Sharrin Sha'awa..
Al-imam Abu-bakr Abdullahi Bn Abiy Shaibah (Rahimahullah) Yace: “Al-amarin sha'awah lamari ne mai hatsari sharrinta mai girma ne, sau da yawa mai bautar ALLAH (SWT) ta maida shi fasiƙi, sau da yawa ta fitar da wasu mutane daga addini waɗanda suka kasance a zahiri ga wanda ya san su sune mafi nesa daga ɓata da karkacewa daga cikin mutane.” [Musnaf Ibn Abiy Shaibah 4/46]
Sharrin Sha'awah bata bar mai bautar ALLAH ba face sai wanda ALLAH ya tsiratar, balle kuma wanda bai damu da bautar Ubangiji ba.
Wajibi ne ga dukkan mutane musamman Matasa suyi ƙoƙarin jajircewa wajen yaƙi da Sha'awah wanda ako yaushe mutanen banza ke ƙoƙarin tallatawa al'ummah ita a kafafen sadarwa da tashoshin telebijin ta hanyar kawo fina-finan batsa da yaɗa maganganun batsa domin neman abokan kasancewa a wutar jahannama.
Yana da kyau al'ummah suyi ƙoƙarin kiyaye waɗannan abubuwan :
1. Yawan istighfari dare da rana.
2. Sallah akan lokaci.
3. Abokai nagari
4. Yawan tilawar alkur'ani.
5. Tuna mutuwa a kowace rana musamman idan kina/kana kallon batsa kada ya zama aikin ka/ki na ƙarshe a duniya.
6. Ka/Ki sani mai aikata laifi da gan-ganci baya samun yardar ALLAH har a karɓi adduo'in sa.
7. Kallon batsa na jawo zubewar mutunci da rashin kwarjini har kowa ya raina ka a tsane ka a cikin al'umma.
8. Kallon batsa laifin sa kamar zina ne, ai yafi muni ma idan sha'awa tana motsawa yayin kallon.
9. Yayin kallon batsa ana kallon tsiraicin wani ko aji maganar batsa duk haramun ne.
10. Kallon batsa yana jawo sauƙin ayi fasiƙanci da mace don kullum a matse take a aikata abunda take gani da ita.
11. Ana samun cutar tsiro a mahaifa in mace na taso da sha'awa bata samun biyan buƙata, har yakan kawo rashin haihuwa ko cutar daji a mahaifa.
12. Keɓewa a ɓuya ana kallon batsa na haifar da munafurcin zuciya. Kuma mace ba zata samu miji ba sai mai hali irin na ta haka namiji ma bazai auri mace ba sai mai hali irin nasa.
ALLAH Ya tsare mana imanin mu ya kuma kiyaye mu da dukkan al'ummar musulmai Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
0 comments:
Post a Comment