Friday, 13 March 2020

Shin Ko Kasan Irin Halin da Azzalumai Suke Kasancewa?

Tura Wannan Zuwa Ga
MENE NE ZALUNCI?

Hali ne daga cikin munanan halayen da addini ya ƙyamata, duk wanda ya samu kansa da irin wannan hali haƙiƙa ya haɗu da halayyar da zai kasance dashi wajen ɗebe albarkar rayuwarsa kuma ya dasa masa ƙunci da baƙin ciki, ƙarshe kuma ALLAH yayi masa sakayya da sakamakon abunda ya aikata.

Zalunci Mugun Ciwo

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

KARKASUWAR ZALUNCI

Zalunci kuma ya kasu kashi uku kamar haka:

1. Zalunci tsakanin mutum da ALLAH wanda mafi girman shi shine shirka.

2. Zalunci tsakanin mutum da sauran Halittu sawa'un dabbobi ne ko mutane ta hanyar shiga haƙƙin wani da zalunci ko ta hanyar magana ko aiki.

3. Zalunci tsakanin mutum da kansa ta hanyar aikata wani laifi ko hana kansa wani alheri ta hanyar aikata zunubi.

AYOYI GAME DA ZALUNCI

Ayoyi da hadisai da dama sunyi hani akan wannan hali na zalunci kuma sun tsawatar akan azzalumai daga ciki:

ALLAH (SWT) Yana cewa: “Kuma kada kayi zaton ALLAH mai shagala ne daga abunda azzalumai suke aikatawa, abun sani kawai yana jinƙirta musu ne zuwa ga wani wuni, Wanda idanuwa suke fita turu-turu acikinsa.” [Suratul Ibrahim aya ta 42]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Haƙiƙa ALLAH Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi bazai kuɓuce masa ba.” [Bukhari da Muslim]

Kuma haƙiƙa ALLAH (SWT) Ya La'anci Azzalumai kamar yadda Yazo acikin AL-KUR'ANI MAI GIRMA: “Sai mai sanarwa ya yi yekuwa, cewa: La'anar ALLAH ta tabbata a kan Azzalumai.” [Suratul a'araf aya ta 44]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Kuji tsoron Zalunci domin shi zalunci duhu ne ranar alƙiyama.....” [Muslim Ya ruwaito shi]

Kuma acikin AL-KUR'ANI MAI GIRMA ALLAH (SWT) Yana cewa: “Waɗanda suka yi zalunci da sannu zasu sani wace makoma ce makomar su.” [Suratul Shu'araa aya ta 227]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Kaji tsoron addu'ar abun zalunta, domin ita bata da tsari tsakaninta da ALLAH.” [Bukhari da Muslim].

ABINDA ZAI BIYO BAYAN ZALUNCI

Lallai lokuta da yawa mutum yakan yi yadda yake so ta hanyar zalunci, ya zalunci wanda yaga dama. Sai dai addu'a ɗaya tak ta Wanda aka zalunta ta isa tasa ka rasa komai daka mallaka, domin addu'ar wanda aka zalunta karɓaɓɓiya ce anan (Duniya) ko a can (Lahira).

Wani mai waƙa yake cewa:

لا تظلمن إذا ما كنت مقتدرا , فاظلم آخره يأتيك بالندم

نامت عيونك والمظلوم منتبه , يدعو عليك وعين الله لم تنم.

Ma'ana: " Kada kayi zalinci in ka kasance kana da iko, domin zalunci ƙarshensa nadama zai kawoma.

Idon ka yayi bacci shi kuma wanda ka zalunta yana ankare , yana ma addu'a Idon ALLAH baiyi bacci ba."

KO ZAN IYA TAIMAKAWA AZZALUMI?

Addinin musulunci mai taushi da tausasawa sai mafificin Halitta masoyin mu Annabi Muhammad (ﷺ) Yace: “Ka taimakawa Wanda za'a zalunta koda shi Azzalumi ne. Sai akace masa ta yaya za'a taimaki Azzalumi ??? Sai Yace: "A hana shi yin zalunci wannan shine taimakonsa.” [Sahihu Jamee 2051]

Ya ALLAH kada ka sanya mu cikin Azzalumai, Azzaluman cikin mu Ya ALLAH ka shiryesu su daina, Ya ALLAH ka gafarta mana baki ɗaya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: