Friday, 16 August 2019

KARANTA MANYAN SUNNONIN SALLAH GUDA GOMA SHA HUDU 14

Tura Wannan Zuwa Ga
Sunnonin Sallah dai guda goma sha hudu ne (14) sune:

1- Karatun sura bayan fatiha ko wasu ayoyi da zasu tsaya a matsayinta, wannan ana nemansa a sallar Asuba da Juma’a da biyun farko na sallolin da aka farlantawa kowa.

Yayin yin Ruku'u a Masallacin Eid a Nigeria


2- Tsayuwa don yin karatun sura.

3- Bayyana karatu a cikin biyun farko na sallar Magriba da Issha’i da sallar Asuba da shafa’i da wuturi da kuma juma’a, da sallolin idi guda biyu, da sauran nafil-fili na dare kai har da sallar rokon ruwa, wadannan dukkansu ana bayyana karatunsu.

4- Asirta karatu a cikin sallolin da ba a ambatasu ba a sama. Shi kuwa abin da ake kira asirtawa shine abin da kow ba ya jinsa wato kishiyar bayyanawa.


FADAKARWA

Da mai sallah zai asirta karatu a mahallin da ake bayyanawa ko ya bayyana a mahallain da ake asirtawa, kamar aya daya ko biyu da ganganci ko da mantuwa, to a nan ba komai a gareshi. Amma a yayin da ya zamo tafi ayoyi biyu kuma ya tuna tun kafin ya kama guiwarsa don yin ruku’u, to sai ya sake karatun fatiha tare da sura. Amma idan ya rigaya ya kama guiwarsa sannan ya tuna to ba zai dawo tsaye ba,domin kulla raka’a a gurin IBN AL-KASIM tana tabbata ne da dago kai daga ruku’u, sai dai a cikin wasu mas’aloli wadanda wannan hukunci na manta bayyanawa ko asirtawa yana cikinsu.

Wasu daga cikin malamai sun ce: da mai sallah zai bar bayyana karatun sallah da gangan, to ya yi laifi sai ya nemi gafarar Allah, amma sallarsa bata baci ba, ba kuma komai akansa. Wasu suka ce ta baci domin ya wulakanta sunnoni kamar yadda hakan take bayuwa izuwa wulakanta farillar.

5- Duka kabbarorin sallah sunna ne ban da kabbarar harama.

6- Zaman tahiya na farko a cikin sallolin da suke da zama biyu. Haka tahiyar farko da ta biyu, kuma a furtata da lafuzzan da aka rawaito a hadisi shine:

ATTAHIYATU LILLAHI. AZZAKIYATULILLAHI, ADDAYYIBATUS-SALAWATU LILLAHI. ASSALAMU ALAIKA AYYUHAN NABIYU WARAHMATUL-LAHI WA BARAKATUHU, ASSALAMU ALAINA WA ALA IBADULLAHIS-SALIHINA, ASH-HADUAN LA’ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WARASULUHU.

7-Yin salati ga Annabi(S.A.W) a cikin tahiyar karshe shine mai sallah ya ce:

ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALIMUHAMMAD KAMA SALLAITA ALA IBRAHIMA WA ALA ALI IBRAHIMA, WA BARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD KAMA BARAKTA ALA IBRAHIMA WA ALA ALI IBRAHIM FIL ALAMINA INNAKA HAMIDUN MAJID.

8- Fadar Sami’allahu Liman hamidahu ga liman da mai yin sallah shi kadai ba.

9- Juyar da sallama ga liman da kuma wanda yake hagun mamu.

10- bayyanawa da sallamar fita daga sallah.

11- saurarar liman a yayin da yake bayyana karatun sallah.

12- Sanya sitra ga liman da kuma mai yin sallah shi kadai.

Saboda haka, mai shigewa ta gaban mai sallah yana yin zunubi in dai yana da wata hanyar da zai wuce.

ABUBUWA MASU ALAKA:

KARANTA SUNNONI DA LADUBBA GUDA GOMA SHA BAKWAI 17 NA RANAR IDI

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

KARANTA FALALAR WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA


13- Yin dadi a bisa gwargwadon abinda yake isa a yi sallama na daga zaman tahiya.

14-Yin dadi a bisa gwargwadon samin nutsuwa akan ayyukan sallah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user