An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, suna na Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal.
Marubuci: Mu'awuya Zakariah Adam Gombe
Muryar Hausa24: Tarihin Rayuwar ka?
Mahaifina Shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-
Neman-Suna Fagge.
Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da
tsohuwar tashar kuka.
Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai.
Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-
Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32
unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala.
Muryar Hausa24: ɓangaren karatun ka?
Na fara karatun Al-Kur’ani mai girma tun ina dan
karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15.
Bayan firamare da sakandare, da
na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan
mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi
da fannoninsa daban-daban.
Muryar Hausa24: Malaman da kayi karatu a wajen su?
Wadannan manyan malamai su ne:
1. Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
2. Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
3. Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
4. Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
5. Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
6. Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
7. Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a
wajensa.
8. Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
9. Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
10. Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
11. Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a
wajensa.
Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji
qansa da rahama!
12. Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa. Wannan malami, a
wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai
haquri da juriyar karantarwa.
13. Dr. Kabiru M. K. Yunus BUK, wanda na yi nahwu da lugga a wajensa.
14. Dr. Aminuddeen Abubakar, shugaban Da’awah, wanda na yi tauhidi da hadith a wajensa.
15. Dr. Ahmad Bamba BUK, wanda na yi hadith a wajensa. Wannan malami uba ne, kuma mai ba da
shawara.
16. Dr. Abubakar Jibirin, wanda na yi Kitabut Tauhid a wajensa.
17. Sheikh Abdulwahab Abdallah, wanda na yi Musdalahul Hadith, da Qadarunnadah (nahawu), da
Subulussalam (hadith) a wajensa.
Wannan malami uba ne, kuma mai ba da shawara.
Wadannan su ne malaman da na kwashe mafi yawan shekaruna ina zirga-zirga a tsakaninsu, wajen
neman ilimi.
Muryar Hausa24 : Ko Malam yayi Karatun Littattafai?
Akwai wasu malaman da suka yi mini tasiri a rayuwa, amma ta hanyar karanta
littattafansu da sauraren kaset-kaset dinsu:
1. Sheikh Muhammad bin Saleh Usaimin. Wannan malami ne, na kwashe tsawon shekara goma ina bin
littattafansa da kaset-kaset dinsa na audio da bidiyo. Na tasirantu da shi kwarai da gaske.
2. