Yayin Zaman Tahiya
HUKUNCINSA
Shi li’itikafi sunna ce mai karfi, kuma a goman karshe na watan Ramadan ake yin sa. Amma yin sa a wani watan mustahabbi ne.
"فَقَدْ كَانَ النَّبِي صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَعْتَكِفُ فِي كُلِّ رَمَضَانَ عَشَرَةَ أَيَّامٍ، فَلَمَّا كَانَ الْعَامَ الَّذِى قُبِضَ فِيهِ اعْتِكَفَ عِشْرُونَ يَوْمًا. (رواه البخارى)
Ma'ana:
Hakika, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yin li’itikafi a kowane watan Ramadan kwana goma, amma da shekarar da zai yi wafati ta zo, sai ya yi kwana ashirin.
(Bukhari ne ya rawaito).
FALALARSA
Shi li’itikafi ibada ne mai girma wanda yake tsarkake zuciya ga barin shagala da duniya kuma yana sa mutum ya dukufa wajen neman lada da kyakkyawar makoma.
SHIGARSA
Ana son shiga li’itikafi kafin faduwar ranar da za a fara.
MAKALOLI MASU ALAKA:
KARANTA ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI
KARANTA RANAKUN DA AKA HANA YIN AZUMIN NAFILA
KARANTA HUKUNCIN MAI AZUMIN DA YA CI ABINCI DA MANTUWA
AYYUKANSA
Ana son mai li’itikafi ya shagala da yin ibada kamar nafilfili, karatun Alkur’ani, tasbihi da hailala, zikiri, istigfari, salatin Annabi da sauran ayyukan bin Allah.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.
Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng