Wednesday, 31 July 2019

Karanta Sharhin Manyan Masifu Da Bala'in Dake Kunshe Cikin Rayuwar Gidan Yari

Tura Wannan Zuwa Ga
A rayuwar dan Adam bayan samun lafiyar jiki babu wani abu da ya fi masa daraja a gare shi fiye da ya samu 'yanci a duk inda yake a matsayin sa na dan Adam.

Rayuwar Gidan Yari


Marubuci: Shaikh Farouq Abdullahi Tukuntawa

Sai da 'yanci ne yake da ikon yin duk wani abu na walwala ko inganta rayuwarsa da kawowa kansa da al'ummarsa cigaba.

Ire-ire wadannan 'yanci da dan Adam yake bukata sun hadar da:

'Yancin yin bauta

'Yancin tunani da kirkira

'Yancin walwala

'Yancin tafiye-tafiye

'Yancin yin ilimi

'Yancin yin sana'a

'Yancin mallakar kadara

'Yancin yin aure da sauransu

Rayuwar Gidan Yari

Dan Adam zai samu ingantacciyar rayuwa mai cike da armashi idan har ya samu muhalli da zai ba shi damar morar wadannan 'yanci nasa.

Ga duk wanda yake sauraron gidajen radiyo da sauran kafafen yada labarai ko kuma yake bibiyar al'amuran kotu, abu ne mai sauki ya ji labarin cewa an yanke wa wani hukuncin zama a gidan yari na wasu lokuta, wani ma har da horo mai tsanani a can ko kuma ma wani ka ji an ce an yanke masa hukuncin zama har karshen rayuwarsa!

Abun da wasu suke gani ko tunani shine kawai mutum zai tafi wani kebantaccen waje na wasu lokuta idan lokutan sun kare sai ya dawo ya cigaba da rayuwa.

Rayuwar Gidan Yari

Shin mai karatu ka taba tsayawa kayi nazarin wacce irin rayuwa ake yi a cikin wannan waje?

A wata tattaunawa da na yi da wasu bayin Allah da suka taba tsintar kansu a wannan hali na samu wasu bayanai daga wajen su masu matukar ban tausayi da kuma motsa zuciyar duk mai imani idan yaji yadda rayuwa dan adam take kasancewa tun daga ranar farko da mutum ya tsinci kansa a wannan gida.

Masifu ne kala-kala tun daga kan yanayin ruwan sha, abincin da ake ci a can, yanayin zama da kwanciya a daki daya da kuma mu'amular zamantakewa tsakanin manya da kananan fursinoni, sannan uwa uba bangaren horo da ladabtarwa.

A bangaren ruwan sha ruwa ne kadan kuma mara inganci babban dan gata a kurkuku shine wanda ruwan shan sa ya kai ingancin pure water shima idan 'yan uwan mutum ne suka kai masa kuma pure water guda daya mutum baida ikon ya shanye shi kadai saboda manyan da suke kwana a daki daya suma sai sun karba sun sha.

Rayuwar Gidan Yari

A bangaren abinci abun ya yi muni da yawa, irin abincin nan ne da ake kira "a ci don kar a mutu".

Abincin sam ba shi da dandanon magi ko gishiri, wanda yake da magi dunkule guda daya shine kamar sarki domin da magi dunkule mutum zai sa cikin abinci domin ya ji dan dama-dama, komai zaben abincin ka dole ka ci abinda aka baka ko kuma ka kwana da yunwa, shima abincin da za a baka ba lallai ya ishe ka ba saidai kawai don ka dan ji sauki saboda azabar yunwa.

An ce mutum yakan yi aiki mai matukar wahala kamar wanki da kwasar bahaya domin a biya shi da magi dunkule.

Kusan kullum mutane suna dankare a cikin daki a cikin cunkoso duk kuwa da irin zafin da ake yi.

Rayuwar Gidan Yari

Idan rana ta yi akan fito da mutane cikin farfajiyar gidan, yamma kuma tana yi za a ce kowa ya koma daki ya kwanta.

Mafi munin kwanciya wadda ko juyin kirki baka da damar yi sannan ba hira ake yi a cikin dakin ba zama ne kawai na kunci da bakin ciki.

A cikin kowanne daki akwai wadanda ake kira 'yan sanda da alkali da sauransu kuma suma din masu laifi ne, yanayin dadewar su a cikin gidan ne ya sa suka samu wannan mukami suke hora 'yan uwansu masu laifi.

An ce ko surutu ka yi idan suka ji ka za su iya cewa hukuncin ka bulala kaza ko kuma kwashe bahaya bokiti kaza.

Rayuwar Gidan Yari

Jama'a mu sani masifun da suke cikin wannan gida Allah ya yi yawa da su, muyi wa kan mu adalci mu guji nemawa kanmu masifa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya fi komai muhimmanci a rayuwa.

Sannan mu kasance masu hakuri da yafiya akan abun da bai kai ya kawo ba mu daina kokarin jefa mutane a cikin wahala da masifa yawanci gidan yari ba ya gyara dan Adam, wani lokaci a can ake koyo muggan dabi'u idan aka hadu da muggan mutane a can.

'Yan uwa musulmi masu zuciyar taimako ku sani taimakawa na tsare ba aiki ne da dole sai kana da makudan kudade ba abun da kake rainawa su kuma abune mai matukar muhimmanci a gare su.

Rayuwar Gidan Yari

'Yan sanda, Alkalai da lauyoyi a ji tsoron Allah a yi aiki da amana aikin ku linzami ne da cikin sauki zai sa ku shiga aljanna idan kuma kuka yi aikin cikin rashin gaskiya nan da nan zai kai ku zuwa wutar jahannama.

Allah yasa mu dace Amin.

MUKALOLI MASU ALAKA:

NAFI KOWA FARIN CIKIN KORAR SUPER EAGLE A WASAN AFCON 2019 - DATTI ASSALAFY

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN DUNIYA NA DAYA

KARANTA ZAFAFAN SHAWARWARI 10 ZUWA GA SHUGABAN KASAR NIGERIA MUHAMMADU BUHARI

KARANTA ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user