Saturday, 11 January 2020

Shin ko Me Ne Ne Dalilin da Yasa Mata basa Son a yi Musu Kishiya?

Tura Wannan Zuwa Ga
Babu ƙarya ko ƙazafi, sannan babu ƙari, akwai mata da suke aikata babban kuskure, wanda zamu iya ambata shi da son zuciya, baza ace Jahilci bane domin da yawansu da ilimin su, ba ilimi bane almuhim gyaran zuciya ne yafi Alkhairi, Ni dako baƙi ban gama iyawa ba idan nafiki wankakkiyar zuciya ke da kika haddace Qur'ani nafi ki hatta a wurin Allah.

Muguwar Zuciyar 'Ya Mace Cikin Zamantakewar Aure...

Marubuci: Fatima Zahra

Wannan duniyar bata da tabbas, karki bari son ZUCIYA yasa ki cutar da abokiyar zamanki, ko 'ya'yanta, duk abin da zuciyar ki ta saƙa maki  me kyau ko mummuna Allah ya sani, kuma ya gani, kuma cikin ikonSa sai ya sakawa wanda aka nufa da wani sharri madamar bashi da Haƙƙi.

Abinda nake so nace shine:

1. Me yasa kike farin ciki idan abokiyar zamanki ta kasa gamsar da mijin ku ta fuskar Aure?

2. Me yasa kike jin daɗi idan mijin ku ya nuna yafi son ki da ƴaƴanki akan ita da ƴaƴanta?

3. Me yasa kike fatan hankalin mijinku ya karkata akanki ke kaɗai?

4. Me yasa kike jin daɗi idan mijin ku yana kyautata miki ita baya mata?

5. Me yasa kike jin daɗi idan yana kyautatawa ƴan uwanki baya kyautatawa nata ko nashi?

Kada Ki Bari Son Zuciya ya ruɗe Ki..

Me yasa?...Me yasa?????

Hmm Amma kin Haddace kasowa Ɗan Uwanka abin da kake sowa kanka?

Matuƙar waɗancan abubuwan dana ambata suna faruwa a cikin gidan ku, baki ji ɗaci aranki ba, kuma baki yi iya iyawarki ba wurin bayar da gudunmuwa to ki sani zuciyar ki bata da kyau! Sam!

Kuma Allah baya farin ciki dake!

Ina ga kuma ta sanadinki hakan ya faru?? Matsalar Hajiya! Idan kin wuce nan Duniya zaki je ki tarar ko kuma tun a duniya ki gani akanki ko akan ƴaƴanki.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA DALILAI 6 DAKE SA MATA KASHE MAZAJEN SU

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Kowanne Miji ya Kula dasu Idan Zai Yi Magana da Matar Sa

KARANTA DALILAN KARIN AUREN MACE SAMA DA DAYA

Muyi haƙuri mu wanke zuciyar mu daga ƙeta da son kawunan mu sai Allah yayi farin ciki damu, sai ya shiga lamuran mu, Allah ya bamu iko Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user