Sunday, 8 March 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (17) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
KORON BAKI

Babu wanda ba ya son alkhairi, wani sa'in ko biredi ka je saya sai ka yi sha'awar da ma a ce kamfanin naka ne, akwai lokacin da na je asibiti na ga yadda likitoci suke aiki sai da na yi sha'awar a ce ina cikinsu, duk wani abin sha'awa da mutum ya gani sai ya ƙaunaci a ce nasa ne, koda kuwa mace ce ta sha kwalliya ta yi irin adon da kake so sai ka ji a jikinka cewa kana so, shi ya sa ma addini ya yi sauri ya kulle wannan babin, wata za ka ga ta sha dogon hijabi da safa a ƙafa da hannu, ga niƙabi ga kamfacecen gilashi, ba za ka taɓa sanin cewa fara ce ko baƙa ba bare ka haɗe yawu.

Karka Fidda Tsammanin Yin Nasara..

MarubuciBaban Manar Alkasim

To irin wancan sha'awar da muke faɗi matuƙar kana da damar mallakarta yadda za ta koma taka mai zai hana ka fara ƙoƙari? Na sani akwai zarafin da mutum zai fara makarantar muslunci bai haɗa da boko ba ko kaɗan ya tafi har jami'a ya tara yara, ga shekaru sun ja sannan ya fara sha'awar zama likita, wanda a tsari sai ya kawo takardar sakandare shi kuma bai san kan lissafi ba, da kamar wuya ya iya cimma burinsa, amma wanda zai iya ɗin wani motsi ya fara? Bai yuwa ga wanda yake son zama likita sai ya fara sanya fararen kaya ya sayi kayan aiki ya shiga asibiti ya ce shi fa yau ya zama likita, ko mai kaciyar yara akwai buƙatar gwanancewa da farko.

Tunda kana da manufa kar ka yarda tsoro ko kasala da ragwanci su hana ka yin gaba, ko wani walkataccen tunani ko mummunan zato ya sa ka fara ɗari-ɗari da abinda kake buƙata, na koyar da wata ɗaliba shekaru da ɗan dama a wani kwaleji, tana da ƙoƙari sosai amma ba turanci, ta gama diploma amma sakamakonta na Education da harshen turancin ya ɓaci sosai, ta karbi shahadarta jiki ba ƙarfi, amma abin mamaki sai ta koma sakandare jss3, har ta zana WAEC, kafin shekara ta huɗu sai ga ta ta zo ofishina ina ta ƙoƙarin tuno sunanta da yake mace ce mai son raha kusan kowa ya san ta.

Ban iya tuno sunanta ba, daga bisani ta gaya min sannan amma ta ƙi magana da ni da Hausa sai da Turanci, nan na sake rikicewa kamar dai ba ita ce wace na sani ba, mace ce matar aure surarta ta ƙara canjawa ta ɗan ƙara ƙiba ga alamun girma, sai na ce ina ganin ba ke ce wace na sani ba wace nake magana kaza-kaza ta ce wallahi ita ce, zan yi mamaki sai ta gaya min tarihin karatunta da abinda ya koma da ita baya, ta ce yanzu ba ma Larabcin ne a gabanta ba kimiyya za ta karanta, likita take so ta zama, na tabbatar za ta iya, wace ta gama diploma amma ta koma sakandare aji uku don cimma wani buri na tabbatar ba abinda ba za ta iya jure masa ba.

Wani kuma za ka iske ba tsoron ne ko ragwanci ba bai son ya kasa cimma burinsa ne, a hakan zai rasa abinda yake so, kamar mai koyon harshe, bai son in ya yi magana a yi masa dariyar abinda ya faɗa, sai ya gummace ya yi shuru, wani jarumin zai yi ta yi ana masa dariya, cikin ɗan ƙaramin lokaci sai ka ga ya iya, akwai wani da na san yana (ta gayu) bala'in son wata yarinya amma ya kasa gaya mata, ita kuma tana ganin kamar irin mutuncinnan ne da suke faɗi, 'yan alamun da yake nuna mata ya sa ta ƙi karɓar wani tana jiran ko zai furta, har dai abu ya yi tsawo ta tabbatar ba da gaske yake yi ba ta ba wani dama, har dai aka ba wancan.

Saura 'yan kwanaki ƙalilan a ɗaura auren ya fito yana zagaye-zagaye yana gaya mata cewar ya fi shekara biyu yana son ta, suka yi 'yan koke-koken da za su yi suka haƙura, ta je ta yi aurenta a wani wuri, abu ɗaya ya wargaza masa shiri, nauyin baki, da a ce ya fito ya faɗi da ƙila ya dasa wata bishiyar soyayya a zuciyarta da za ta riƙa girma a hankali, shi ya kasa yi mata magana ne tsoron kar ta ce ba ta son sa, wannan tsoron da yake ji shi ya ja masa yin asarar komai, in dai kana son cin nasara ɗayan abu biyu ne, ko ka samu ko ka rasa, in ka samu madalla, in ka rasa ka yi karatun da zai ba ka damar kiyaye gaba.

Na sha jin mutane na cewa "Da ka yi min magana wallahi da na bar maka, jiya-jiyannan na yi kyauta da shi" wani ya ce "Kash! Me ya sa ba ka gaya min ba? Ai wallahi ban san kana so ba!" Abubuwa da dama waɗanda za su nuna cewa tun farko nauyin da mutum yake yi wajen fuskantar abinda zai kai shi ga cika burinsa shi ke hana shi cin nasara, da farko tsoron me za ka ji in ka ce wa mace kana son ta ta ce ba ta son ka? Mace ma da shekara sama da dubu ɗaya lokacin kunya na budurwa ta sami Annabi (S.A.W) a cikin jama'a ta ce masa ta ba shi kanta ya aura, burinta bai cika ba don Annabi (S.A.W) bai nuna yana buƙata ba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta riƙe wuta sosai sai da ta cimma burinta, rana guda aka ce ta wuce gidan ma'aiki an ɗaura aurenta da shi.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (15) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (16) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (18) Cikin Sauki

Khadija (R.A) ta fito babban gida ne, kuma babbar mace ce, Allah (S.W.T) ya hore mata abin hannunta, ta sami manyan mutane da suka fito suna ƙaunarta amma ta ƙi, sai ga shi ta yi sha'awar auren Annabi (SAW) duk da cewa yaron gidanta ne a lokacin, ta manta da girman hali da na shekara, ta manta da cewa ita mai hali ce tsakanin manyan mutane, ba ta jira sai an zo nemanta kasancewarta mace wace za a aura ba, tana da manufa kuma tana son cika burinta, cikin ikon Allah 'ya'yan Annabi (S.A.W) 7 ne ita ce uwar 6, wannan abinda ya shafi zamanta kewa kenan, hatta a al'amuran saye da sayarwa sau tari sai ka sayar da kaya za ka ji wani ya ce ya daɗe yana son ya yi maka magana amma bai sani ba ko ba za ka sayar ba, ko sai ka yi wa wasu hanyar ɗaukar aiki a ƙarshe ka ji wani ya ce yana so amma ya kasa yi maka magana ne.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: