Monday, 21 October 2019

KARANTA RA'AYIN 'YAN NIGERIA AKAN GIDAN ABINCI WANDA ZAKA CI FILATE DAYA A ₦30 KACAL

Tura Wannan Zuwa Ga
Mu gayawa kan mu gaskiya, ministan Noma bai kyautawa Talakan kasarnan ba, ba lallai bane ka yarda da abunda zan rubuta, amma ni dai na yarda da zancena gaskiya ne.

Abincin ₦30 ya haifar da kace-nace a Media


Marubuci: Haji Shehu

Duk irin tsadar rayuwa, da halin matsi da Talakan Najeriya yake fuskanta minista bai gani ba, kuma baiji ba, har yake ikirarin cewar Naira 30 zata ciyarda mutum a jihar Kano, kuma wai kukan yunwa da yan Najeriya keyi shagwaba ce. Wannan kalamai na minista abun Allah wadai ne ba wai abunda zamuyi wasu dasu bane.

Mutane da dama sun maida waɗannan kalamai abun wasa ko zolaya ba tare da duba su ta fuskokin basira ba, ba tare da jirkita su ta bangarorin da zasu shafi rayuwar talaka da gudanar da gwamnati ba. Wannan kalamai na minista sun nuna a fili Qarara cewar ba zai iya isarda koken talaka ba a majalisar ministoti, ba zai iya fadawa shugaban kasa gaskiyar halin matsi da talaka yake ciki ba.

Karanta Illolin da Kabilar IGBO ta yiwa Sauran Kabilun Nigeria Wanda Hakan Zai Iya Haifar da Matsala anan Gaba

Ko shakka babu, Ministan Naira 30 sune irin ministotin dake boyewa shugaban kasa gaskiyar halin da talakawa ke ciki, na tabbata yadda ya saki baki ya gayawa duniya wannan maganar zai iya fadin fiye da haka a majalisar Ministoti.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user