Wednesday, 6 November 2019

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

Tura Wannan Zuwa Ga
A rayuwa dole ne sai ka zamo mai shuka dayan abubuwan nan Alkhairi ko Sharri, ta yadda daga karshe kuwa za ka samu sakamakon aikin ka.

Abinda Ka Shuka Shi Zaka Girba

Marubuci: Idris M. Rismawy

Kai Uba ne kuma jagora ne sannan Kaine Shugaba kuma Namiji , kamata yayi kari ke girman da Allah yabaka, wajan nuna dattaku tare da tsare mutuncin ɗiyar mutane domin kai ma Allah yatsare maka naka.

DAN UWANA MAI ALBARKA

Ya kamata kasan da cewa ita rayuwar duniya zagayowa takeyi sai kaga ta zãga kuma ta zãgayo sannan sai ta tsaya a kanka domin ta aikata maka abinda ka aikatawa wanin ka. Ko ta aikatawa ɗiyarka, matarka, ko 'yar uwarka irin abinda ka aikatawa ɗiyar wanin ka ko matarsa ko kuma 'yar uwar sa.

Ka ji tsoron Allah wajan lalata tarbiyyar ɗiyar mutane a fili ko a ɓoye, ka guji wargaza rayuwar ɗiyar mutane, yarinya mai tarbiyya mai kamun kai amma kabi duk yadda za ka iya bi domin cimma bukatar ka. ( YA ALLAH KA KARA TSARE MANA IMANIN MU).

Ka lalata mata rayuwa, ka hargitsa tunaninta kuma ka rushe duk wani ginin tarbiyyar da iyayenta, malamanta da kuma sauran 'yan uwanta suka ginata akai. Ka ki tabbatar da cewa Allah yana kallonka kuma da sannu zaiyi sakayya akan haka.

ME KAKE TUNANIN ZAI BIYO BAYAN HAKA?

YA 'YAR UWATA MAI DARAJA

Karki zama mai kwaɗayi musamman ga abin yake a hannun duk wani Namijin waje, kar ki ɗorawa rayuwarki dole sai kinyi kaza da kaza saboda kinga wance ta yi, kizama mai kamun kai mai auna magana alokacin fitar ta, kuma kizama mai shiga irin ta Addinin Islama, ki zamto mai kunya da yawan kau da kãy musamman ga abinda bai shafeki ba.

Allah ya karramaki, ya bãki girma, ya daraja ki, kuma ya ni'imta ki da ni'imar Addinin Islama, sannan kuma yabaki hankali da tunani domin tantancewa da kuma warware zare da abawa tsakanin fari da baki, abu mai amfani da mara amfani, da kuma cancanta da rashin ta, kuma ke mace ce. To kamata yayi kiyi amfani da su domin rayuwarki tayi kyau sosai da armashi.

Tunda Allah yayi miki wannan baiwar kuma iyayen ki sun bãki tarbiyya da kulawa mai tsafta, to karki bari wani watsatstse ya watsa tarbiyyarki, yazubar miki da mutuncinki a Idanuwan duniya kuma ya lalata rayuwar ki a banza. Ta yadda Zaki zamto abar kwatance, duk inda kikabi ke ce ake nunawa domin watsewar ki tayi muni Subhanallah.

MAKALOLI MASU ALAKA:




A karshe kuma sai ki zama abar tausayi, kullum a cikin nadamar da bata da amfani, domin da muguwar rawa gwamma kin tashi. Kai kuma Allah bazai kyale ka haka ba, kaima sai Ya juyo wajan ka kuma an aikata kwatankwacin abinda ka aikatawa ɗiyar mutane akan ɗiyar ka ko 'yar uwar ka.

YA ALLAH KA SHIGA TSAKANIN NAGARI DA MUGU, KA KARA TSARE MANA IMANINMU SANNAN KASA MUCIKA DA KYAU DA IMANI AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user