Friday, 27 December 2019

Karanta Addu'ar Gamuwa da Abokin Gaba Ko Wani Mai Iko

Tura Wannan Zuwa Ga
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ .

Allahumma inna naj'aluka fee nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim.

Ya Allah! Mu mun sanya ka a gabansu, kuma muna neman tsarinka daga sharrace-sharracensu.

Addu'ar Gamuwa da Abokin Gaba ko Wani Mai Iko
Hoto: Sound cloud

اَللَّهُمَّ أَنْتَ عَضُدِي، وَأَنْتَ نَصِيرِي، بِكَ أَجُولُ وَبِكَ أَصُولُ وَبِكَ أُقَاتِلُ.

Allahumma anta 'adudee, wa-anta naseeree, bika ajoolu wabika asoolu wabika oqatil.

Ya Allah kai ne mai karfafa ni, kuma kai ne mataimakina, da karfinka ne nake yin dabarun yaki, kuma da karfinka ne nake kai hari, kuma da karfinka ne nake yin yaki.

حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.

Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.

Allah ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro.

اَللَّهُمَّ رَبِّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبِّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَارًا مِنْ (فُلاَنٍ)، وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلاَئِقِكَ؛ أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى، عَزَّ جَارُكَ، وَجَلَّ ثَنَاؤُكَ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ.

Allahumma rabba s-mawati s-sab'i wa rabba-l-'arshi-l-'azimi. Kun li jaran min (fulanin) wa ahzabihi min khala'iqika, an yafruta 'alayya ahadun minhum aw yatgha. 'Azza jaruka, wa jalla thana'uka, wa la ilaha illa anta.

Ya Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, ka kasance mai tsari gare ni daga wane dan wane, da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare haddi, kariyarka ta buwaya, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai kai.

اَللهُ أَكْبَرْ، اَللهُ أَعَزُّ مِنْ خَلْقِهِ جَمِيعاً ، اَللهُ أَعَزُّ مِمَّا أَخَافُ وَأَحْذَرُ، أَعُوذُ بِاللهِ الَّذِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ، الْمُمْسِكِ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ أَنْ يَقَعْنَ عَلَى اْلأَرْضِ إِلاَّ بِإِذْنِهِ، مِنْ شَرِّ عَبْدِكَ فُلاَنٌ، وَجُنُودِهِ وَأَتْبَاعِهِ وَأَشْيَاعِهِ، مِنَ الْجِنِّ وَاْلإِنْسِ، اَللَّهُمَّ كُنْ لِي جَاراً مِنْ شَرِّهِمْ، جَلَّ ثَنَاؤُكَ وَعَزَّ جَارُكَ، وَتَبَارَكَ اِسْمُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ " ثَلاَثَ مَرَّاتٍ.

Allahu akbaru. Allahu a'azzu min khalqihi jami'an. Allahu a'azzu mimma akhfu wa ahdharu. A'udhu billahi lazee la ilaha illa huwal mumsikis samawatis sab'i an yaqa'na 'alal-ardi illa bi'izinihi, min sharri 'abdika (fulanin) wa junudihi wa atba'ihi wa ashya'ihi minal-jinni wal-insi. Allahumma kun li jaran min sharrihim Jalla thana'uka wa 'azza jaruka, wa tabaraka smuka, wa la ilaha ghayruka. (3).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Addu'ar Maganin Damuwa da Bakin Ciki

Karanta Addu'a Ga Wanda ya Razana a cikin Bacci Da Wanda Ya Kasa Yin Bacci

Karanta Addu'ar Tafiyar Da Kuncin Zuciya

Allah shi ne mafi girma, Allah shi ne mafi buwaya daga dukkanin halittarsa, shi ne mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin Allah, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai rike sammai daga su ruguzo a kan kasa sai da izininsa, daga sharrin bawanka wane (ya ambai sunansa), Ya Allah! Ka zamo mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma kaiyarka ta buwaya, kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba. (sau uku).
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user