Monday, 30 September 2019

Karanta Yadda ake Yin Salatin Annabi Muhammad (SAW) a Mahangar Sunnah

Tura Wannan Zuwa Ga
SALATI GA ANNABI (SAW) , TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI (SAW) , BAYAN ANYI TAHIYA.

اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.

Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala  Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed.

ANNABI MUHAMMAD (SAW)

Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda kayi salati ga Ibrahimu da alayen Ibrahim, lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu, da alayen Ibrahimu, lallai kai abon godewa ne, mai girma.

اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ  وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ. وَبَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ. إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.

Allahumma salli AAala Muhammad wa-'ala azwajihi wathurriyyatihi kama sallayta 'ala ali Ibraheem, wabarik 'ala Muhammad, wa-'ala azwajihi wathurriyyatih, kama barakta 'ala ali Ibraheem. innaka Hameedun Majeed.

Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi salati ga alayen Ibrahim. Kuma ka yi albarka ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi albarka ga alayen Ibrahim. Lallai kai abin godewa ne, mai girma.

اَللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ فِتْنَةِ  الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ.

Allahumma innee a'u'zu bika min 'athabil-kabr, wamin 'azabi jahannam, wamin fitnatil-mahya walmamat, wamin shari fitnatil-maseehid-dajjal.

Ya Allah ina neman tsari da Kai daga azabar kabari, da azabar Jahannama, da fitinar rayuwa da ta mutuwa, da sharrin fitinar Dujal shafaffe.

اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ مِـنْ عَذابِ القَـبْرِ، وَأَعـوذُ بِكَ مِـنْ فِتْـنَةِ  المَسيحِ الدَّجّـالِ، وَأَعـوذُ بِكَ مِـنْ فِتْـنَةِ  المَحْـيا وَالْمَمَـاتِ. اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ مِنَ المَأْثَـمِ وَالمَغْـرَم .

Allahumma innee a'u'zu bika min azabil-kabr, wa-a'u'zu bika min fitnatil-maseehid-dajjal, wa-a'u'zu bika min fitnatil-mahya walmamat. Allahumma innee a'u'zu bika minal-ma'thami walmaghram.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga azabar kabari, kuma ina neman tsarinka daga fitinar Dujal shafaffe, kuma ina neman tsarinKa daga fitinar rayuwa da ta mutuwa. Ya Allah ina neman tsarinka daga laifi da bashi.

اَللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي ظُلْمًا كَثِيراً وَلاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ، فَاغْفِرْلِي مَغْفِرَةً مِنْ عِنْدِكَ وَارْحَمْنِي، إِنَّكَ أَنْتَ الغَفُورُ الرَّحِيم .

Allahumma innee zalamtu nafsee zulman katheeran wala yaghfiruz-zunooba illa ant, faghfir lee maghfiratan min 'indika warhamnee, innaka antal-Ghafoorur-Raheem.

Ya Allah! Hakika ni na zalunci kai na, zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai Kai. Saboda haka Ka gafarta mini, gafara daga gare Ka, kuma Ka ji kai na, lallai Kai ne mai yawan gafara, mai yawan jin kai.

اَللَّهُمَّ اغْفِرْلِي مَاقَدَّمْتُ وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ، وَمَا أَسْرَفْتُ، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي. أَنْتَ الْمُقَدِّمُ، وَأَنْتَ الْمُؤَخِّرُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ.

Allahummagh-fir lee ma kaddamtu,  wama akhkhart, wama asrartu wama a'alant, wama asraftt, wama anta a'alamu bihi minnee, antal-mukaddimu wa-antal-mu-akhkhiru la ilaha illa anta.

Ya Allah ka gafarta mini abin da ya wuce da abin da zai zo, da abin da na boye da abin da na bayyana, da kuma abin da Kai ne Ka fi fi ni saninsa. Kai ne Mai gabatarwa, kuma Kai ne Mai jinkirtawa; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.

اَللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِك، وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ.
Allahumma a'innee 'ala zikrik, washukrik, wahusni ibadatik.

Ya Allah! Ka taimake ni a kan zikirinka, da yin godiya gare Ka da kyautata ibada gare Ka.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ  البُخْلِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الْجُبْنِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ أَنْ أُرَدَّ إِلَى أَرْذَلِ الْعُمُرِ، وَأََعُوذُ بِكَ مِنْ فِتْنَةِ الدُّنْيَا وَعَذاَبِ القَبْرِ

Allahumma innee a'u'zu bika minal-bukhl, wa-a'uzu bika minal-jubn, wa-a'uzu bika min an oradda ila arzalil- umur, wa-a'u'zu bika min fitnatid-dunya wa'azabil-kabr.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga rowa, kuma ina neman tsarinka daga tsoro, kuma ina neman tsarinka daga a mai da ni zuwa wulakantacciyar rayuwa (tsufa tukuf-tukuf), kuma neman tsarinka daga fitinar duniya da azabar kabari.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَأََعُوذُ بِكَ مِنَ النَّارِ.
Allahumma innee as-alukal-jannah, wa-a'u'zu bika minan-nar.

Ya Allah! Ina rokon Ka aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.

اللّهُمَّ بِعِلْمِكَ الغَيْبِ وَقُدْرَتِـكَ عَلَى الْخَلقِ أَحْيِنِي مَا عَلِمْتَ الْحَيَاةَ خَيْراً لِي، وَتَوَفَّنِي إِذَا عَلِمْتَ الوَفَاةَ  خَيْراً لِي، اَللَّّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَشْيَتَكَ فِي الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ، وَأَسْأَلُكَ كَلِمَةَ الْحَقِّ في الرِّضَا وَالغَضَبِ، وَأَسْأَلُكَ الْقَصْدَ فِي الْغِنِى وَالْفَقْر، وَأَسْأَلُكَ  نَعِيماً لاَ يَنْفَذْ، وَأَسْأَلُكَ قُرَّةَ عَيْنٍ لاَ تَنْقَطِعْ  وَأَسْأَلُكَ الرِّضَا بَعْدَ القَضَاءِ، وَأَسْأَلُكَ بَرْدَ الْعَيْشِ بَعْدَ الْمَوْتِ، وَأَسْأَلُكَ لَذَّةَ النَّظَرِ إِلَى وَجْهِكَ وَالشَّوْقَ إِلَى لِقَائِكَ، فِي غَيْرِ ضَرَّاءَ مُضِرَّةَ، وَلاَ فِتْنَةٍ مُضِلَّةٍ، اللّهُمَّ  زَيِّنَّا بِزينَةِ اْلإِيـمَانِ، وَاجْـعَلْنَا هُدَاةً مُهْتَدِينَ.

Allahumma bi'ilmikal-ghayb, wakudratika 'alal-khalk, ahyinee ma 'alimtal-hayata khayran lee watawaffanee iza 'alimtal-wafata khayran lee, allahumma innee as-aluka khashyataka fil-ghaybi washshahadah, wa-as-aluka kalimatal-hakki fir-rida walghadab, wa-as-alukal-qasda fil-ghina walfakr, wa-as-aluka naAAeeman la yanfad, wa-as-aluka qurrata 'aynin la tankati'a, wa-as-alukar-rida ba'adal-qada, wa-as-aluka bardal-'ayshi ba'adal-mawt, wa-as-aluka lazzatan-nazari ila wajhik, washshawka ila lika-ik fee ghayri darraa mudirrah, wala fitnatin mudillah, allahumma zayyinna bizeenatil-eeman waj'alna hudatan muhtadeen.

Ya Allah! Saboda saninka da abin da ya faku, da kuma ikonka a kan halitta, Ka rayar da ni idan Ka san rayuwa ta fi alheri a gare ni; kuma Ka kashe ni idan Ka san mutuwa ta fi alheri a gare ni; Ya Allah! Ina rokonka jin tsoronka a boye da kuma a sarari, kuma ina rokonka jin tsoronka a boye da kuma a sarari, kuma ina rokonka fadar gaskiya a halin dadin rai da halin fushi, kuma ina rokonka tsakaitawa a cikin wadata da talauci, kuma ina rokonka ni'ima da ba ta karewa, kuma ina rokonka sanyin idaniya (watau farin ciki) da ba ya yankewa. Kuma ina rokonka yarda da kaddara bayan afkuwarta. Kuma ina rokonka dadin kallon fuskarKa, da kuma shaukin saduwa da Kai, ba tare da cuta mai cutarwa ba, ko fitina mai batarwa. Ya Allah! Ka yi mana ado da adon imani, kuma Ka sanya mu masu shiryarwa kuma shiryayyu.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ يَا اللهُ بِأَنَّكَ الْوَاحِدُ الأَحَدِ، اَلصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُواً أَحَدٌ، أَنْ تَغْفِرْ لِي ذُنُوبِي إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِّيمِ.

Allahumma innee as-aluka ya Allah bi-annakal-wahidul-ahadus-samad, allathee lam yalid walam yoolad, walam yakun lahu kufuwan ahad, an taghfira lee zunoobee innaka antal-Ghafoorur-Raheem.

Ya Allah! Ina rokonka, ya Allah saboda Kai ne daya kadai tal, wanda ake nufi da dukkan bukatu, wanda ba a haifa ba, kuma ba a haife ba, kuma babu wani tamka gare Shi, Ka gafarta mini zunubai na, kai ne mai yawan gafara, Mai yawan jin-kai.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّ لَكَ الْحَـمْدُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ الْمَنَّانُ يَا بَدِيعَ السَّمَوَاتِ وَاْلأَرْضِ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالإِكْرَامِ، يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ النَّارِ.

Allahumma innee as-aluka bianna lakal-hamd, la ilaha illa ant wahdaka la shareeka lak, almannan, ya badee'as-samawati wal-ard, ya thal-jalali wal-ikram, ya hayyu ya kayyoom, innee as-alukal-jannah, wa-a'uzu bika minan-nar.

Ya Allah! Ina rokonka saboda dukkan yabo ya tabbata gare Ka, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Kai kadai babu abokin tarayya a gare Ka, Mai yawan baiwa; ya makagin halittar sammai da kasa, ya ma'abocin girma da alheri, ya rayayye, ya mai tsayuwa da komai, ina rokonka aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.

DUBA WADANNAN:

KARANTA FALALAR ZIKIRI

Karanta Yadda ake Yin Tahiyya

Karanta Addu'ar Bude Sallah Bayan An yi Kabbarar Harama

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّي أَشْهَدُ أَنَّكَ أنْتَ اللهُ لاَ إِلَهَ إِلاّ أَنْتَ اْلأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ ، وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُواً أَحَدٌ.

Allahumma inne as-aluka biannee ashhadu annaka antal-lah, la ilaha illa ant, al-ahadus-samad, allazee lam yalid walam yoolad walam yakun lahu kufuwan ahad.

Ya Allah! Ina rokonka, saboda ni na shaida cewa Kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Kai kadai tal, wanda ake nufa da dukkan bukatu, wanda bai Haifa ba, kuma ba'a haife Shi ba, kuma babu wani tamka a gare Shi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user