Sunday, 27 October 2019

Karanta Kurakurai 4 da akai a cikin Film din HAFEEZ tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Hafiz

Tsara Labari: Fauziyya D. Sulaiman

Kamfani: Maishadda Global Production Limited

Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda

Umarni: Ali Nuhu

Jarumai: Umar M. Sharif, Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Hassana Muhammad, Maryam Yahya, Amal Umar, Bilkisu Shema, Aisha Humaira, Abba El-Mustafa, Asma’u Sani, Jamila Umar Nagudu, Aisha Yola. Da sauran su.

Sharhin Fim din Hafeez


Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Salma (Aisha Humaira) suna hira da kanwarta Saudat (Amal Umar) a sannan ne kuma mahaifiyar su (Asma’u Sani) ta shigo dakin ta kira Salma da nufin taje wajen bakon saurayin ta Hafiz wanda yazo gidan, jin hakan ne yasa Saudat ta soma yabawa da Hafiz amma sai Salma tayi saurin dakatar da ita ta hanyar gargadin ta akan kada ta shiga sabgar sabon saurayin ta.

Sai dai kuma cikin rashin sa’a, bayan Salma ta fita zuwa wajen Hafiz tun a haduwar farko yaji bata birge shi ba saboda sabanin fahimta da suka samu wanda ya janyo sanadin day a mari Salma din kafin ya bar gidan.

Amma kuma duk da wulakancin da yayiwa Salma mahaifiyar ta bata ji haushin abin ba sai ma laifin Salma din da take gani saboda ta bata mata shiri domin ta kasha kudi masu yawa a wajen malamai don a jawo mata hankalin Hafiz zuwa kan ‘yar ta saboda kasancewar shi dan masu kudi, a dalilin haka ne ma yasa bayan kanwar Salma ta samu mahaifiyar tasu da rokon a shawo mata kan Hafiz ko ita zai saurare ta, mahaifiyar ta su bata bata lokaci ba wajen daukar Saudat din suka nufi gidan iyayen Hafiz.

Amma duk da kasancewar mahaifiyar Hafiz wato Azeema (Jamila Nagudu) ta kasance aminiya ga Mahaifiyar su Salma (Asma’u Sani) Hakan bai sa Azeema tayi kokarin tilastawa Hafiz akan yayi soyayya da Saudat ba, domin shi dan gata ne sosai a wajen iyayen nasa wadanda ba sa son ganin abinda zai bata masa rai. Shima kuma Hafiz ko bayan day a shigo gidan ya hadu da Saudat sai ya fice daga gidan saboda ganin yadda take kallon shi, amma duk da haka sai da Saudat tabi bayan shi zuwa waje inda ta nuna masa cewar tana kaunar shi, nan Hafiz ya watsar da ita ba tare daya karbi soyayyar ta ba.

Shi dai Hafiz ya taso mutum me tsananin farin jini a wajen ‘yammata, duk budurwar da ta gan shi sai taji ya birge ta kuma ta fara soyayya dashi, akwai ba don komai ba sai don kyau da iya kwalliyar sa gami da kudin da mahaifin shi ya mallaka wanda yake takama dasu. Babban abin takaicin kuma shine, Hafiz sam bai taba ganin yarinyar da ta birge shi ba akaf cikin ‘yammatan da suke zub da ajin su wajen nuna masa cewar suna son shi, gaba daya wulakanci yake yi musu bay a basu fuskar da zasu rayu tare, yayin da a kullum iyayen shi ba su da burin da ya wuce su ga yayi aure ya zauna da iyalin sa.

Hakan ne kuma yasa iyayen shi suka bashi goyon baya wajen zuwa ya ga ‘yar abokin mahaifin sa ko zasu daidaita har ya aure ta, amma cikin rashin sa’a Hafiz sai yaga itama yarinyar bat a birge shi ba, hakan yasa yayi mata kyautar kaya yayi tafiyar sa, wanda ganin haka sai ya yiwa mahaifin yarinyar ciwo (Abba Al-Mustafa) saboda yana matukar son Hafiz ya auri ‘yar shi ko don hakan ya zamo sanadin wani cikar burin sa, dalilin hakan ne yasa yaje ya sanar da mahaifin Hafiz wato (Yakubu Muhammad) cewar Hafiz ya amince da auren ‘yar sa, amma ko da mahaifin Hafiz ya tuntube sa sai ya nuna sam ba haka bane.

Ana tsaka da haka ne Hafiz ya hadu da Safna (Hassana Muhammad) wadda ta kasance ‘yar talakawa, tun daga sanda ta taimakawa da Hafiz ruwa ya zuba a motar shi sai yaji ta birge shi har ya kamu da son ta, sai dai kuma tun daga lokaci na farko day a fara zuwa hira wajen ta yaci karo da mahaifin ta Malam Sada (Ali Nuhu) sai hankalin Hafiz ya tashi, domin ya taba cin zarafin Malam Sada ya ture shi da mota har yaji masa rauni kuma ya soma kokarin dukan Malam Sada din.

Ko da Hafiz ya fahimci cewar Malam Sada ne mahaifin Safna sai hankalin shi ya tashi amma son da yake mata ne yasa ya kasa hakuri da ita yayi yunkurin turo iyayen sa, sai dai kuma Malam Sada yaki yarda da auren Hafiz da Safna saboda wulakancin da Hafiz din yayi masa. Ganin yadda Hafiz ya rikice akan son Safna ne hakan yasa iyayen sa suke takaici saboda ba ‘yar masu kudi ya nema ba, amma son da suke yiwa Hafiz ne yasa suka yi ta kokarin ganin cewar an daidaita da mahaifin Safna, ana cikin haka kuma sai aka tashi mahaifin Safna wato Malam Sada daga gidan da yake haya, hakan ne yasa ya hada kan iyalan sa gaba daya ya koma kauye, duk da kafin tafiyar shi, mahaifin Hafiz yayi masa tayin muhalli amma Malam Sada yaki amincewa domin shi mutum ne me zafin zuciya da gudun abin hannun wasu.

Ko da Hafiz ya samu labarin cewa Safna sun koma kauye sai ya gujewa iyayen sa ya tafi kauyen su Safna don neman soyayyar ta. Bayan zuwan Hafiz kauyen ne da yadda yake yin wahala sai abin ya soma bawa Malam Sada tausayi wato mahaifin Safna har daga karshe ya amince da nadamar Hafiz sannan ya bawa Hafiz din dammar turo magabatan sa don ya aura mishi Safna.

Abubuwan Birgewa:

1. Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa sannan an nuna tsantsar soyayya muhimmancin da jajircewa kan abinda mutum yake so.

2. Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin bisa tsari ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari sosai.

3. Sauti ya fita radau, hoto ma ba laifi

4. An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.

5. Wakokin fim din sun yi dadi kuma sun nishadantar.

Kurakurai:

1. Lokacin da Malam Sada (Ali Nuhu) yaje neman rancen kudi a wajen wani me kanti, da kuma lokacin daya dawo gida sa’in da akayi masa rauni a kafar sa, muryoyin jaruman basu hau da bakin su ba a wuraren.

2. An nuna cewar iyayen Hafiz masu kudi ne kuma suna nuna masa gata da tsantsar kulawa, amma kuma lokacin da Hafiz ya gujewa iyayen na sa ya tafi kauye wajen masoyiyar sa, me kallo bai ga sun yi yunkurin neman shi ba. Ya dace a nuna cewar sun watsa cigiyar sa ko da ta kafafen sadarwa ne.

3. Me kallo yaga Hafiz ya taso cikin gata da sangarta daga wajen iyayen sa, wanda hakan ya ba shi damar da ya ke cin mutuncin duk wanda ya so, musamman na sama da shi, amma sai ga shi kuma lokacin da Hafiz ya gane kuskuren da yayi wajen cin zarafin Malam Sada mahaifin budurwar sa, wanda har Hafiz din ya bar gaban iyayen sa don neman soyayya da kuma yafiyar mahaifin budurwar tasa, duk da ganin faruwar hakan amma ba a nuna cewar iyayen Hafiz sun yi nadama ba a bias tafarkin da suka dora dan nasu na rashin tarbiyya, ya dace a nuna cewar sun yi nadama ko don ganin illar da rashin tarbiyya ta ja wa Hafiz wanda abin ya zamo sanadin da Hafiz ya nisance su.

4. Shin wace irin sana’a mahaifin Hafiz yake yi ne? An nuna cewar Hafiz ya taso cikin gata da tunkaho da dukiyar mahaifinsa, sai dai kuma har fim din ya kare ba a nuna irin sana’ar da mahaifin nashi ya ke yi ba wadda ta sa ya mallaki dukiya me tarin yawan da a ke fada.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Kurakurai 4 da akai a cikin Film din NAMIJIN KISHI tare da Sharhin Fim din

Karanta Kuskure 5 da akai a cikin Film ɗin MATAR MAMMAN tare da Sharhin Fim ɗin

Karanta Kuskure 7 da akai acikin Film din KANWAR DUBARUDU tare da Sharhin Fim din

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin ya yi nasara wajen rike mai kallo, sannan kuma an nuna tsantsar soyayya gami da muhimmin darasi a kan wasu matasan masu ji da giyar kudi, wanda hakan ke sa wa su wulakanta makaskanta, yayin da daga karshe su ke yin nadama a kan hakan. Wallahu a’alamu!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Source: LEADERSHIP A YAU 
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user