Saturday, 16 November 2019

Karanta Muhimman Abubuwan da Yakamata Ku sani Kafin ku Fara yin Taimako

Tura Wannan Zuwa Ga
TAIMAKO baiwace mai matukar tsada wanda ba kowa bane ALLAH yake bashi ikon taimakawa ba domin ba kowa ne yake da arzikin wadatar zuci ba.

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Sau da dama aduk sanda aka ambaci wannan kalma ta Taimako mafi yawan tunanin mutane yafi karkata zuwa ga neman wani abu musamman na daga arzikin dukiya wato kudi.

Sai dai abun ba haka yake ba hanyoyin Taimako suna da yawa, bawai kawai ka bawa mutum kudi shine ka taimaka masa ba. Kada kayi tunanin baka da hanyar taimakawa dan'uwanka musulmi saboda ka kasance daga cikin matalauta, ka sani cewa bada Dukiya (kudi) kawai ake taimako ba.

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Akwai hanyoyi da yawa daga ciki:

1. Kana iya taimakawa dan'uwanka ta hanyar karfi da lafiya da ALLAH ya wadata ka dashi.

2. Kana iya taimakawa dan'uwanka ta hanyar ilimin da ALLAH ya hore maka walau kai malami ne ko dalibi ne ko likita ne koma dai wani fanni ALLAH ya baka ikon fahimta zaka iya bada taimako dashi.

3. Kana iya taimakawa dan'uwanka ta hanyar addu'a musamman wacce kayita ba tare da ya sani ba. Ni a ganina ma wannan itace koluluwar gaba mafi girma domin idan ALLAH Ya amsa addu'ar da kayiwa dan'uwanka yafi masa daraja sama da bashi wannan duniyar da abunda ke cikinta.

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Akwai abubuwa da yawa wanda bawa zai iya taimakawa dan'uwansa dashi bawai sai da dukiya (kudi) kawai ba.

Acikin Al-Qur'ani Maigirma ALLAH (SWT) Yace: 

ﻭَﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒِﺮِّ ﻭَﺍﻟﺘَّﻘْﻮَﻯ ﻭَﻻ ﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻹِﺛْﻢِ ﻭَﺍﻟْﻌُﺪْﻭَﺍﻥِ ﻭَﺍﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺷَﺪِﻳﺪُ ﺍﻟْﻌِﻘَﺎﺏ

“Kuma ku taimaki juna akan aikin kwarai da takawa, kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da zalunci, kuma kubi ALLAH da takawa, lallai ne ALLAH mai tsananin ukuba ne.” [Ma'idah: 02].

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Wannan ayar ta kara fito mana da cewar bawai Dukiya (Kudi) dashi kawai ake taimako ba, balle daga an ambaci taimako ka zumbura baki saboda kana tunanin zaka bada taimakon kudi dukiyarka zata ragu. Akwai mutanen da suka daina Ziyartar masallatai da wuraren wa'azi wai don kawai ana ambaton neman taimako.

Shi fa taimakon nan ba ace dole sai ka bayar ba idan kana dashi ka bayar idan baka dashi kayi addu'a.

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Duk wanda ya samu wata dama daga cikinku da zai amfanar da dan'uwansa, to ya aikata.”

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Akwai Hadisai da dama da suka yi magana akan Falalar da mutum yake samu idan ya kasance yana Taimakon dan'uwansa daga ciki:

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Lallai ALLAH yana cikin taimakon bawa matukar bawa yana cikin taimakon dan'uwansa.” [Muslim].

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Mafi aikin alkhairi a wajan ALLAH, shine sanya dan'uwanka cikin farin ciki ko ka biya masa bashi ko ka ciyar da shi abinci.” [Sahihul-Jamee].
Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Ashe sanya dan'uwanka farin ciki shima taimako ne, hakanan akwai hadisin da ya tabbata cewa yiwa dan'uwanka murmushi ma sadaka ne.

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Duk wanda ya taimaki wanda yake cikin kunci, ko ya dauke masa wani nauyi da yake akansa, ALLAH zai sanya shi a inuwarsa, a ranar da babu inuwa sai Inuwarsa.” [Sahihul-Jamii].

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: “Dukkan wanda ya saukakawa wanda yake cikin kunci, shima ALLAH zai saukaka masa anan duniya da Lahira.” [Sahihul-Jamii].

Hanyoyin Taimako Suna da Yawa

Ashe saukakawa dan'uwanka game da wani kunci da yake ciki shima taimako ne, Hakika akwai hadisai da dama da suka yi magana game da falalar da mutum yake samu ta hanyar taimakawa dan'uwansa musulmi.

Don haka mu sani ba wai ta hanyar Dukiya ce kadai ake taimakawa ba, akwai hanyoyi da yawa kuma muyi kokari wajen taimakawa junan mu ta hanyoyin da zai amfani junan mu bisa tafarkin ALLAH (SWT).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Amfanin Sada Zumunta Guda 20

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

KARANTA FA'IDODIN SADAKAH GUDA TALATIN DA UKU 33

Wadanda suke kokari wajen taimakon bayin ALLAH ta hanyar dukiyarsu da ilimin su da lokacin su da duk wata hanyar dama da ALLAH ya basu, ALLAH Ya saka musu da alkhairi (Ameen).

ALLAH Ya sanya mu cikin bayinsa masu taimakon Junansu, ALLAH ya bamu ikon kyautatawa da amfanarwa (Ameen).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user