Friday, 14 February 2020

Bayyanar Bidiyon Tsiraicin Maryam Booth da Wani Sanata Gaskiya ta Fara Bayyana daga Bakin Mahukunta Kannywood

Tura Wannan Zuwa Ga
Mujallar film magazine ta ruwaito cewa "Shuwagabannin masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) suna taimakawa Jami'an Tsaro domin kama wasu mutum biyu da ake zargi da ɗaukar wani hoton bidiyo na fitacciyar jaruma Maryam Booth tsirara tare da yaɗa Shi a soshiyal midiya."


Jaruma Maryam Booth

Marubuci: Harunasp Hamisu Dansadau

Tun daga shekaran jiya ne guntun bidiyon ya ɓulla yafara yawo gadan-gadan a gari,.

An faɗawa Mujallar Fim Cewa "Yau shekara uku kenan da ɗaukar bidiyon".

A bidiyon mai tsawon daƙiƙa biyu kacal, anga kyakkyawar jarumar ta Kannywood tsirara a cikin ɗaki kamar ta fito daga wanka babu komai a jikinta sai Ɗankwali a kanta.

Akwai tabbacin cewa "Wanda yayi bidiyon ya ɗauke tane da gangan, batare da amincewar taba". Domin kuwa data ankara ana ɗaukar ta sai tayi wuf ta ƙwace wayar da ake ɗaukarta da Ita.

Mujallar Fim tayi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar, amma sai akaji Wayarta a kashe.

Sai dai shugaban ƙungiyar Jaruman Kannywood ta jihar Kano Alhaji Alhassan Kwalle, ya tabbatarwa Da Mujallar Fim Cewa "Ƙungiyarsa ta shiga cikin al'amarin, tana taimakawa wajen ƙoƙarin kamo wasu mutum biyu, Namiji da Mace waɗanda aka tabbatar da cewa sune suka saki bidiyon a gari bayan sun jima suna cutar Maryam Booth tare da yi mata barazana.

Amma abinda bincike ya nuna da kuma labarin da aka samu shine "Wannan abin yafaru ne kusan shekaru uku da suka Wuce."

Kuma yaran da sukayi abin sun tayi mata barazana dashi, kan ta basu kuɗi, Idan bahaka ba zasu saki bidiyon ɗin, kuma akan haka sun karɓi kuɗi masu yawan gaske a wajenta don gudun kada abin ya bayyana.

To a ranar larabar da ta gabata ne ɗaya daga cikin su yace tabashi kuɗi zai kai mahaifiyarsa asibiti, ita kuma tace batada kuɗi kuma ta gaji da basu kuɗin, don haka ganin basu samu kuɗin ba suka saki bidiyon ɗin, kuma akwai shaida ta banki yadda ta rinƙa tura masu duk abinda suka nema a wajenta, don haka ana nan yanzu ana bin hanyar da za'a kama su.

Shi kuwa sakataren Ƙungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa Ta Ƙasa (MOPPAN), reshen jihar Kano, Malam Salisu Muhammad Officer, da Mujallar Fim tayi masa tambaya dangane da lamarin, sai yace "Mun san da maganar, amma mu a matsayin mu na shuwagabannin harkar fim babu wani abu da zamu ce...kawai abu ne da ya shafeta ba harkar fim ba."

Wata ƙawar Maryam Booth data faɗawa Mujallar Fim Cewa "Al'amarin ya girgiza jarumar matuka, har tayi ta kuka domin baƙin ciki akan wannan cin amana da akayi mata."

Bugu da ƙari wakilin jaridar Tsakar Gida ya tabbatar da cewa "Mafi Yawancin 'Yan Fim da suka ji labarin ɓullawar bidiyon mai matsakaicin zango, sun tausayawa Maryam Booth, suna faɗin cewa, ba laifinta bane, kuma ba sabon abu bane yarinya tafito daga wanka a banɗaki tsirara a gaban ƙawarta musamman a cikin ɗaki.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Jaruma Fati Washa ta Tayar da Kura a Shafukan Sada Zumunta Bayan Fitar Wasu Zafafan Hotunan Ta

Shin dagaske ne Zainab Indomie tayi Film din Batsa na Blue Films???

Ku Kalli Sabon Iskancin Video da Hotunan Rahama Sadau A Film Din Kudanci na Nollywood

Ku  Ci gaba da kasancewa tare da shafin MURYAR HAUSA24 domin samun Cikakken Tarihin Maryam Booth.

Allah ya kyauta gaba yakuma tsaremu daga sharrin shaiɗan da kuma sharrin abokan zama waɗanda suke kusa dakai zaune ba saboda Allah ba, sai don suyi maka sharri ko su aibantaka a idon duniya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user