Daga cikin manya manyan Jakadun masu sabon tsarin Duniya, sune mawaqan zamani wadanda suka shahara kuma wadanda ake ganin sune celebrities.
Sabon Tsarin Duniya
Hatta a cikin nau'ukan rawa da suke akwai alamu dayawa da nuna wakilcin su ga masu bautar shaidan (Illuminati) wanda kuma sune suka tsara yanda suke so duniya ta zama da irin shiri da suke mata. Idan muka duba shine, zamu ga yanda suke gudunar da irin rawar tasu chakude ta yan mata tsirara sai kawai dan abunda ya rufe al'aurar su. A cikin masu dukkan wadannan rawa, daga Mazinata sai masu Luwadi da kuma Yan madigo.
Daga cikin dumbin nasarori da masu sabon tsarin Duniya suka samu shine bayyanar mawaqa na turanci da sauran harsuna da yaran mu suka karkata wajen kwaikwayon su, wanda hakan yana daga babban illa da suka mana qwarai. A yau an wayi gari, zaka samu matasa sun haddace waqoqin dukkanin wani Celebrity dake tashe, sawa'un ya qunshi da harshen turanci yake waqar tashi ko da wata yaren daban wanda zaka samu shi wannan matashi baya fahimtar abunda suke cewa, amma sabida tsabar ta'asiri da suka yi a zukatan matasa, zaka samu haka suke haddacewa, qarshen abunda dake zuwa qwaqwalen su shine, yin hakan shine wayewa.
A yau idan ka tara matasa goma sai ka tarar tkwas ko bakwai daga ciki sun iya waqoqin wadannan celebrities da ake hi dasu a duniya, sa6anin yanda zaka same su sukan addinin su, wajen haddar Qur'ani. Abun haushi wani ko farillan Sallah bai sani ba, wani ya balagha bai iya wankan Janaba ba, amma zaka samu yasan babban Mucian wane, da babba Rapper wane, da irin tarin waqoqain da yayi harda kiyaye shekarun su.
Wallahi tallahi bakwa bina bashin rantsuwa, duk wadanann mawaqa da kuke ganin su har suke burge ku duk wakilai ne na masu Sabon tsarin Duniya. Amma sabida mun durmuya wajen koyi dasu, maimakon sanya suturar mu ta musulunci, sai ya zama sututurar tasu burge mu dasu muke koyi da zimmar wayewa, kisan komai nasu matasan mu sun faka cikin koyi dasu. Zaka samu hatta wajen auratayyar mu waqoqin su muke sakawa muna rawa, ba tare da ana fahimtar irin munanan kalamai na batsa da suke anfani dasu ba wajen waqoqin nasu. Daga qarshe, mu sani cewa bamu da abunda yafi cancanta muyi da tafarkin sa face tafarkin Manzon Allah tsira da amkncin Allah su tabbata gare shi.
Domin Allah madaukakin sarki ya jawo hankalin mu da cewa:
{لَّقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِّمَن كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا } [الأحزاب 21]
.
"Haqiqa ya kasance tattare da Manzon Allah abun koyi mai kyau, ga dukkan wanda yake fatan Allah da ranar Qarshe, ya kuma ambaci Allah dayawa"
Malamai sun kasa abun koyi zuwa kashi biyu kamar haka:
فالأسوة نوعان: أسوة حسنة، وأسوة سيئة.
Abin koyi mai kyau, da kuma abun koyi marar kyau:
فالأسوة الحسنة، في الرسول صلى اللّه عليه وسلم، فإن المتأسِّي به، سالك الطريق الموصل إلى كرامة اللّه، وهو الصراط المستقيم.
1. "Abun koyi mai kyau, shine wamda manzon Allah yake tattare dashi. Mai koyi dashi, shine ya kama hanya ga zuwa karamcin Allah, hakan shine hamya miqeqqe"
وأما الأسوة بغيره، إذا خالفه، فهو الأسوة السيئة، كقول الكفار حين دعتهم الرسل للتأسِّي بهم
2. "Amma abun koyi sa6anin sa, idan ya sa6a da abunda yake mai kyau, abun koyi marar kyau kenan. Kamar cewar kafirai a lokacin kiran su ga Manzon Allah da yin koyi dasu"
Ashe kenan duk wani abun koyi sa6anin koyi da abunda Manzon Allah ya koya mana bisa dabi'un sa kyawawa, bai zama abun koyi mai kyau ba. Sabida haka, muyi qoqarin watsi da wadancan mutane muke qoqarin koyi dasu wadansa baza su anfane mu da komai ba face su kaimu ga hallaka.
DUBA WADANNAN:
KARANTA SABON TSARIN DUNIYA KASHI NA FARKO (1) NEW WORLD ORDER
KARANTA SABON TSARIN DUNIYA KASHI NA BIYU (2) NEW WORLD ORDER
KARANTA CIKAKKEN TARIHIN IMAM MALIK BN ANAS
Mu hadu a kashi na hudu, zamu tattauna akan yan kwallo, suma duk suna wakiltar ma sabon tsarin Duniya ne.
Ya Allah ka mana dacewa bisa hanyar tsira.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng