Sunday, 11 August 2019

KARANTA SUNNONI DA LADUBBA GUDA GOMA SHA BAKWAI 17 NA RANAR IDI

Tura Wannan Zuwa Ga
1-Yin ado da kwalliya dan ranar Idi

Saboda Hadisn Umar bin kaddhaba R.A.

@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 948.



Lokacin Ruku'u a kasa mai Tsarki

Marubuci: Abu Dhurr

2-Yin wankan ranar Idi kafin tafiya sallar idi

Ibn Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wankan idi.

@ﻣﻮﻃﺄ ﻣﺎﻟﻚ، 384.

Sa'id bn Musayyib Allah yayi masa Rahama yana cewa:

"Manyan sunnonin ranar Idi guda ukku ne tafiya masallacin idi a kasa da cin abinci kafin afita a idin karamar sallah da kamewa daga cin komai sai an dawo a babbar Sallah da yin wankan idi".

@ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ‏( 3/104 ‏) ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

3-Yin sallar idi kafin Huduba

Manzon Allah s.a.w da Abubakar da Umar sun kasance suna yin Sallar idi kafin Huduba.

@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ-ﺗﻔﺮﻳﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺑﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :972 ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻰ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻰ ﺩﺍﻭﺩ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 1134 0

4-Haramunne yin Azumi a ranar Idi guda biyu,idan azumi da idin Layya

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

(Babu azumi a ranakun idi guda biyu,idin azumi da idin Layya)

ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ،1197

5-Cin abinci ko wani abu kafin tafi sallar idin azumi,kuma anfi so aci dabino kuma aci mara sabanin Idan layya ana kamewa ba'acin komai sai an dawo daga Idi.

Manzon Allah s.a.w ya kasance baya tafi sallar idin azumi har sai yaci Dabino kuma yana cin dabinon ne mara.

ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 953.

6-Yin sallar Idi a musalla shine sunnah wato a bayan gari a wani fili ba masallaci ba.

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana fita musallane don yin sallar idi.

ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 510.

Ibn Umar R.A yana cewa:

"Manzon Allah s.a.w yana fitane da wuri zuwa musalla dan yin sallar idi...."

ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ1294

7-Sunnane a fitar da mata da yara zuwa sallar idi,amma matan suyi shiga ta musulinci kuma kada su sanya turaren da kamshensa yake tashi.

ﺍﻟﻠﺆﻟﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ، 511.

Sayyadina Abubakar R.A yana cewa:
"Hakkine akan kowace budurwa da macen aure fita zuwa sallar idi".

ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ .

8-Tafiya masallacin idi kasa idan da ikon hakan

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tafiya masallacin idi akasa kuma ya dawo akasa.

ﺣﺴﻦ / ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 1078 1311 )

Aliyu bn Abi Dhalib R.A yana cewa:

"Yana cikin Sunnah tafiya sallar idi a kasa kuma aci wani abu kafin a fita idi".

ﺣﺴﻦ /ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ530

9-Chanza hanyar dawowa ko hanyar zuwa masallacin idi

Manzon Allah s.a.w ya kasance yana chanza haryar dawowa daga masallacin idi.

@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، 986.

Ibn Umar R.A yana cewa:

"Na koya daga Manzon Allah s.a.w chanza har dawowa daga masallacin idi.

@ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ، 254.

10-Yin kabarbari a ranar Idi,ana fara kabbarar ne daga farkon wanta zul-Hijjah har zuwa karhen yini na ranar 13 ga wata anayi son yawaita yin kabbarori akowane lokaci ba sai bayan sallah ba kadai.

Imam Sun'ãni yana cewa:

"Yin kabbar tun daren idi har zuwa fara sallar idi yin hakan sunnane abisa haduwa mafi yawan malamai saboda farrasa fadin Allah Madaukakin sarki.

(ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ )

@ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 185

@ ﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺳﺒﻞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺍﻟﺠﺰﺀ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ : 100-101 .

11-Sigogin Kabbarorin ranar Idi

Daga Cikin sigogin da aka samo daga Sahabbai sun hada da;-

Siga ta farko;-

ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺃﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ

@ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ.ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ‏( 3/125 ‏)ﻭﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ.

Siga ta biyu;-

 ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ*

Siga ta Ukku;-

 ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﺃﺟﻞ، ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻫﺪﺍﻧﺎ .

@ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ، ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ . ﻗﺎﻝ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ
‏( 3/125 ‏)ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ

12-Sanya Turare dan zuwa sallar idi

Abdillahi dan Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wanka ya sanya turare.

@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ - ﺑﺎﺏ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻓﻲ ﺍﻻﻏﺘﺴﺎﻝ ﻟﻠﻔﻄﺮ ﺣﺪﻳﺚ 015

13-Ba'a sallar nafila kafin sallar idi ko bayanta,kuma ba'a kiran sallah ko iqama

@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﺣﺪﻳﺚ :1517

@ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ ﻟﻠﻔﺮﻳﺎﺑﻲ - ﺑﺎﺏ ﻣﺎﺭﻭﻱ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺻﻼﺓ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻗﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻻﺑﻌﺪﻫﺎ ﺣﺪﻳﺚ 0143

14-Yin gaisuwar sallah da fatan Alkhairi da fatan Allah ya maimata mana

An samu daga aiyukan maganata suna yiwa junansu barka da sallah da fatan alkhairi,daga cikin abinda suke fada akwai;-

ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ

15-Yin wasa na al'ada wanda babu sabon Allah acikinsa dan nuna farincin ranar Sallah,sannan mata zasu yi nasu wake da buda kayan kidansu na al'ada wanda babu sabon Allah

@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ - ﺃﺑﻮﺍﺏ
ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ - ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺤﺮﺍﺏ ﻭﺍﻟﺪﺭﻕ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ - ﺣﺪﻳﺚ :921 ، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ - ﻛﺘﺎﺏ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﻴﺪﻳﻦ - ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻌﺐ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻣﻌﺼﻴﺔ ﻓﻴﻪ ﻓﻲ ﺃﻳﺎﻡ ﺍﻟﻌﻴﺪ - ﺣﺪﻳﺚ 01527:

16-Cin wani abu daga cikin abinda ka yanka na layya bayan dawowa daga sallar Idi.

Manzon Allah SAW ya kasance baya cin abinci a idin babbar sallah har sai ya dawo daga Masallaci sannan yana fara cine daga wani sashe daga abinda ya yanka na layyarsa.

@ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ / .144

17-Girmama ranar Idin layya akan sauran ranaku domin ranace mai girma awajan Allah.

Manzon Allah SAW yana cewa;

(Mafi girman ranaku a wajan Allah sune; Ranar Layya da ranar washe garin Layya).

@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ

  Allah ne mafi sani

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

KARANTA YADDA AKE YIN SALLAH

KARANTA SALLOLI WAJIBABBU A CIKIN ADDININ MUSULINCI

Ina yiwa dukkan musulmai barka da sallah da fatan alkhair,Allah ya maimata mana.

ﺗﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻣﻨﻚ


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user