Thursday, 26 December 2019

Shin Ko ya Dace Musulmi ya Karbi Kyaututtukan Ranar Kirsimeti?

Tura Wannan Zuwa Ga
Da yawa Musulmi suna tambayar shin ko ya halatta su karɓi kyautar kiristoci a ranar kirsimeti, musamman wandanda suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki a guri ɗaya.

Baya Halatta GA Musulmi yaci abin yankan su

Ga bayanin da Malamai suka yi dangane da haka:

1. Baya halatta ga Musulmi ya nuna farin cikin sa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantan su.

2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.

3. Ya halatta ya karbi kyautar da za su bashi a wannan ranar. Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi waɗanda ba yankawa ake yi ba, Kamar kayan marmari.

4. Dalili kuwa shi ne:

A. Baihaqi ya ruwaito a cikin littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bn Sirin ya ce: an kawo wa
Ali, Allah ya kara yarda a gare
shi, kyautar idin majusawa Nairuz.

Sai ya ce: me ne ne wannan kuma? Sai suka ce masa, ya Sarkin
Muminai yau ranar idin Nairuz ce. Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar.

B. Ibn Abi Shaibah a cikin littafin sa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk
ranar bukukuwansu suna aiko masa da
kyaututtuka gidan sa, sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to ku ci, wanda kuma ba kayan marmari bane, to ku mayar musu kayan su.

C. Haka kuma ya ruwaito 5/126 cewa: wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta.

Sai A'isha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce mata, abin da aka yanka domin wannan ranar kada ku ci. Ku ci kayan marmari na itatuwa.

Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautar su. Karbar kyautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk hukunci ɗaya ne, domin wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Dalilai 13 Da Suka Sa Na Musulunta- Inji Emmanuel Adebayo Dan Kwallon Kafa

KARANTA YADDA LITTAFIN BIBLE YA TABBATAR DA ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Shin me kasani dangane da Takaitaccen Tarihin Addinin Kirista? Shin me ne ne Alakar Addinin Kirista da Addinin Musulinci??

Sannan a ƙarshe yana da kyau mu fahimci cewa, Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar.

Kuma koda musulmi ne
ya yanka musu ba za a ci ba.

Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user