Yadda ake yin Sallah
Ga yadda lafazinta yake:
Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah, Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah. Hayya alas-Salati. Hayya alal-falahi. Kad-kamatis-salatu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilah aillall-lahu.
Sai ka daga hannuwanka daidai kafadunka ko daidai kunnuwanka sai ka yi Kabbara wato ka ce: “Allahu Akbar”.
Sai ka dora hannunka na dama akan hannunka na hagu a kirjinka (kabalu), ko kuma ka sake su (sadalu), duk wanda ka yi daidai ne.
Sai ka karanta karatun bude sallah a asirce ake yinta ita ce:
“Subhankal Lahumma wabihamdika watabaraka ismuka wata’ala jadduka wala’ilaha gairuka”
ko kuma ka ce:
“Allahumma ba’id baini wabaina hadayaya kama ba’adta bainal mashriki wal magribi, Allahumma nakkini min hadayaya kama yunakkal saubul abyadi minad danasi, Allahumma agsilni bil ma’i wassalji wal baradi”.
Sannan a karanta Fatiha zuwa karshenta.
Sannan a karanta abinda ya sauwaka na daga Alkur’ani sura ko wani sashi na sura daga Alkur’ni.
Yadda ake
Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” ayi ruku’u, a cikin ruku’u ana iya karanta: “Subhana Rabbiyal Azim Wabihamdihi” ko a karanta “Subbuhun Kuddusun Rabbul Mala’ikati Warruhu” gwargwadon abinda ya sauwaka.
Sai a dago daga ruku’u ana fadar "Sami'al Lahu Liman Hamidahu" idan an dago an tsaya kafin a tafi sujjada sai a ce:
“Allahumma Rabbana walakal hamdu” ko ka ce “Rabbana walakal hamdu”
Sai kuma ayi kabbara “Allahu Akbar” a yi sujjada ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjada gwargwadon abin da ya sauwaka a (a lura cewa sujjada ana yinta akan gabobi guda bakwai, goshi tare da hanci, tafuka biyu, guiwoyi biyu da kuma kafafu biyu).
Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada a zauna akan kafar hagu ko duwawun hagu, a dora tafuka akan cinyoyi ana fadin “Rabbigfirli” ko kuma “Allahumma Igfirli”.
Sannan ayi kabbara “Allahu Akbar” a koma sujjada ta biyu ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjadar gwargwadon abin da ya sauwaka.
Sannan a yi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada ta biyu, yayin mikewa zuwa raka’a ta biyu (idan an zauna dan kadan kafin mikewa raka’a ta biyu ba laifi, ana kiran wannan dan zama kadan “jalsatul istirahati”).
Sai a sake kawo raka’a kamar yadda aka yi wannan ta farko, amma idan an dago daga sujjada ta biyu a raka’a ta biyu sai a zauna kamar irin zaman da aka yi na dagowa daga sujjada ta farko a dora hannaye akan cinyoyi, sannan hannun dama ayi nuni da dan yatsa manuniya a yi karatun tahiya a wannan zama, karatun tahiya shine:
“Attahiyatu Lillah, Azzakiyatu Lillah, Addayyibatus Salawatu Lillah, Assalamu alaika ayyuhan Nabiyu Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina wa’ala ibadil Lahis Salihina, Ash’hadu an La’ilaha illal Lahu Wa’ash’hadu anna Muhammadan Abduhu warasuluhu”.
Haka ya zo a (Muwadda Malik, lafazin Umar bn Khaddab).
Idan sallar mai raka’a biyu ce, kamar sallar Asubah sai ka cikasa karatun tahiyar anan da salati Ibrahimi. Shi ne kamar haka:
“Allahumma salli ala Muhammadu wa’ala aali Muhammad kama sallayta ala Ibrahim wa’ala aali Ibrahim innaka Hamidun Majid, Wabarik ala Muhammad wa’ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim waala aali Ibrahim Innaka Hamidun Majid”.
Sai kayi sallama, ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah”. Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.
Idan kuma sallar mai raka’a uku ce kamar Magariba ko raka’a hudu kamar Azahar da La’asar da Isha’i, idan kayi kashi na farko na karatun tahiya sai ka tashi ka cikasa ragowar raka’ar da ta rage ko daya ko biyun (a lura cewa a ragowar raka’ar da ta rage bayan biyun farko Fatiha kadai za’a karanta ban da sura ko wani sashi na sura).
Sai ka sake zama na tahiya a karo na biyu ka cikasa tahiyar har zuwa sashi na biyu na salati Ibrahimi sannan ka yi sallama ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah” Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.
KARANTA YADDA AKE YIN KIRAN SALLAH A CIKIN ADDININ MUSULINCI
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode