Zagayen Takutaha
Marubuci: Fatuhu Mustapha
Birnin Kano a wannan lokaci ya shahara ne a matsayin wurin bauta, dake cike da addinai kalakala. Wadanda suka hada da ; masu bautar ruwa, wadanda ke zaune a Bakin Ruwa, kuma asalinsu sun taso daga kasar Gaya ne. Wadannan suke ke bautar ruwan jakara. Kuma sun amince shine yake tsaresu daga dukkan wani balai da zai taso musu, ko kuma ya taso ma garinsu.
Akwai masu bautar farji, wadanda ke zaune a Dutsen Bompai, wadanda aka fi sani da Gwandarawa, sukan yi wa azzakarin limaminsu, farjin limamiyarsu sujada (ba lallai irin ta musulunci ba). Kuma addinin nasu cike yake da raye-raye da kade-kade. Shine asalin ake kiransu da Gwandarawa wato: Gwanda-rawa-da-sallah.
Wani nau'in addinin shine Adzna ko Arna. Wadanda ke Gwabron Dutse. Su wadannan sune masu bautar Ubangiji. Wato wani Allahnsu ne da suke bautawa, Wanda a zatonsu yana ko ina. Haka kuma suna da gumaka da suke bautawa a matsayin wakilan Shi wannan ubangiji. Ita wannan kalma, ita ce malaman musulunci suka amsheta, suka nuna cewa ba Wanda ya cancanci wannan siffa ta ubangiji in banda Allah (domin shine yake ko ina, ilminsa ya game komai).
Addinin da yafi kowanne karfi da shahara, kuma manyan sarakunan kasar Kano dake da helikwata a Santolo suke bi, shine addinin maguzanci. Wanda babban wurin bautarsu ke kan Dutsen Dala. Masu bin wannan addini su ake kira Maguzawa, Farfesa Murray Last a kasidarsa maitaken : Historical Metaphor in the history of Kano ya bayyana cewa asalin sunan, ya samo ne daga "Majus " wato majusawa. Wadannan bayin Allah na bautar iskokai ne, wato aljannu. Musamman wata aljanna da ake kira Tsumburbura, ko kuma Danko. Malam Adamu na Maaji ya bayyana a littafinsa I'lan bi Tarikh Kano cewa, asalin wannan aljan ana bauta mata tun zamanin Annabi Nuhu, inda ya tabbatar da cewa ita ce 'Yaquqa ' da aka fada a alqurani, cikin suratul Nuh.
Akwai kuma masu bautar Bishiya da aka fi sani da Gazargawa, wanda sheikh AbdurRahman Zagaiti ya sha fama da su. Sune ke zaune a Shirawa, akwai cikakken bayani akan wannan rigima a kundin nan maisuna: Waraqa makatuba, fiha asl al wangariyun ".
Akwai sauran addinai da dama wanda Malam Nasiru Kabara ya yi dogon bayani akan su, a wani kaset na waazinsa da ya Maida martani ga malaman Izala akan gudunmowar sufaye a wurin yada addinin musulunci a Kasar Kano. (Abin bakin ciki na nemi kaset din na rasa).
Dokar kasar Kano a wannan lokaci shine: tunda kasa ce mai tsarki ta gamayyar addinan Hausawa, da suke aikin hajji duk shekara acikinta, kuma malamnsu da limamansu duk na ciki, to baa yadda kayi noma acikinta ba, ba kuma a yadda kayi farauta acikinta ba. Duk yayi wannan to zaiyi fuskantar fushin Allolinsu ko kuma ya fuskanci yaki daga Sarakan Kasar dake zaune a Santolo (wato Tsakuwa kenan dake karamar hukumar Dawakin Kudu a yau). Wannan dalilin ne ya sanya Shi kansa limaminsu mafi shahara (Barbushe), yake tafiyar wuni domin ya farauto nama. Saboda ba damar yin farauta a garin Kano da kewaye. Hakan ta sanya kqbilar Doma suka bar gari saboda mafarauta ne, suka koma Kazaure, karkashin jagorancin shugabansu maisuna Kazaure.
Yunkurin Bagaudawa;
Farkon Wanda suka fara yunkurin rusa wannan addinai sune Abagayawa, asalinsu makera ne da manoma, sukan kuma taba farauta. A wannan lokaci saboda bukatar sabon wurin noma da kuma neman karfe domin kara fadada sanaarsu, ta sanya dole su fara neman sabon wuri, inda zasu samu kasa mai yalwa, da kuma isasshen karfe. Ba kuma inda yake da wannan abubuwa in ba Kano ba. Gashi kuma baa noma a kasar Kano, kuma baa farauta, ba kuma dama a haki maadaninta. To amma fa, dan wuya ba zaa bar dadi ba.
Zuwa Bagauda Kano ya tabbatar da shi fa yaga, domin yaga akwai karfe a kasa, ga kuma kasar noma mai albarka, sannan ga dabbobi kala kala. Don haka ya yanke shawarar Shi fa, sai dai ayi wacce zaayi, amma dole a barsu, su cigaba da rayuwa a kasar Kano. Kuma dole su noma kasa, dole su hako karfe, dole kuma a barsu suyi farauta, don ba zasu bar nama a banza ba.
Wannan yunkuri na Bagauda da mutanensa, ya jawo musu tsangwama daga sarakunan Santolo da kuma tofin Allah tsine daga manyan limaman Kano. Koda yake da farko Bagauda ya keta doka yayi yanda yake so, amma baa jima Santolo ta zo da runduna mai karfi ta fatattake shi, inda ya sha da kyar, ya tattara yanasa-yanasa ya koma Shema a kasar Kazaure, acan ya mutu!
Sai dai wannan fatattaka da akayi masa ya bar baya da kura, domin ya haifar da gadajjiyar gaba tsakanin Bagaudawa da manyan addinan Kano, inda suka sha alwashin ko bajima, ko badade, sai sunga bayan wadannan addinai. Sun shafe kusan shekara 100 da doriya suna mulki a kasar Kazaure, kafin daga baya dama ta samu a zamanin Gajimasu su dawo su kafa garin kano.
Bawata cikakkiyar bayani, akan ko ya akai suka dawo, cikin Kano, domin kundin Tarikh Arbab bai bada wani bayani cikakke ba akan yadda sukayi nasarar dawowa cikin garin Kano, da maido da masarautarsu, amma alamu na nuna cewa, a wannan lokaci karfin Santolo yayi rauni ainun! Kila ko saboda yake yake da ya addabe su, musamman da daulolin Tumbi da kuma Washa, ko kuma da Zazzau. Kila hakan ne ya sanya aka bar shirayin Kano ba wani tsayyayen tsaro da zai kareta, daga mamayar Bagaudawa.
Koda yake Bagaudaw sun dawo Kano, amma kuma sai ga shi basu samu yadda suke so, na murkushe tsoffin abokan gabarsu ba. Duk wani yunkuri da suka yi na tabbatar da mulkinsu, abin yaci tura. Shi kansa Zamnagawa (usmanu) da yayi yunkurin farko, bai kare lafiya ba.
Yunkurin Musulunci
Acikin wannan hali ne, a wata shekara zamanin sarkin Kano Yaji dan Tsamiya, wasu malaman Wangarawa karkashin jagorancin sheikh AbdurRahman Zaiti suka zo, Kano, baya ga musulunci da kuma kasuwanci, suna kuma da sabbin makamai da dabarun yaki da baa san da su ba a Kano. Wannan ya sanya Bagaudawa suka karbi musulunci, domin su samu hadin kan wadannan baki, su taimaka musu su yaki abokan gabarsu. Kwana daya da zuwansu Sarkin Kano Yaji ya karbi musulunci, ya kuma canjawa kansa suna zuwa Ali. Wanda hakan ke nuna, cewa , shirin yaki zaayi, domin ana cewa Ali bin Abu Talib shine sarkin yakin manzon Allah (saw).
A farkon watan Rabiul Awwal na wannan shekara, ne Yaji ya tara dukkan maguzawa, ya kuma karanta musu dokar-ta-baci. Inda yace musu
"Ku sani, daga yau, komai tsakanina daku, sai yaki da tsinin mashi, ba yaudara, bawani boye boye, domin ba mayaudari sai matsoraci, ku shirya gani nan zuwa gareku "
Mataki biyu suka dauka, na farko sunyi kokarin bada cin hanci ga Sarki Yaji, amma yaki karba, yace a maida musu baya so. Na biyu, sai suka koma ga Tsumburbura, domin neman nasara, amma ta gaya musu, cewa wannan yaki ba nasara, domin lokacin karshen addininsu a kasar Kano yazo.
Acikin watan dai, rundunar musulmi suka fuskanci, rundunar maguzawa, a gefen Dutsen Dala, inda suka hadu, aka gwabza. A wannan lokacin ne, Jarmai Bajere ya samu nasarar Kutsa kai cikin shigifar Tsumburbura, inda ya samu wani halitta na tsaye, rike da maciji a hannunsa, ya daga mashi ya bugawa halittar nan, tayi kuwwa ta fito a guje. Nan da nan suka bita, inda ta nufi kofar ruwa, ta fada cikin ruwan Dankwai. Wannan Shi ya kawo karshen Tsumburbura, da kuma addinin maguzawa a garin Kano.
MAKALOLI MASU ALAKA:
Karanta Jerin Sunayen ’Ya’yan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero
KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN ATTAJIRI NA DAYA A AFIRKA ALHALIKO DANGOTE
Karanta Jerin Abinci Hausawa Kafin Zuwan Shinkafa 'Yar Kasashen Waje
Takutaha
Samuwar wannan Nasara, ba karamin abu bane a wurin musulman Kano. Wanda aka shafe sama da shekaru 100 ana nema. A dalilin haka ne, ya sanya musulman kanawa duk shekara, sukan taru su hau Dutsen Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci. Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe addinin kafirai. Domin kafin zuwan musulunci, ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci, yanzu kowa ma sai ya hau, ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake takutaha a duk shekara a Kano, Wanda wasu da basu san tarihin ba, ke ganin jahilci ne, ko kuma abu ne, da ya sabawa musulunci.
Allah ya sa mu dace Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.
Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode