Sunday, 29 September 2019

KARANTA LAIFIN ME MALAM DR ISA ALI PANTAMI YAYI WA 'YAN KWANKWASIYYA SUKE KOKARIN HALLAKA SHI?

Tura Wannan Zuwa Ga
Na kalli wani Video wanda wasu daga ƴan kwankwasiya ke wa Sheikh Dr Isa Ali Fantami Ihun basayi, suna neman farmasa don su illata shi, wannan mummunan lamari mara dadi ya auku ne a filin tashin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Dr. Isa Ali Pantami

Marubuci: Aliyu Imam Indabawa

Tabbas wannan abun baƙin ciki da taƙaici ne garemu Kanawa da sauran mutanen kirki na Nigeria dama duniya baki daya.

Wannan ba komai bane sai Jahilci, Iskanci, rashin mutunci da dabbanci, Malam Fantami be wa wadan nan mutane laifin komai ba, idan ma yana da laifi be wuce kasancewarshi Malamin addinin musulunci wanda Allah yayi mishi ɗumbin baiwa gami da tarin ni'ima wanda babu dan siyasar dake da irinsu a kasar nan. Wanda ke kokarin kare addinin Allah da Sunnar Manzonshi S.A.W da ƙoƙarin ɗabbaka tauhidi da Suburbudar Jahilai masu izgilanci wa Allah da addininshi.

Alaji ita fa Siyasa ra'ayi ce, idan jin haushin Ni'imar da Allah yayi wa Malam yasa kake ƙokarin mishi ɓatanci me zai hanaka ƙokarin neman irin ilmin addininshi da bokonshi? Me zai hanaka neman fasaha da azanci  irin na Malam? Me zai hanaka lazimtar kyawawan ɗabi'u irin nashi irinsu takawa da tawadi'u?  Sai kazo kana Hauka da sunan siyasa, da wane yace maka dole sai kayi? Wannan ba komai bane sai hassada daga wajen mutane marasa daraja wanda basu sami tarbiyyar siyasa ba, waɗanda basu yarda da cewa Allah yana daukaka wanda yake so cikin bayinshi ya kaskantar da wanda yaso ba.

Ko kaɗan be kamata ace magagin Hassada da rashin mulki yasa kuyi rashin mutunci ga Malamai masu daraja irin Fantami ba, amma ba abin mamaki bane, Domin babu ta yadda barewa zatai gudu ɗanta yayi rarrafe, wannan muguwar ɗabi'a ba bakuwa bace a Jahar Kano, domin an sha ambatar malamai anawa Gemunsu izgilanci.

Wadannan yara masara daraja ba Malam suka wulakanta ba, Addinin musulunci suka wulakanta, duk wanda ya wulakanta musulunci Manzon Allah ya wulakanta, duk wanda ya wulakanta Manzon Allah S.A.W Allah ya wulakanta. Duk me wulakanta Allah da Manzonshi Tsinanne ne duniya da lahira.

Manzon Allah shine ya umarce mu cewa" Ku girmama Malamai domin su magada Annabawa ne." Yau an sami wasu marasa daraja suna wulakanta malaman nan da Annabi yayi mana wasici da girmamasu, ta yaya wannan al'umma zata ga abinda take so.

A karshe mu Kanawa mutane ne masu daraja da addini, mun barranta daga wannan Jahilci, bamu aikata ba, wasu bara-gurbin cikinmu ne suka aikata, bamu ji daɗi ba, bama goyon baya, muna Allah wadai da haka.

Ba Fantami ne ya kayar daku a zaben Jahar Kano ba Ganduje ne, ba kuma Malam ne yayi sanadin fara azumin irin na siyasa wa jagoranku ba son zuciyarshi ne, ba kuma Fantami ne ya baiwa kansa muƙamin dake rike dashi wanda kuke hassada ba Allah ne, to mene laifinsa da kuke ƙokarin hallaka shi? Laifin fantami be wuce raddi da yayi wa jagoranku ba na sukar hallitar Allah da yayi. Kuma malam yayi dai dai, domin ba'a kyale mutum indai ya taɓa Allah kowaye.

Masu magana sunyi gaskiya da suka ce" Kowanne tsuntsu kukan gidansu yake yi" kuma kowa yana bayar da kyautar abinda yake dashi ne, wannan mummunar ɗabi'a ta cin mutunci da zage-zage wa Malamai, Sarakuna da manyan gari sai ka wahala kafin samun wanda bai da ita cikin waɗannan yara marasa daraja, (ana samu) domin a haka madugunsu ya ɗorasa kuma koyi suke dashi.

Duk wanda ke bibiyar tarihin siyasa a jahar kano yasan wannan mummunar ɗabi'a ta jagoransu itace silar rasuwar Sarkin Kano na gaskiya Dr Ado Bayero rahimahullah akan mas'alar naɗin wazirci, wanda har yau mu kanawa bamu sami Sarki irinsa ba, kuma bamu daina baƙin cikin rashinsa ba.

In Iskanci kuke ji dashi me ya hanaku yiwa irinsu Dr Yabo Sokoto abinda kuke wa Malam Fantami? Malam yabo da yace "duk Nigeria ba'a taɓa Jahili irin Kwankwaso ba," saboda ɓatanci da akace yayi wa Shugaban halitta S.A.W kenan saboda Yabo ba kanwar lasa bane idan kuka ci mutuncinshi ba zai kyale ba sai yayi wa Jagoranku ninkin yadda kukai masa saɓanin Malam Fantami mai hakuri da kawaici.

Ko a Shekarar 2011 a lokacin data bayyana Kwankwaso ya sami nasarar lashe zaɓen Gwamnan Kano aka sami wasu ƴan iskan gari marasa mutunci maza da mata sukai tsirara suka ɗauki kwalaben giya suka je gidan Sheikh Umar Sani fagge suna mishi Shegantaka wai an kashe shari'a a Jahar Kano.

Tabbas babu abinda ke cikin Kwankwasiyya sai bala'i, musiba da rashin alkhairi, a shekaru shida baya nayi amma yanzu ba nayi, domin na gano Qungiya ce da babu addini,  tarbiyya da kyakkyawar manufa, sai Hassada, ƙyashi da baƙin ciki, babu abinda ake koyarwa sai rashin mutunci, Hegantaka , ta'addanci da aika-aika, yanzu idan kuka hallaka mana Sheikh Fantami a ina zamu sami madadinsa?

Ina tuna shekarar 2011 lokacin da nake Kwankwasiyya idan aka fito "rally" tun sha biyun rana jagorori basa tsayawa suyi sallah har zuwa dare  bayan an gama, sai dai wanda yake so yake yayi kayarsa, amma banda jagororin dake kan mumbari, cashewa kawai suke da waqar Kwankwaso dawo- dawo ko ruwa Baba ruwa, ƙatulan maƙatulan dasu ko kunya basaji, kuma da an fara magana ba wata maganar arziki da ake a wajen banda cin mutunci da habaici. Nagode Allah dana jima da fita daga wannan musiba. Domin duk wanda ke cikinta sai ta illata shi.

Wallahi babu wani cigaba a tafiyar  Kwankwasiyya sai tsantsar riya da propaganda, duk me bibiyar siyasar Kano da idon basira yasan haka, bani da ra'ayin cin mutuncin kowa a siyasa, shi yasa ko Jam'iyya bani da, amma ba zamu lamincewa iskancinku da hegantakarku akan Malamanmu ba, da sannu zamu saka ƙafar wando ɗaya daku a sannan ne zaku san abinda ake nufi da haƙikanin Saukale.

Na rasa meke damun al'umarmu ta arewa mafi yawancinmu ƙiyayya da adawa sun makantar damu, yau mene laifin Dr Isah Ali Fantami don ya karɓi mukamin minista? Siyasa halastacciyar abace, domin zamanin Annabawa da Sahabbai anyi ta.

Don haka kamata yayi ga duk wani mutumin kirki yayi farin ciki da hakan, domin samun Malam a matsayin ministan Sadarwa ba ƙaramin alkhairi bane ga gwamnatin Nigeria da Sauran jama'ar gari, kuma hakan alkhairi ne, martaba ne da gata ga addinin musulunci.

Masu cewa wai don a ramawa kura aniyarta aka baiwa Malam wannan mukami lallai sun cika mahassada, domin Malam baya Nigeria ma a shekarar 2015 da aka gudanar da zabe, yana Saudiyya, kuma malam bai zo gida Nigeria don ya gyara miyarsa ba, yazo ne domin ya hidimtawa ƙasarsa ta hanyar ilmi da baiwa da Allah ya bashi, domin abinda yake samu a can Saudiyya yafi wanda zai samu a nan nesa ba kusa ba.
 
Amma an sami wasu Jahilai munafukai suna sukar Malam wai a matsayinsa na malami be kamata ya shiga Siyasa ba, to ai siyasa bata haramta ba, asalima anfi son mutanen kirki irinsu Malam Fantami su shigeta. Ita kanta kalmar Siyasa an samota ne daga luggar Arabiya, ana cewa masdar dinta  سياسة fi'ili madhi shine ساس mudhari'i kuma shine يسيس fi'ili Amri kuma سس،
masana sukace ta'arifin siyasa shine

" ﻭﻫﻲ ﺍﻟﻘﻴﺎﻡ ﻋﻠﻰ شىء ﺑﻤﺎ ﻳﺼﻠﺤﻪ"

"shine tashi akan wani abu da abunda zai gyara shi."

Idan muka koma harshen turanci ana kiran siyasa da "Politics" "pä-lə-ˌtiks" Noun kenan, koda yake definition na politics nada matukar yawa a wannan harshe, amma bari na dauki guda daya kacal.

"Politics is Activities aimed at improving someone's status or increasing power within an organization"

"Siyasa wata harka ce da aka tsara akan Wasu ayyuka da niyyar tabbatar da matsayin wani, ko karin karfi cikin hadakarJama'a." (Fassara mai 'yanci)

Tsohon Shugaban kasar America na 34th Dwight D. Eisenhower ya bayyana siyasa kamar haka:

"Politics ought to be the part-time profession of every citizen who would protect the rights and privileges of free people and who would preserve what is good and fruitful in our national heritage."

"Ya kamata siyasa ta zama takaitaccen aiki ga kowanne ɗan ƙasa wanda zai kare haƙƙi da gatan mutane masu ƴanci, wanda kuma zai tanadi abinda yake mai kyau da shirya kyakkyawan sakamako a cikin ƙasarmu ta gado"

Dr. Isa Ali Pantami

Siyasa tanada matukar fadi a wannan harshe, akwai political philosophy wanda akafi sani da political theory, da Political science, haka nan idan muka duba litattafai irinsu "The shook doctrine" wanda Naomi Klein ya wallafa, da irinsu "The Rascal King" na Jack Beatty da irinsu "A foreign policy of freedom" cike suke da concepts na Siyasa.

Ashe kuwa siyasa bata nufin komai sai gyara, kishin al'umma da hidimta musu,  umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, jagoranci, gogewa kwarewa a zamantakewa, Iya mu'amala wayewa, Hakuri, rama Alkhairi ga Sharri, Jan ra'ayoyin mutane cikin hikima da dabara, shi yasa duk mutumin daya iya zama da mutane ake ce mishi dan siyasa, wannan yasa Dr Sani Rijiyan Lemo a cikin tafsirinsa ya ta6a cewa" duk duniya ba'a ta6a dan Siyasa kamar Annabi S.A.W ba," wanda maganar ta bawa mutane da dama mamaki, shin mene abun aibu don Dr Fantami yayi siyasa?

shi yasa Alfazazi me Littafin Ishiriniya cikin yabon da kewa Annabi yayi Amfani da Kalmar Siyasa yace"

و ساس بذاك الخلق لينا و شدة

ya Jagoranci mutane, ya sauqaqa a inda ya dace, ya kuma tsananta a inda ya dace.

bayan haka idan muka duba rayuwar Manzo S.A.W da Mulkin Khulafa'urrashidin zamu iske cike yake da  siyasa, idan mutum ya koma littafi irinsu السياسة الشرعية na Ibn Taimiyya ko kuma irinsu

(1)ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺴﻴﺎﺳﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻓﻲ ﺇﺻﻼﺡ ﺍﻟﺮﺍﻋﻲ ﻭﺍﻟﺮﻋﻴﺔ

(2) ﻏﻴﺎﺙ ﺍﻷﻣﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻴﺎﺙ ﺍﻟﻈُّﻠَﻢ

(3)ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻧﻴﺔ ﻭﺍﻟﻮﻻﻳﺎﺕ ﺍﻟﺪﻳﻨﻴﺔ

Duk wanda ya duba wadan nan Litattafai zai gane cewa Addini yana tare da siyasa, idan babu siyasar to Addini bazai samu cigaban da ake so ba, masanin tarihi na ƙasar England George Edward ya siffanta siyasa a matsayin komai da ruwanka inda yake cewa":

 In our age there is no such thing as 'keeping out of politics.' All issues are political issues.

" A wannan Zamani namu babu wani abu da za'a fitar dashi daga Siyasa, dukkanin Lamura lamuran siyasa ne"

idan muka koma Alqur'ani akwai ayar dake cikin suratut tahrimi ayata 8 wacce Allah ke Umarnin Annabi kan yayi Jihadi ga kafurai da munafukai, ya kuma tsananta akan Jihadin,
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺟﺎﻫﺪ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ﻭﺍﻟﻤﻨﺎﻓﻘﻴﻦ ﻭﺍﻏﻠﻆ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﻣﺄﻭﺍﻫﻢ ﺟﻬﻨﻢ ﻭﺑﺌﺲ ﺍﻟﻤﺼﻴﺮ

Malaman tafsiri karkashin wannan ayar sukace Jihadin Addinin musulunci Guda biyar ne, ciki kuwa har da Jihadin Siyasa, wannan jihadin guda biyar sune الجهاد المالى Shine Jihadin fitar da kudi don Taimakawa Addini, da الجهاد التعلمى shine Jihadin Koyar da Ilmi, na Addini kona zamani, sai الجهاد باليد shine Jihadin Amfani da hannu wajen Umarni da Kyakkyawa da hani da mummuna,  الجهاد باللسان shine Jihadin Amfani da harshe wajen fadin gaskiya a inda ta dace, sai الجهاد السياسي shine Jihadin Siyasa, Shine ka shiga Siyasa don ka taimaki Addinin musulunci, kamar yadda malam yayi muke koyi dashi.

Yana daga dalilan daya saka yau  muke cizon yatsa a kasar nan nokewar da malamai da mutanen kirki suka ki shiga a dama dasu a harkokin Gomnati, wannan ya samo asali ne daga kallon da mutane kewa siyasa da 'yan siyasa, aka bar mutanen da basu damu da addini ba suke Jagorantarmu, yau wadan nan shugabanni suke daure gindi ana sabon Allah maimakon hanawa, yau su ke aikata  abubuwan da suka sa6a da addini a bayyanar jama'a, yau su ke Girmama Fasikai da mutanen Banza Maimakon Mutanen Kirki, su ke bari yahudawa ke shigowa da munanan manufofi su yada cikinmu, wannan be ishe mu abun kunya ba?

bazamu ta6a daina cizon yatsa a wannan kasa ba, muddin malamanmu da mutanen kirkin cikinmu basu yunkura sun shigo siyasa don tsaftace ta ba, garemu masu dangwale, Tsohon Shugaban kasar Amurka Abraham Lincoln dai na cewa" The ballot is stronger than the bullet. "kuri'a tafi bullet Karfi da amfani,"

Don haka nagarta itace tushen nasarar komai, ita kuma nagarta ba'a samunta sai da Addini, wannan yake nuna lallai babu mutumin daya cancanta ya shiga siyasa sai mai Addini, shi yasa Gogaggen dan siyasar nan na kasar faransa Alexis de Tocqueville ke cewa"

Liberty cannot be established without morality, nor morality without faith"

" 'Yanci bazai kafu ba batare da nagarta ba, haka nan kuma bazai kafu da nagarta kadai ba, batare da Imani ba"

Ashe bai ishe mu darasi ba yadda kiristoci ke shiga harkar siyasa dumu-dumu a ƙasar nan suna taimakon addininsu tare da cutar da namu addinin? Ko Me yasa saɓanin siyasa baya sa kiristoci sukar mataimakin Shugaban ƙasa Pastor Osinbajo kan shiga siyasa? Bayan ance akwai coci dubunnai a karkashinsa, dalili shine su sunfi girmama addininsu fiye da ra'ayinsu, saɓanin mu da muke fifita son zuciyarmu akan addininmu.

Alaji rainin hankali ne ma ka dubi matashi wayyaye mai ƙwaƙwalwa ɗan boko irin Malam gogagge ƙwararre, jajirtacce hafizin Alqur'ani masanin shari'ar Musulunci, mai hikima da zalaqar zance, mai ɗumbin baiwa kace wai kada ya shiga siyasa, idan su malam basu shiga siyasa sun kyautatawa al'umma da addini ba suwaye zasu shiga?
Mu masoya Malam munsan jihadin can da nayi bayani a sama shine silar shigar Malam siyasa kuma ko yanzu Malam ya bar siyasa kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya farfaɗo da darajar malaman addini da musulunci. Kuma insha Allah indai muna raye Malam yayi ta samun cigaba da daukaka kenan a rayuwarshi. Insha Allah muna ji a jikinmu cewa wata rana Malam sai ya zama Shugaban Nigeria, kuma wannan dama alkawarin Allah ne wa mutanen kirki cikin Alqur'ani.

Allah yace"

ﻭﻋﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻣﻨﻜﻢ ﻭﻋﻤﻠﻮﺍ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺎﺕ ﻟﻴﺴﺘﺨﻠﻔﻨﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻛﻤﺎ ﺍﺳﺘﺨﻠﻒ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻬﻢ"

"Allah yayi alƙawarin wa muminan daga cikinku wadanda sukai kyakkyawan aiki zai basu mulki a ban ƙasa kamar yadda ya bayar ga waɗanda suka gabace su.

A wani wajen kuma Allah yace"

ﻭﻟﻘﺪ ﻛﺘﺒﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺰﺑﻮﺭ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﺃﻥ ﺍﻷﺭﺽ ﻳﺮﺛﻬﺎ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻮﻥ"

"Hakika mun rubuta cikin zabura (littafin Dauda A.S) bayan ambato mulkin kasa wa salihan bayi zamu bayar dashi"

Kalmar  الذكر Wato ambato da tazo cikin ayar nan. Malam Mujahid yace littafin Zabura ake nufi, yayin da Malam Ibn Abbas yace Alqur'ani ake nufi.

DUBA WADANNAN:

Karanta Ma'anar Kalmar VAT a Mahangar Masana? Akan Su Waye Karin Harajin da Gwamnati Take yi Zai Shafa?

Kalli Yadda Aka Kashe Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto A Kan Idona-Inji Direban Sardauna

KARANTA KAMA DARACTAN FILM A KANO ZALUNCI KO ADALCI?

Wata ayar kuma Allah yace"

 ﺇﻥ ﺍﻷﺭﺽ ﻟﻠﻪ ﻳﻮﺭﺛﻬﺎ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻣﻦ ﻋﺒﺎﺩﻩ ﻭﺍﻟﻌﺎﻗﺒﺔ ﻟﻠﻤﺘﻘﻴﻦ

"Shi mulki na Allah ne yana bayar dashi ga wanda yaso cikin bayinshi, amma kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah"

Allah ka taimaki Malam Fantami ka kiyaye shi daga sharrin mahassada kai riko da hannayensa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user