Idan Ba'a Son Ka Ka Haƙura Kawai..
Ba fa a soyayya dole, mace in ta so mutum ba ta damu ba, za ta iya yi masa komai, da daɗi ko da wuya, don ta bautu, ko ta zauna cikin talauci ba damuwa matuƙar ta ƙaunace ka.
In kuwa ta so wani, kai kuma ka aure ta a dole, ko da shekara nawa ne, ta dunga maganarsa kenan da kewarsa a kowani lokaci.
'Yan wasu hidundumu da ya kamata ta yi maka ba ka taɓa ganin ko ƙwara ɗaya, i mana ai ba son ka take ba.
Shi dai an zuga shi wai kunya ce ai za ta bari, wasu kuma suka ce, na ɗan lokaci ne bar ta kawai.
Shi ma Allah ya so shi ya ga uwar bari, na tabbata da ya aure ta a haka da ya gane kurensa, mace fa in ka ce kana son ta aka yi dace da ba ta son ka ka shiga uku.
Duk wani baƙin jinin duniya za ta kwaso ta watsa maka, in ba cewa ka yi ka ƙi jininta ba to ba za ka zauna lafiya ba, ka ji wani ikon Allah.
A taƙaice in mace ta ce ba ta son ka ka haƙura kawai, yanzu ake haihuwar kyawawa, ga su nan kamar riguna, in wannan ba ta yi maka ba, ka ɗauki wancan ka sanya.
Wanda ya kuskura ya ɗauki wace ta yi masa yawa a riƙa ganinsa tsirara, wanda ya ɗauki wace ta yi masa kaɗan kuma ta yage ta bar shi haka, auri wace ta dace da kai kawai, soyayya ko sunanta ba ta yi kama da ƙiyayya ba.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.