Wednesday, 5 February 2020

Karanta Abinda Yakamata Kowanne Ango da Amarya su Yi a Daran Farko na Amarcin Su

Tura Wannan Zuwa Ga
Da farko idan zaka shiga ɗakin Amaryarka, zaka shiga ne da alwala, sannan zaka nemi ɗan wani abinci mai daraja.

Ladubban Daran Farko Don sababbin Ma'aurata.. 

MarubuciAn-naseer Muhammad

Misali kamar Naman Kaza, ko Tsire, da sauransu.

Idan ka shiga zaka umurceta itama taje tayi alwala.

Sannan kuyi Sallah raka'a biyu. Sannan kuyi ma Allah godiya abisa cika muku burinku da yayi. Kuyi addu'a abisa kanku da dukkan al'ummar da suka amsa gayyatarku suka halarci wajen ɗaurin aurenku.

Daga nan sai ka dafa kanta. Ko goshinta, sannan ka karanta wannan addu'ar kamar haka:

"ALLAHUMMA INNEE AS'ALUKA KHAIRAHA WA KHAIRA MA JABALTAHA 'ALAYYA."

WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIYYA.

(ko kuma MA JUBILAT ALAIHA)"

(Abu dawud ya ruwaito  da Ibnu Maajah da Nisa'I).

MA'ANA:

"YA ALLAH ina roƙonka alkhairin da yake tare da ita, da kuma alkhairin abinda ka ginata akai. Kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da kuma sharrin abinda ta ginu akansa"

Ita wannan sallar Nafilar da akeyi, tazo ne acikin ayyukan Sahabbai.

Kamar irinsu Ibnu Mas'ud (rta).

Daga nan kuma sai kuci wannan abin da ka shigo dashi, ku dan sha wani abu mai zaƙi haka.

Amma ba'a so mutum yaci abu mai nauyi sosai a irin wannan lokacin.

Daga nan kuma sai ku kusanci juna, tare da gabatar da 'yan wasanni da juna kafin kufara gabatar da ibadar Aure.

Kuma akwai addu'ar da ake karantawa dai-dai lokacin da za'a fara jima'I ita ce:

"Allahumma Jannibnash Shaitan Wa jannibiSh-shaytana ma razaqtana"

MA'ANA: "Ya Allah ka nisantar da shaitan daga garemu.

Kuma ka nisantar da shaitan daga abinda zaka azurtamu dashi".

Annabi (saww) yace:

"Idan aka ƙaddara samun ciki awannan saduwar, to shaitan ba zai iya cutar dashi ba har abada"

(Bukhary da Muslim suka ruwaito shi).

Kabi amaryarka ahankali.

Domin kuwa wasu amaren zaka iske sun wuni cikin gajiyar biki, sannan ga kunya ta lulluɓeta saboda tunanin wannan lokaci mai daraja.

Sannan yawancin angwaye suna ƙwallafa ransu akan cewar wai sai sunyi jima'I adaren farko.

Wannan ba dole bane.

Idan kaga alamar ta riga ta gaji, to ka ƙyaleta.

Idan kuma tsoro take ji, (musamman ma idan mai kananan shekaru ce, ko kuma Allah ya tsareta bata taɓa kusantar namiji ba).

Zaka tarar ta gama tsorata, wata ma har tana karkarwa (jikinta yana rawa saboda tsoro).

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA SHAWARA ZUWA GA MA'AURATA DA MASU NIYYAR YIN AURE

Karanta Yadda Zaka Gane Budurwar da Ba ta Taba Saduwa da Namiji ba Kafin Kuyi Aure

KARANTA DALILAN KARIN AUREN MACE SAMA DA DAYA

Don haka ka kwantar mata da hankali ta hanyar kalamai masu daɗi na soyayya, nasiha, da sauransu.

Haka shari'a ta koyar.

Allah ka aurar da matasan mu maza da mata ga Ma'aurata nagari Amin

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user