Fahimta Fuska Ce
Kamar yadda Fahimta ta zama fuska daban-daban haka mutane ma suke mabambanta ne.
Gashi nan dai dukkanin su sunan su mutane amma kuma ana iya samun banbancin fahimta a tsakaninsu, ma'ana yana iya zamowa kowa da yadda ya fahimci abu.
Kamar yadda sugar da gishiri suke dukkaninsu kala ɗaya ne amma kuma ɗanɗanonsu ya banbanta to haka mutane suke.
Wasu daga cikin mutane sukan tsananta su zafafa da tsayuwa akan lallai sai anbi fahimtarsu 100% wanda kuma hakan abu ne mai matuƙar wuya.
A rayuwa duk yadda ka fahimci abu wani kuma bazai taɓa fahimtarsa yadda ka fahimce shi ba, wani lokaci guda zai iya fahimtarka wani kuwa har abada bazai taɓa fahimtarka ba.
Ana samun banbancin fahimta a kowani fuska a Fuskar Addini ko kuma a Fuskar Rayuwa, saboda haka bai dace mutane su ringa zafafawa akan lallai kowa sai ya fahimci inda suka dosa ba, kuma ya kamata a ringa girmama ra'ayin juna ba tare da kushe da musgunawa ba matuƙar dai fuskar da aka fuskanta bai saɓawa karantarwa kitabu was Sunnah ba.
Domin idan kai ka yadda da fahimtarka 100% to wani har'abada ko 1% bazai taɓa fuskantar fahimtarka ba.
Balle ma banbancin fahimta a ɓangaren addini a bisa irin tafiyar da ake yi a yanzu da zarar an samu banbancin fahimta sai a hau kafirta juna, wannan ba adalci bane domin ko wani ɓangare yana jin cewa fahimtarsa ita take akan dai-dai 100%, to yadda kake ji shima wancan haka yake ji.
Abunda yafi dacewa dai ko wace fahimta a jajirce wajen fuskantar kitabu was Sunnah domin shine Fuska mafi gaskiyar zance.
ALLAH Ta'ala Yayi mana muwafaƙa da dai-dai Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.