Mai Girma Sarkin Kano Sunusi Lamiɗo Sunusi ll da Sauran Sababbin Masarautu
Marubuci: Bashir Abdullahi El-bash
A Ranar Litinin, 9 ga watan Disamba, 2019.
A ƙarƙashin dokar da ta samar da masarautun Jihar Kano ta shekarar 2019, sashe na 4 cikin baka ta (2) da baka ta (g) da kuma sashe na 5 cikin baka ta (1) da ta (2) wacce ta ba wa mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje dama, mai girma gwamna ya amince da waɗannan naɗe-naɗe kamar haka: ya zaɓi mai martaba Sarkin masarautar Kano, Mallam Muhammadu Sunusi Lamiɗo Sunusi a matsayin sabon shugaban majalissar sarakunan Jihar Kano, (Chairman Kano State Council of Chiefs).
Membobin majalissar sun haɗa da: dukkan sarakunan masu daraja ta ɗaya na sauran masarautun guda huɗu waɗanda su ka haɗa da na Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da na Rano Alhaji Dakta Tafida Abubakar (Autan Bawo) da na Ƙaraye Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar Na Biyu da kuma na Gaya Alhaji Ibrahim Abdulƙadir, waɗanda dukkaninsu membobi ne kai tsaye cikin majalissar sarakunan kamar yadda doka ta tanadar.
Sannan kuma sashe na 4 cikin baka ta (2) ya tanadar da ƙarin membobin majalissar waɗanda su ka haɗa da: sakataren gwamnatin Jiha da kwamishinan ƙananan bukumomi da kuma shugabannin ƙananan hukumomi guda 5 wanda kowane ɗaya daga cikinsu ya na cikin majalissar sarki a kowacce masarauta.
Kamar yadda sashen dokar ya tanadar, sauran sun haɗa da ƴan majalissar sarki a ƙalla guda goma, guda bibbiyu daga kowacce masarauta da kuma kowane babban limamin kowacce masarauta kamar yadda sashe na 3 cikin baka ta (1) ya tanadar.
Sauran sun haɗa da wakilan ƴan kasuwa daga kowacce masarauta waɗanda gwamna zai naɗa, ya kuma naɗa Alhaji Alhaji Ɗalhat Al-Hamsad da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano daga cikin waɗanda za su kasance cikin membobin majalissar sarakunan.
Sannan kuma ƙunshin dokar ya tanadar da shigar da wakili daga majalissar malamai ta Jiha da kuma wakilai daga hukumomin jami'an tsaro na ƴan sanda da na farin kaya da kuma na tsaron fararen hula waɗanda dukkaninsu ba za su wuce mutum bibbiyu ba. Sauran membobin da gwamna Ganduje ya naɗa sun haɗa da Alhaji Nasiru Ali Ƙoƙi wakili daga majalissar malamai ta jiha, sai kuma sakataren majalissar sarakunan wadda kuma ita majalissar ce za ta zaɓa da kanta.
Haka zalika, sashe na 5 cikin baka ta (1) da ta biyu cikin ƙunshin dokar, ya tanadar da wa'adin shekaru biyu ga duk sarkin da aka zaɓa a matsayin shugaban majalissar sarakunan, inda shugabancin zai dinga zagayawa a tsakanin sarakunan a duk bayan shekara biyu.
Kuma duk waɗannan naɗe-naɗe za su fara aiki ne nan take daga wannan rana ta Litinin, 9 ga watan Disamba, 2019. Sannan kuma an buƙaci shugaban majalissar sarakunan da ya kira zaman farko na ƙaddamar da majalissar ba tare da wani jinkiri ba kamar yadda doka ta tanadar.
MAKALOLI MASU ALAKA:
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.
Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.
Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng