Wednesday, 25 September 2019

KARANTA KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA CIKIN GAGGAWA

Tura Wannan Zuwa Ga
WASU  DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA CIKIN GAGGAWA.

1. HASSADA

Hakika Hassada tana daya daga cikin abinda yake cutar da al'umma.

Manzon Allah (S.A.W) Yace:

"Kashedin ku da hassada domin hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye Auduga.

Halayen da Suke Cutar da Al'umma

MarubuciSaifullahi Adamu Binginde

2. ANNAMIMANCI

Annamimanci shima yana cutar da al'umma.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:

"Lokacin da aka yi mi'iraji dani mun wuce wasu mutane masu zara-zaran kumba, (farce) suna jan naman fuskokinsu, da jikkunan su.

Sai nace su wanene wadannan Ya Jibrilu ???

Sai yace sune wadanda suke cin naman mutane.

Don haka akwai tanadin azaba mai tsanani ga masu cin naman mutane.

3.GIRMAN KAI

Kowa da irin nasa nau'in girman kan.

Akwai girman kai na rashin karban gaskiya.

Akwai kuma girman kai na wulakanta Jama'a.

Manzon Allah (S.A.W) yace:

"Mai girman kai koda kwayen zarrane bazai shiga Aljannah ba.

4. GIBA

An tambayi Manzon Allah (S.A.W) menene Giba ???

Sai yace ka ambatawa dan'uwanka abinda baya so.

5. KARYA

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:

"Yana daga cikin manyan laifuka kabawa dan'uwan ka labari, shi yana dauka gaskiyane amma kuma kai karya kakeyi, wannan shima yana cutar da al'umma, domin karya tana leading mutum zuwa ga Abubuwa masu yawa, kada kaji tsoro ko faduwar gaba indai abinda kake fada gaskiyane, koda dukkan mutane zasu ki yarda dakai.

6. KADE KADE DA RAYE RAYE

Tabbasa yawan jin waka yana kashe zuciyar bil Adama yana lalata zuciya, yana kuma haifar da sharri, yana kuma samar da mummunar dabi'a.

Wani sai yayi sati bai karanta Qur'ani ba, kuma baya saurara, wani ma gani yake kauyancine saka karatun Qur'ani acikin wayarsa, domin su zigi zasuce bai
waye ba.

Zaka sami mutum yana da Memory Card mai nauyi, amma ba abinda yake ciki sai wakoki da videos masu nauyi, hakika dan'uwa ko 'yar uwa duk wadanda suke aikata haka to sun dauko hanyar halaka.


7. ZINA

Zina shima yana cikin munanan halayen da suke cutar da al'umma.

8. KALLON FINA FINAN BATSA

Hmm wannan musifa ya riga ya yadu a duniya, laifi ne babba ma'aurata su fadi sirrin su, sai gashi yau ana samun mutanen da suka mai dashi sana'a, wai kuma musulmi ya cire kudin shi yaje ya siya, hakika duk mai kallon wannan fina finan yayi asara babba wallahi, idan kana kallo ne domin karage wa kanka sha'awa to wannan hudubar shaidan ne, babu wani rage maka sha'awa da zayyi, sai dai ma kullun yasa muku kwadayi.

Ba anan shegantakar ta tsaya ba hatta mijin aure musamman sabon aure, haka zaije ya siyo musu wai saboda su koyi yadda akeyi, wannan abin yana faruwa sosai a cikin al'umma.

Gaskiya sai munyi da gaske sannan mu yaki shaitan.

9. CIN HARAM

A gaskiya yawancin mutanen wannan zamanin suna cin haram idan kana cin haram ko addu'a kayi ba za'a amsa maka ba.

Yanzu akwai wani abin tsiya da Attajirai suke yi, idan suka ci haram suka wawuri kudin talakawa, suka yi handama da babakere, sai kuma su yawaita aikin lada, su rinka daukan kudin haram suna gina masallaci da islamiyya, da zuwa aikin hajji da sadaqa, su a jahilcin su wai wannan aikin ladan shi zai kankare musu zunuban su,shi zai hana Allah yayi musu azaba, Wai kaji sune zasu yi ma Allah wayo.

Sun mata Manzon Allah yace "Lallai Allah Madaukakin sarki mai tsarki ne, kuma baya karban aiki sai mai tsarki".

Kudin dakaci basu da tsarki, so ta ya ya Allah zai amsa maka Ibadun da kayi da wannan kudin.

Kacuci 'ya'yan ka raine su da dukiyar haram hakika Allah zai muku hisabi.

10. CIN AMANA

Amana muka rasa yanzu mu musulmai, daidaikun mutane ne masu Amana, yanzu kafin ka sami wanda zai rikemaka amanar dukiyar ko iyalinka sai ka bincika, shiyasa yanzu kafirai basa jin tsoron mu, shiyasa suke tattakamu, suke karkashe mu, suke wulakanta mu suke ci mana mutunci.

DUBA WADANNAN:

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

KARANTA YADDA RAYUWAR AURE TA LALACE A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

Karanta Sharhin Manyan Masifu Da Bala'in Dake Kunshe Cikin Rayuwar Gidan Yari

Don haka cin amana yana daya daga cikin MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'AUMMA.

A SABODA HAKA NAKE MANA
NASIHA DA MUJI TSORON
ALLAH KUMA MU GUJI AIKATA
DAYA DAGA CIKIN WADANNAN
MUNANAN DABI'UN.

ALLAH KA KAREMU DAGA WADANNAN MUNANAN AYYUKAN AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user