Falalar Salati Ga Annabi Muhammad (S.A.W)
Marubuci: Mustapha Musa
(Don haka ku Yawaita yin Salati a Gareni a Cikinta, domin Ana Bijuro da salatinku Gareni).
@Saheehu Abu Dauda.
Annabi (ﷺ) Yana Cewa:
Duk Wanda Yayi Salati a Gareni, Allah zaiyi masa Salati Guda Goma.
@Saheehul Jami'i.
KADAN DAGA CIKIN FALALAR SALATI GA ANNABI (ﷺ).
1-Wanda yayiwa Manzon Allah (ﷺ) Salati ya cikasa Umarnin Allah ne dayiwa dukkan masu imani.
2- Kuma ya yi koyi cikin Abinda Allah da Mala'ikunsa sukeyi ga Annabi (ﷺ).
3- Wanda yayi Salati Guda ga Annabi (ﷺ) Allah zaiyi masa Guda Goma.
4- Za'a Rubuta Masa Lada Guda Goma kuma a kankare masa Zunubai Guda Goma.
5- Za'a Daukaka Darajarsa Sau Goma.
6- Allah yana Amsa Adduar da Akayi tare da Salatin Annabi (ﷺ) A Cikinta.
7- Mai Yawan Yi Masa Salati Yana Samun Ceton Manzon Allah(ﷺ).
8- Hanyace ta samun Gafarar Allah.
9- Hanyace ta Samun kariya da tsaron Allah ga mai yawaita salati ga Annabi (ﷺ).
10- Manzon Allah (ﷺ) Yana mayar da Salati ga dukkan wanda yayi masa Salatin.
11- Yin salati ga Manzon Allah (ﷺ) a wajan Zama yana sanyawa Mutum Rashin Asara a Ranar Alkiyama.
12- Hanyace ta Magance Talauci.
13- Mai Yawaita Salati ga Annabi (SAW) duk lokacin da aka Amabaci Sunansa, mai wannan halin baya cikin Marowata.
MAKALOLI MASU ALAKA:
Karanta Yadda ake Yin Salatin Annabi Muhammad (SAW) a Mahangar Sunnah
KARANTA YADDA LITTAFIN BIBLE YA TABBATAR DA ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)
KARANTA HUDUBA MAI RATSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI TA ANNABI MUHAMMAD (SAW)
Kuma ya Kuɓuta daga Addu'ar Dauwama cikin Azaba ga Dukkan Wanda aka Ambaci Sunansa baiyi masa salatiba.
14- Samun kusanci ga Annabi (SAW) a Ranar Alkiyama.
15- Annabi (SAW) yana Sanin duk Wanda Yayi Masa Salati.
16- Samun Rayuwa mai Dadi.
ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠﻰ ﻣُـﺤﻤَّﺪٍ ﻭﻋﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُـﺤﻤَّﺪٍ،ﻛَﻤَـﺎ ﺻَﻠَّﻴﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇﺑْﺮَﺍﻫِﻴْﻢَ ﻭﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇﺑﺮﺍﻫِﻴْﻢَ،ﺇﻧَّﻚَ ﺣَﻤﻴﺪٌ ﻣَﺠﻴﺪٌ،ﺍﻟﻠﻬُﻢَّ ﺑَﺎﺭِﻙْ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤﻤَّﺪٍ ﻭﻋَﻠﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤﻤَّﺪٍ،ﻛﻤَﺎ ﺑَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫِﻴْﻢَ ﻭﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇﺑْﺮﺍﻫﻴﻢَ،ﺇﻧَّﻚ ﺣَﻤِﻴْﺪٌ ﻣَﺠِﻴْﺪ.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.
Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng