Turawan Mulkin Mallaka
Marubuci: Datti Assalafy
A lokacin turawan Mulkin Mallaka kaf cikin garin Bauchi babu inda ake siyar da kananzir (Kerosene) sai anje garin Jos ake samu, turawan mulkin mallaka suna aikamu daga Bauchi zuwa Jos mu je mu saya musu kananzir da kafa mu dawo.
Kakana yace min suna tafiyar kwanaki shida su je Jos su sayo kananzir su dawo, tafiya kwana uku, dawowa kwana uku, wannan itace misalin azabtarwan da turawa suka yi ga kakanninmu.
Kakana ya rasu a shekarar 2012 yana da shekaru 109 Allah Ya gafarta masa.
Lokacin ina sakandare, bana manta tarihin da Malamanmu suka bamu akan irin azabtarwan da turawa suka yiwa kakannin mu da yadda suka sace tattalin arzikin Nigeria suka gina Kasarsu.
Sun yiwa kakanninmu mafi munin bautarwa da wulakanci, ba su yarda cewa bakin fata halittace ta dan adam ba, shiyasa suka bautar dasu kamar dabbobi, ance idan suka turasu gona noma baka isa ka tashi tsaye wai don ka huta ba, idan ka tashi bature zai kiraka, ya sa ka zare harcenka, sai ya sa almakashi ya datse maka harce a matsayin horo.
Lokacin da turawan mulkin mallaka suka fara jigilar kakannin mu a jirgi zuwa turai aikin bauta, yadda ake jera kifin sadin a cikin kwali wani na kan wani haka turawa suke yiwa kakannin mu, wanda ya isa da rai shikenan, wanda ya mutu sai a jefashi ruwa, ya zama abincin kifaye da dabbobin ruwa.
Turawan mulkin mallaka sun yiwa kakannin mu kisan kai yadda suka ga dama, sunyi sata iya son ransu, sannan sun yiwa mata fyade na wulakanci.
Yadda 'yan ta'adda suke kwantar da mutane su yanka kamar rago, ko su harbe da bindiga, haka turawan mulkin mallaka suka yiwa kakannin mu, Kakannin mu zasu yi noma a gonakinsu bature idan ya gani sai yace ya zama nashi.
Ya kamata ace gwamnatin Nigeria ta mayar da wannan ranar a matsayin ranar tunawa da 'yan mazan jiya, wadanda suka sadaukar da rayukansu suka ceto kakanninmu daga kangin bauta na turawan mulkin mallaka.
DUBA WADANNAN:
Karanta Sharhin Manyan Masifu Da Bala'in Dake Kunshe Cikin Rayuwar Gidan Yari
KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN KAFUWAR BIRNIN KANO A AREWACIN KASAR NIGERIA
SHIN DA GASKE NE NIGERIA TA KUBUTA DAGA MULKIN MALLAKA?
Muna rokon Allah Ka jikan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Sir Abubakar Tafawa Balewa da makamantansu Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode