Friday 16 August 2019

MU SHA DARIYA: KARANTA LABARIN WANI RIKITACCEN TSOHO DA SAURAYI

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani saurayi yana tafiya a hanyarsa ta zuwa rumfar mai abinci, sai ya hangi wani tsoho sai sharɓar kukansa yake ba kakkautawa.


'Yar Auta ta cikin shirin Kannywood


Sai tausayin wannan tsoho ya kama shi, sai ya nufi wurin tsohon.


Saurayi: "Baba lafiya kake irin wannan kuka haka?"


Tsoho: "Yaro ina da mata 'yar kimanin shekara ashirin da biyu a gida. Kullum da safe sai ta yi mini tausa, kuma ta soya mini ƙosai, ta yi min koko ta kuma dafa mini shayi mai daɗi."


Saurayi: "To mene ne ya sa kake kuka?"


Tsohon' "Da rana kuma ta mini miyar alayyahu da tuwon shinkafa mai daɗi, ta kuma haɗa mini zoɓo mai sanyi, ta kuma tsaftace gidan, bayan ta gama, sai ta zauna kusa da ni, ta kunna mana talabijan mu yi kallo cikin jin daɗi har yamma.".


Saurayi: "Baba har yanzu ba ka faɗa mini  abinda ya sa kake kuka ba!.".


LABARAI MASU ALAKA:

KARANTA LABARIN WANI BAFULATANI DA BATURE

KARANTA LABARIN WANI BAKANO A RESTAURAN TARE DA GAYU

LABARIN WANI GAYE DA BUDURWA A MOTAR HAYA


Tsoho: "Da daddare kuma ta yi mini alkubus da romon kaza, ta kuma matse lemo ta kawo mini, na ci na sha cikin annashuwa".


Saurayi: "To duk da wannan abu da take maka me kuma ya sa ka kuka Baba?"


Tsoho: "To ai hanyar gidan na manta.".


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user