Friday, 19 July 2019

KARANTA HIKAYAR WATA RANA A KASAR HAUSA KASHI NA BIYU: HIKIYA MAFI NISHADANTARWA A TARIHIN DUNIYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Ishaqa yayi murmushi. Yace "wataqila ma na rigaki sanin wannan labarin. Kinsan mu matafiya ne, muna bada kyauta don a bamu labari, wannan labarin kuwa ya shahara a qasar hausa" Daga nan dai suka ci gaba da firar su ta arziki.


Wasannin Al'adun Hausawa



Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo

A wani lokaci suna cikin tafiya, sai suka jiwo ihu da hargowa. Daga can kuma suka ga hayaqi na tashi, ashe mahara ne masu dibar bayi suka tasamma wani dan qauye.

Akan idon su ishaqa maharan nan suka rinqa rashin mutumci, su kashe na kashewa, su kama na kamawa a matsayin bayi. Mata da yara kuwa me sukeyi idan ba kuka ba. Gashi kuma duk sun cinnawa qauyen wuta.

Ishaqa ya matsa da dokinsa kusa dadokin Randiyya, ya saitu da ita sannan ba ya fara magana da cewa "Tarihi na ya soma ne da misalin wannan abinda kike gani. An bani labarin cewa tun ina yaro akayi wa kauyen mu irin wannan zaluncin, ahaka aka daukeni daga wurin mahaifana tare da siyar dani bawa ga Mehmet. Don haka a hannun sa na girma, a yanzu haka na mance siffar garin mu data mahaifana, ban san komi ba kuma sai bauta..

Jikin Randiyya yayi sanyi, duk ta kamu da tausayin sa gami da tsantsar kauna. A hakika a yanzu tana jin babu wanda ya dace da ita sai Ishaqa.

A yanzu ta kamu da tausayin kanta gami da tausayin sauran al'umma marasa qarfi. Kuna ji kuna gani, za'a maishe da gidaden ku kufai, amaidaku bayi ba tare da kunyi laifin komai ba. A gabanta Uwa ke rabuwa da danta kowa na kuka, uwar  sadauki kaza ya kamata, 'ya'yan kuma wani sadaukin ya kame su, kuma wataqila suda haduwa har abada. Wannan wacce irin rayuwa ce? Randiyya ta raya a zuciyar ta.

    Hargowar dawakan dataji yana tunkaro su ne ya katseta daga halin tunanin da take ciki, da ita da sauran 'yan tawaga gaba daya suka karkata hankulansu izuwa ga abinda ke tahowa garesu.

 Runduna ce ta mayaka suka durfafo su, ba abinda kake ji sai ihu da kade-kade. Tun daga nesa suka hango jagoran tafiyar a gaba, yana ta azama ya tarar dasu. Wani makidi kuma sai zuga shi yake da baitoci. Yana cewa;

      Ja gaba, kaine a gaba
     Gimbau aljanin dare
      Na burungu tsoranku ake
      Take mutum Sare mutum
      Ja gaba, kaine a gaba

Sarkin yaki ya daga murya yana cewa "Ku fito mana da macen data shiga cikin ku, ko kuma yanzu zaku hadu da fushi na"
   ya cigaba da cewa "Ku fito da macen nan da gaggawa. Haqiqa an tabbatar mana da cewa tana cikin ku. Ku fito mana da macen nan da gaggawa" yana maimaitawa har sai da yazo dab da ishaqa, rundunar sa kuma tana baya.

   Ishaqa ya dubi rundunar Sarkin yaqi wadda ta ninka su ninkin ba ninkin, ya kuma kalli tawagarsa wanda da alamar sun tsorata matuka, ya tabbatar da cewa idan fada zasuyi bazaisha Lalai ba, sai kawai ya fara kwallawa Randiyya kira.

"Randiyya! Randiyya!! Randiyya!!!" Har sau uku.

   Daga baya sai gata ta matso kusa dashi ba tare da ta amsa kiran ba, fuskarta na rufe cikin bakin mayafi kamar yadda ta saba.

 Shima Ishaqan bai kalle taba, ya fara bata umarni da cewa "wadannan mutanen na son daukar ki, don haka kiyi saurin shiga cikinsu"

    Ya dubi sarkin yaqi yace "gata nan, kuna iya daukar ta"

   Sarkin yaki yayi ihu gagarumi, ya kuma bushe da dariya, yace "yaro kayi arziki, da yanzunnan zan cire makogwaran kowanne daga cikin ku. Ka ganmu nan, koda girka muna iya buga fada ballantana ku dinnan 'yan tsirari. Kuma sa'ar ku daya bada izininku ta shiga cikin kuba, amma haqiqa da sai mun hukunta ku"

   Daga nan sai ya matso da dokinsa kusa da Randiyya, ya sureta izuwa dokinsa, sannan ya juya akalar dokin ya fita aguje.        Randiyya na zullo da qoqarin kubucewa amma ya riketa katamau, kuka kawai takeyi tana neman taimakon Ishaqa tana cewa "kaji tausayina ishaqa, na shiga halaka, bani da kowa sai kai, kada kayi mini haka ishaqa.."

     Kwalla ta kwaranyowa Ishaqa, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Sannan a sanyaye shima ya juya akalar dokinsa ya fincika a guje yayi hanyar damagaran tare da umartar 'yan tawaga subiyo shi.

   Ottoman yayi azamar saituwa da Ishaqa yana masa magana da cewa "ka ceci rayuwar mu da dukiyar mu, ban taba tunanin kana da basira haka ba"

   Ishaqa yayi murmushi yace" ai masu magana na cewa gudun da babu tsira kwanciya tafishi, don haka naga bai kamata na sanya rayukanku da dukiyoyinku cikin asara ba akan abinda a zahiri ni ya shafa ba kuba"

   Tun daga nan bai kara cewa uffan ba suna ta faman azama kamar wadanda aka biyo har saida getsin yammaci suna daf da shiga garin damagaran, sannan yaja akalar doki ya tsaya.
    Ya matso kusa da ottoman yace "anan zamu rabu daku, ina roqonka kayiwa maigidana bayanin nasarar fataucin da mukaci, ka kuma nemar mini gafara. Hakika zan sadaukar da raina wajen ganin na ceto ran waccan yarinya. Daman na fada maka dalilin dayasa ban tanka suba dazu, amma a yanzu inaganin kun tsira, don haka zan tari aradu daka.."

   Ottoman yace sam baza'ayi haka ba, ya bari su shiga damagaran sai su tattauna yadda za'ayi fadan. Tunda suna da bindigogi kuma akwai tsama tsakanin Sarkin damagaran dana kano, don haka yana ganin Sarkin damagaran zai iya basu rundunar sadaukai wadanda zasuje suci kano da yaki harma su rushe ta su kuma qwato macen. Amma yanzu Mehmet bazaiji dadi ba idan yaji cewa saboda mace ka tafi a kasheka kai kadai."

   Ishaqa dai ya qeqashe kasa yace sam bazai shiga damagaran ba, hakan kuma akayi. Ala tilas suka rabu, su suka shiga gari shi kuma ya juyo yana dauke da doguwar bindigarsa da kuma takobinsa. A rataye, yayi nadi irin na buzaye, babu mai iya gane shi.

    A dai wannan ranar wajajen dare Ishaqa ya cimmarwa rundunar Sarkin yaqi wadda take ta azama ta isa kano. Sai kace sun san wani abu zai biyo baya.

   Tun daga nesa ya sakar musu bindiga, ji kake daram. Dawakai suka firgice abinka da dare mai amsa qara, cikin mazaje ya duru ruwa saboda wutar da suka gani ta tashi daga bindigar.

Dawakai suka fara ja da baya suna tirjiya. Ishaqa ya fuskance su yana mai daka musu tsawa, yace "Ku fito mini da macen cikin ku ko kuma yanzu naga bayanku"

    Sarkin yaqi yace ai mutuwa ce kadai zata sa ya rabu da yarinyar nan ba mutum mahaukaci kamar saba mai tarar mutuwa da dare. Don haka baya tsoron a gwabza yaqi a kanta.

Da fadin haka sai ishaqa ya sakar musu harbi, bindiga ta qara tashi daram, wannan yasa wasu dawakan suka ranta a na kare.

     Da ganin haka sai sarkin yaqi ya kurma ihu, sannan yace arna maza bisa kanka bari yanzu na sare kanka kowa ya huta, sai kawai ya tunkaro ishaqa a guje cikin azama yana mai rike da wani dogon mashi a hannunsa na hagu, takobi kuma a hannunsa na dama. Yana ta azama da dokin yiwa Ishaqa kwaf daya. 

   Ishaqa ya saici sarkin yaki da harbi amma bindigar taqi tashi, yayi yayi sai dai ina, wannan yasa sarkin yaqi ya qara azama yana ihun cewa sunci sunsha ba don qaramin qwaro irinsa ba. Shi kuma Ishaqa sai ya juyar da bindigar sa izuwa bayan sa tare da zare takobinsa sannan yayi kan Sarkin yaqi da sara.

    Arangamar tasu tana da ban tsoro, sara kowannen su yake kaiwa ba tare da yasamu inda yake kai sarar ba. Kowanne ya himmatu wajen cin nasara. Yayin da rundunar sarkin yaqi kuma ta tsaya tana kallon abinda zai faru.

    Ishaqa dai ya wanzu kai sara gami da gociya sai dai a haqiqa ya soma galabaita saboda jarumtar sarkin yaqi tasha bam-bam da tashi. Kafin ayi nisa ma sai da sarkin yaqi ya illata dokin Ishaqa, tilas ishaqa da dokin suka fadi qasa wanwar, sannan sarkin yaki ya qara binsa da niyyar soke shi da mashi, amma Ishaqa yayi gociya wadda duk da haka saida sarkin yaqi yayi nasarar sukar sa a qafa.

