, ya fara gina babbar ganuwar Katsina, wadda ta zagaye duk unguwannin da ke cikin birni Katsina.
Amma ba a ƙarasa ginin ba sai zamanin Ibrahim Maje (1599-1613). Shi Ibrahim Maje baya ga ci gaba da ginin ganuwa, ya kuma ƙarfafa addinin Musulinci a ƙasar Katsina baki ɗayanta.
Shi kuma Ali Karyagiwa (1475-1525) wanda ya yi mulki kafin Ibrahim Maje, ya ƙara faɗaɗa ƙasar Katsina, inda aka kai yaƙi har Kuyambana da Birnin Gwari da Zamfara, don ƙara samun ƙasar mulki. Umurnin yin hakan ya fito ne daga fadar Cikin Gida.
Kuma a zamanin Karyagiwa aka karɓi baƙuncin wani malami mai suna Muhammad Bin Ahmad Al-Tszakht, wanda aka fi sani da Ɗantakun. Shi Ɗantakun, ya zama babban alƙali a Katsina.
Lokacin mulkin Uban Yara da Janhazo (1708-1740) Katsina ta tsunduma cikin yaƙi da maƙwabtanta, musamman ma Gobir da Kano.
A zamaninsa ne martabar malaman birnin Katsina, irin su Abu Abdullahi Bin Ghumehu Bin Nuh Al-Barnawi, Al-Katsinawi (Ɗanmasani), da kuma ɗayan malamin Muhammadu Bin Al-Sabbagh, Al-Katsinawi(Ɗanmasani), ta ɗaukaka, wato waɗannan malamai suka shahara a ko'ina a duniyar lokacinsu.
Shi kuma Gunawa Agwaragi (1779-1788), a lokacinsa aka dinga samunhamayyar gadon Sarauta tsakanin 'ya'ya da jikoki na Sarakunan da suka gabata a nan Cikin Gida, wanda har abin ya kai ga yaƙin basasa.
Sarki Goza (1788-1802), shi kuma ya haɗu da fitinu na 'yan Cikin Birnin Katsina da na 'yan Cikin Gida. Haka aka yi ta yi har Bawa Ɗangiwa (1802-1804) ya zo, wanda shi ma ya ci gaba da fuskantar wannan fitina.
Su 'yan Cikin Birni waɗanda ke yammacin Cikin Gida, 'yan kasuwa ne attajirai da malamai masu ɗinbin ilmi da dukiya. Su kuma 'yan Cikin Gida, fadawan Sarki ne da barorinsa, bayinsa da barwansa da mayaƙansa. Wannan bambancin shi ya kawo kallon raini tsakani sassan biyu.
Baya ga wannan sai ga wata babbar sabuwar matsala ta fuskanci Bawa Ɗangiwa, mai fada a Cikin Gida. Matsalar kuwa ita ce ta jihadi, wanda ya ɓullo wa Katsina da masarautarta, a ƙarƙashin jagorancin Mallam Ummarum Dallaje da Malam Muhammadu Na'Alhaji da Mallam Ummaru Dumyawa.
Waɗannan Mujahidai sun karɓo tutar ƙaddamar da jihadi daga Sakkwato ga ƙasar Katsina baki ɗayanta, da masarautar Katsina ɗin da ke Cikin Gida. An ci gaba da yin yaƙi tsakanin mayaƙan jama'a na masu jihadi da mayaƙan Sarakunan Katsina har Allah ya yi wa Ɗangiwa rasuwa. Wanda ya karɓi ragamar mulki da ci gaba da yaƙi, shi ne Muhammadu Maremawa (1804-1805), wanda a wata gwabzawar da aka yi a Iyatawa, aka kashe shi. Sai Magaji Halidu ya karɓi sarauta, aka ci gaba da yaƙi.
A shekarar 1807, mayaƙan jama'a sun ci Katsina da yaƙi, inda shi Magaji Halidu (1805-1807) ya tsere zuwa Dankama daga can sai Damagaram. Shi kuma Ummarun Dallaje (1807), wanda shi ne jagaban yaƙi ya shige gidan Sarautar gidan Korau da ke Cikin Gida, ya zama Sarkin Katsina na farko a daular Usman Ɗanfodiyo, a kuma zuriyar Fulani na Dallazawa.
Daga lokacin da Ummaru Dallaje ya shiga Gidan Korau da ke Cikin Gidan, daga nan ne mulkin Dallazawa ya fara, a shekarar 1807 wanda ya kai ƙarshe a shekarar 1906.
Ummarun Dallaje, ya jaddada addinin Musulinci a ƙasar Katsina baki ɗaya, ya kafa mulki irin na tarayya, a inda aka ba malam Muhammadu Na'Alhaji kudu maso yamman Katsina a matsayin 'Yanɗakan Katsina, mai fadarsa a Zakka da gidansa na mulki a 'Yantaba da ke cikin birnin Katsina.
Shi kuma malam Ummarun Dumyawa, aka ba shi mulkin arewa maso yammacin Katsina, a matsayin Sarkin Sulluɓawan Katsina, mai fadarsa a Bugaje da kuma gidan Sarautarsa da ke Sulluɓawa ta Ƙofar Guga. Shi kuma Ummarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina gaba ɗayanta, mai babbar fadarsa a Gidan Korau da ke Cikin Gida.
Abubakar Saddiƙu shi ne ya gaji Ummarun Dallaje a shekarar 1835, wanda shi ma, ya zauna, ya yi rayuwarsa a Gidan Korau na Cikin Gida. A zamanin mulkin Saddiƙ, an sami tawaye na Maraɗawa, wato Sarakuman Haɓe na Katsina waɗanda aka ci da yaƙi, suka koma Maraɗi. Su waɗannan Maraɗawa, sun ƙuduri aniyar dawowa Katsina, da nufin karɓar mulki daga hannun Fulani Dallazawa.
Wannan shi ya kawo yaƙe-yaƙe a tsakanin mayaƙan Maraɗawa da mayaƙan Katsina a ƙarƙashin jagorancin Abubakar Saddiƙu tare da taimakon mayaƙan kuma manyan Sarakunan fada, irin su Durɓi Giɗaɗo da Abdu Nadabo, Tarno Gajeren Badde.
Bayan rasuwar Abubakar Saddiƙu, sai Muhammadu Bello ya ɗare karaga a shekarar 1844. Shi ma, a nan Gidan Korau da ke Ciki Gida ya zauna ya yi mulkinsa. A zamanin Bello ɗin ne, aka ƙarfafa harkokin shari'a a Katsina, aka inganta karɓar baƙi malamai da 'yan kasuwa. Muhammadu Bello ya kakkafa sababbin jini a mulkinsa, irin Giɗaɗo, Tarno Gajeren Badde da Abdu Nadabo. Waɗannan mutane, su ne manyan jarumai na Katsina, waɗanda suka dinga fafatawa da Maraɗawa, kuma su ne manyan fadawa masu murɗa zare a fadar Cikin Gida.
Ahmadu Rufa'i (1869-1870) da Ibrahim Muhammadu Bello (1870-1882) su ma, sun yi mulkin Katsina, kuma a nan Gidan Korau na Cikin Gida suka zauna suka rasu a nan.
A zamanin Rufa'i ne, yaƙi da Maraɗawa ya tsananta, har ma ya hana abubuwa na cigaba. Ibrahim Bello ya zama Sarki bayan rasuwar Ahmadu Rufa'i a (1870). Shi ma Ibrahim, ya gaji wannan fitina ta yaƙi da Maraɗawa, a ƙarƙashin su Ɗanmari da Ɗanbaskare.
A zamanin Sarkin Ibrahim ne aka gina ƙofar shiga Cikin Gida, wato Ƙofar Soro, inda aka yi mata gini Inda ake wuchewa ta chikin kofar idan za'a Shiga gidan korau.Bayan rasuwar Ibrahim Bello, sai Musa ya gaji Sarauta a shekarar 1882, wanda shi ma ya yi rayuwarsa a Gidan Korau na Cikin Gida. A zamanin Musa ne mayan dakarun nan na Katsina, kuma manyan fadar Cikin Gida, irin su Durɓi Giɗaɗo da Abdu Nadabo suka rasu.
Abubakar Ibrahim ya gaji Sarauta a shekara ta 1887, wanda shi ma ya zauna a Cikin Gidan Korau na Cikin Gida. Amma Abubakar ba a Gidan Korau ya rasu ba, domin Turawa sun tuɓe shi daga Sarauta, suka tafi da shi Ilorin, a shekarar 1925 aka dawo dashi kano a zamanin sarkin kano Usman Dan Abdullahi maje karofi ,Sarkin katsina abubakar ya rasu a kano a shekarar 1940 zamanin Sarkin Kano Abdullahi bayero. Kamar yadda bayani ya gabata, a zamanin Abubakar ne Turawa Ingilishi suka kama Katsina, koda yake ba a yi yaƙi da su ba.
Bayan tuɓe Abubakar da Turawa suka yi a dalilin rashin fahimtar da ta shiga tsakanin Sarki Abubakar da Turawa, sai Turawan suka tuɓe shi, suka yi masa murabus, suka tafi da shi Ilorin. Sai suka naɗa Muhammadu Yero Sarkin Katsina, wanda shi ma, ya ɗan zauna a Gidan Korau na Cikin Gida, kafin abin da ya sami Abubakar, shi ma ya same shi. Turawa sun tuhume shi da rashin iya aiki wanda a wannan dalili suka tuɓecshi, suka kai shi Lakwaja.
Wannan al'amari ya auku ne a shekara ta 1906. Wannan ne kuma ya kawo ƙarshen mulkin ƙasar Katsina da Dallazawa suka yi daga Gidan Korau na Cikin Gida.
Muhammadu Dikko, ɗan Durɓi Giɗaɗo, ya zama Sarkin Katsina na farko a tsatson Fulani Sulluɓawa. Shi Dikko, Turawa ne suka naɗa shi, ya zama Sarkin Katsina a shekarar 1906, bayan tuɓe Muhammadu Yero da aka yi.
A zamanin Muhammadu Dikko ne aka matso da ƙofar shiga Cikin Gida, wato Ƙofar Soro Inda take a yanzu, aka yi mata ginin dutse da tagogi, aka kuma yi mata bene wanda a Katsina ake kira Soro. Daga nan ne ma, ƙofar ta sami sunan Ƙofar Soro, wato ƙofa mai bene ko soro. Daga baya, an kuma riƙa kiran ƙofar da sunan Kan-Giwa, saboda wannan soron yana kama da kan giwa da aka sani. Ƙofar an sanya mata agogo, wadda a da, take bugawa duk bayan awa guda, wadda ake jin ƙarar bugawar a ko'ina cikin birnin Katsina.
A zaminin Dikko ne, aka gyara filin da ke gaban Kan-Giwa ko Ƙofar Soro, ya zama filin yin jahi ran salla ƙara a ko babba, da kuma yi wa hakimai da jama'ar Katsina da suka taru a wurin jawabi. A yamma da filin aka yi ofishin 'yan doka, wanda ya zama ofishin 'yan sanda a yanzu. A arewa da filin Kan-Giwa ko Ƙofar Soro, aka gina ɗakunan shari'a na Alƙali Babba da Alƙali Ƙarami, wanda kafin wannan lokacin, a zauruka ake yin shari'ar.
An kuma gina sakatariya ta ma'aikatan En'e ta Katsina. A kudu kuwa, da filin na Ƙofar Soro, aka gina ma'aikatar wakshof inda ake yin ƙere-ƙere. A can gaba da ma'aikatar aka gina babban masallacin Juma'a na uku a Katsina. Dikko ya yi gaba ɗayan rayuwarsa a Gidan Korau da ke Cikin Gida, kuma ya rasu a nan a shekarar 1944.
Wanda ya gaji Muhammadu Dikko shi ne ma kamar mahaifinsa, ya zauna a Gidan Korau.
A zamanin Usman Nagogo, an ƙarfafa bayar da ilmin boko da buɗe makarantun boko a birni da ƙauye na faɗin ƙasar Katsina. Sarki Usman Nagogo ya rasu a shekara ta 1981. Wanda ya gaji Sarki Usman, shi ne Muhammadu Kabir Usman a shekara ta 1981. A zamanin mulkin Kabir Usman ne, ƙasar Katsina ta sami Jihar kanta a shekara ta 1987, wanda a dalilin haka, garin Katsina da wurare da dama a Jihar, suka sami ci gaba. Abdulmumin Kabir Usman, shi ya gaji mahaifinsa a matsayin Sarki. Kamar sauran Sarakunan Katsina, shi ma a Gidan Korau na Cikin Gida yake zaune.
Abin lura a nan, game da Gidan Korau na Cikin Gida shi ne, duk ilahirin Sarakunan Katsina, tun daga Haɓe na zuriyar Korau na Wangarawa, har zuwa Fulani Dallazawa, zuwa Fulani Sulluɓawa, dukkaninsu a Gidan Korau ɗin ne suka zauna, suka yi Sarauta, kuma wata ƙila, suka rasu a nan, in ka ɗebe Abubakar Saddiƙu wanda aka tuɓe daga Sarautar Katsina, aka tafi da shi ƙasar Sakkwato, da Abubakar Ibahim da Muhammadu Yero waɗanda Turawa suka tafi sa su wani wuri na daban.
Abin lura na biyu, shi ne, Gidan Korau wanda aka gina a farko-farkon ƙarni na goma sha biyar, yana da wajen shekara dari biyar (500) da ginawa.
Allah ya gafarta wa magabatan mu Ameen.
Source: M.T.SAFANA ARCHIVES

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode