Wednesday, 19 June 2019

RASUWAR SHUGABAN KASAR MISRAH TA GIRGIZA DUNIYA: DAN KISHIN ADDININ ISLAMA YA KWANTA DAMA

Tura Wannan Zuwa Ga
Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji'uun! zuciya ta kadu matuka da samun labarin rasuwar tsohon shugaban kasar Misrah (Egypt) Sheikh Muhammad Morsi.



Muhammad Mursi





Marubuci: Datti Assalafy



Marigayi Muhammad Morsi 'dan kishin Islama ne, babban bango kuma babban jigo a kungiyar 'yan uwa musulmi na duniya, mai ra'ayi irin na sojojin tsohuwar daular Usmaniyyah, malami ne Mahaddacin Al-Qur'ani kayan Allah, yana daya daga cikin manyan 'yan siyasar duniya musulmai da suke rage a duniya wadanda suke iya kalubalantar makirci da sharrin yahudu da nasara.


Kamar yadda na gani a labarai, ance ya rasu yau litinin bayan an gabatar dashi a gaban alkali don cigaba da tuhumar da ake masa akan laifin cin amanar kasa, sai ya yanke jiki ya fadi ya suma, daga bisani mahukuntar Kasar sukace ya mutu


Wannan bawan Allah ya shafe shekaru 6 a gidan yari tun bayan hambarar da gwamnatinsa da Janar Abdel-Fattah Alsisi yayi, gashi dai babu wanda ya kaisu cin amanar kasa tunda hambarar da gwamnati suka yi, amma suka dawo suna zargin wannan bawan Allah da laifin cin amanar kasa saboda kawai yayi adawa da iyayen gidansu turawa makiya addinin Musulunci


Inda ace duniyar yahudu da nasara suna tare da Muhammad Morsi na tabbata sai majalisar dinkin duniya ta fito tace ayi kwakkwaran bincike akan mutuwarsa, domin har ga Allah ni kaina ban yarda da mutuwar wannan bawan Allah haka kawai ba, da kyar imba guba suka shayar dashi ba, saboda basu da wata hujjar da tasa suke tsare dashi tun bayan da suka kifar da gwamnatinsa


Kungiyar 'yan uwa Musulmi (Ikhwanal Muslimina) kungiyace ta siyasa wanda 'yan kishin musulunci suka kafa don kwatawa musulmin duniya 'yancinsu tun bayan kifar da daular Usmaniyyah, hakika ni Datti Assalafiy ban san wata kungiyar siyasa da take da kyakkyawan manufa akan musulunci kamar Ikhwan ba, duk da suna da kura-kurai a tsarin kungiyar amma wallahi alherin kungiyar yafi kuskurenta yawa nesa ba kusa ba, marigayi Muhammad Morsi babban jigo ne a kungiyar Ikhwan


Yanzu dai dukkan manyan jigogin kungiyar Ikhwan an kawar dasu daga doron duniya, dayane kawai ya rage shine Magajin tsohuwar daular islama ta Usmaniyyah, shugaban Kasar Turkiyyah Sheikh Recep Tayyip Erdogan wacce marigayi Sheikh Usman Ghazi ya kafa, kafin cin mutuncin da turawa suka mata ta hannun karen farautarsu Mustapha Kamal Ataturk (L), Ataturk rikekken Bayahude ne a rigar musulunci, mai nuna matsananciyar kiyayya ga Musulunci


Marubuta da dama sunyi jayayya akan batun asalin Mustapha Kamal Ataturk, amma magana mafi inganci Ataturk bayahuden Doenman ne, Doenman kuwa wata darikar Yahudawan Sabbetaians ce, Yahudawa ne da suke Turkiyya, wadanda suke yin shiga da mu'amala tamkar Musulmi, suna kuma amsa sunan Musulmi, amma zukatansu suna da wani abin bautarsu daban wato "Sabbetai Zevi" wani "masihun" 'karya ne da ya bayyana a karni na 17.


Mustapha Kamal Ataturk, ya jefa Turkiya cikin mawuyacin hali, ya ci mutuncin Shari'ar Allah, ya ci mutuncin tsarin shugabanci irin na Khalifanci tare da soke shi a Kasar Turkiyya a ranar 3 ga watan 3 na shekarar 1924, daga bisani ya kori duk wadansu mutane da suke da alaka da daular Usmaniyya.


Bayan haka, Ataturk ya haramta mazhabobin ilimin Islama da makarantun koyon addinin Allah a Turkiyyah, Sannan ya haramta aiki da shari'ar musulunci, ya hana kiran sallah da harcen larabci, kotunan Musulunci duk ya bada umarni aka rufe su


Daga karshe bayan ya gama cin mutuncin addinin Allah sai shima Allah Ya karyashi, mulki ya sake dawowa hannun 'yan kungiyar Ikhwan, wanda har zuwa yau 'dan kungiyar Ikhwan (Recep Tayyip Erdogan) shi ke shugabancin Kasar Turkiyyah, gashi yau ya rasa 'dan uwa abokin gwagwarmaya marigayi Sheikh Muhammad Morsi



Na tsaneka azzalumi shugaban kasar Misrah Abdulfatah Alsisi, duk abinda ya faru a dalilin mutuwar Malami Mahaddacin Al-Qur'ani Maigirma marigayi Sheikh Muhammad Morsi kai ne sila, kuma alhakkin jininsa yana rataye a wuyanka


Ka hambarar da Morsi daga kan kujeran shugabanci wanda a ka'idah kaine ya kamata a zartarwa hukuncin kisa, ka kamashi ka tsare shekaru 6 cur, ka dinga wulakanta kayan Allah Mahaddacin Al-Qur'ani Maigirma a gidan yari


Duk manyan mutanen da suke tare da Mohammad Morsi ka kamasu ka daure a gidan yari ka yanke musu hukuncin kisa, wasu tuni an kashe su, don haka mutuwar Morsi bai zo mana da abin mamaki ba


Muhammad Morsi yace; "da suka tsareni a gidan yari, sai suka hana a bani Al-Qur'ani Maigirma, sun manta cewa na haddace Qur'ani sama da shekaru 40 da suka gabata, bukatata da Qur'ani bai wuce na shafa shi ba.."


Kalmomin Muhammad Morsi kafin a hambarar da gwamnatinsa, yace: "zamu yi raga-raga da duk Kasar data taba ko ta zagi Annabin mu Muhammad (SAW), zamu cigaba da yin mulkin Dimokradiyyah mai kyau, muyi hukunci da Al-Qur'ani da ingantattun Hadisai a matsayin kundin tsarin mulkin mu (Constitution), kuma bamu jin tsoron Turawan yamma akan haka".



"Na tabbata baza su bar ni ba, amma na sadaukar da rayuwa ta ga addinin Musulunci da kuma talakawa na mutanen Misrah, ba'a biyan farashin tsare Musulunci da sauran bayin Allah da kudi sai dai da rai da jini, bana nadamar abinda nayi, kuma bana tsoron abinda yammacin duniya suke fada akai.." ~Muhammad Morsi (Rh)


Allah Zai cika hasken musulunci ko da kafirai da karnukan farautarsu sun ki, kisan Morsi babu abinda zai rage face zai kara daukaka darajar Musulunci da kungiyar 'yan uwa musulmi (Ikhwan) a duk fadin duniya, Alsisi da kana da zurfin tunani da baka kashe Morsi ba!, wanda bai san ikhwan ba yanzu zai santa ya kaunaceta tunda an kashe babban jigonta akan zalunci


Al-sisi ka zama tamkar fir'aunan Misrah, la'anar bayin Allah musulmin duniya, da bakar addu'ah da za'a maka kadai ya isheka babban bala'i da masifa, ba zaka wanye lafiya ba insha Allah



KARANTA ABUBUWAN MAMAKI 15 GAME DA MUTUWAR MUHAMMAD MURSI




Yaa Allah Ka karbi shahadar Muhammad Morsi Amin


Muna rokon Allah Ya gafartawa Muhammad Morsi

Allah Ka yafe masa kuskurensa

Allah Ka jikanshi da rahama

Allah Ka saka masa da Aljannah Madaukakiya Amin.




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode









TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user