   Ishaqa yayi qara yana kiran sunan Allah, anan nema Randiyya ta jiyo muryar sa har ta gane shi, sai kuma tsoro ya qara rufe ta, da yake an kulle tane acikin wani qaton akwati na qarfe wanda bayi ke dauka, sai ta fara bubbuga akwatin bam-bam bam-bam tana kuka. 

Tsammanin ta an kashe Ishaqa.

   Ishaqa yaja jiki daqyar ya tashi yana jan qafa, yana ja da baya. Yayin da shikuma Sarkin yaqi ke murmushin qeta, tsammanin sa fadan yazo qarshe.

   Sarkin yaqi yayi azama ya tsikari dokinsa, yayi kan Ishaqa takobi zare da niyyar tsinke kansa, sai akayi sa'a ishaqa ya durkusa qasa tare dakai mahaukacin sara. Wanda yayi sa'ar sare qafafuwan gaba na dokin sarkin yaqi.

    Kafin kace kwabo doki ya fadi rica, shikuma sarkin yaqi fuskar sa ta tunkuyi qasa idonsa ya rufe sosai saboda yashi daya shiga ciki.

   Ya tashi fagam-fagam yana qoqarin goge qasar daga idon sa, ya dakawa rundunar sa tsawa  kuma da cewa suyi azamar halaka Ishaqa kafin wani abu ya same shi.

Ganin yuyar rundunar Sarkin yaqi ta taso kansa, yasa yayi saurin ciro bindigarsa dake maqale a bayan sa. Da fari dai bakin bindigar da akayi da qarfe ya samu ya cakawa sarkin yaqi a maqogwaro, tunda ya fuskanci takobi ma bata samun nasara akan sa, wanda nan take sarkin yaqi yayi rashe-rashe a qasa cikin jini, sannan ya fuskanci rundunar ya fara sakar musu harbi daram, amma tashin bindigar biyu harsashi ya qare, don haka sai jikinsa yayi sanyi  yasan tabbas bazai tsira ba. Kawai daya fuskanci sarkin yaqi ya mutu sai fara rayawa aransa cewar ko yanzu ya mutu Randiyya zata samu sassauci tunda ga makiyinta ya mutu. Don haka ya shiga sauraro da tsammanin mutuwarsa daga rundunar dake daf da aukar masa.

   Daf da isowar sune sai suka fara jiyo harbi daga baya tare da sautin kofatan dawakai, Ishaqa ya juya da sauri don ganin mutanen da suka iso wurin. Sai kuwa ya hango ubangijinsa Mehmet, da Ottoman da kuma gagarumar rundunar yaqi. Yayi murmushi, yaji wani farin ciki da qwarin guiwa ya lullebe shi, bai san sa'ar daya zare takobi yayi kan  rundunar da sara ba.

    Fada ya kaure sosai, runduna da runduna, sadaukai sai aiki sukeyi. Amma da yake mutuwar sarkin yaqi ta raunana rundunarsa, ba'a jima ana gwabzawa ba akaci nasara akansu, wadansu suka arce, wadansu kuma suka miqa wuya tare da gabato da Randiyya ga Ishaqa.

    Randiyya ta rungume Ishaqa tana kuka gami dayi masa godiya, ta rasa kalmomin da zata fada masa ma don murna.

    Ishaqa ya kama hannun ta sannan ya gabata ga Mehmet, suka duqursa agabansa duka suna masa godiya.

Ishaqa yace "ya shugabana, haqiqa zuwan ka wajen nan ya sani mamaki, kuma tabbas ka ceci rayuwata. Bani da abinda zance maka don yi maka godiya"

  Mehmet yace "Ishaqa kayi sani, na riqeka tamkar dana. Tunda na samu labarin abinda ya auku nace bazan dakata ba, tilas a darennan na biyo bayan ka domin inaji inagani mutuwa tayi awon gaba da Abdulkarem, ba zaiyiwu na bari kaima ka mutu ba alhali inada abinda zan iyayi. Wannan yasa muka nemi taimakon sarkin damagaran na sadaukai kuma shine ka ganmu anan. Don haka yanzu daukar ku zamuyi mu koma damagaran kawai"
  
(Bayan wani lokaci aka daura auren Ishaqa da Randiyya, anyi biki gagarumi. Ishaqa kuma ya cigaba da kula da dukiyar mehmet, suna fatauci daga ankara izuwa qasashen hausawa).

KARANTA HIKAYAR WATA RANA A KASAR HAUSA KASHI NA DAYA

Muna adduar Allah ya mayarwa 'Yan kasuwar da sukayi asara sanadin gobara da alheri amin.

MU KALOLI MASU ALAKA:

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN FADAR BEGE

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA

TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BA


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user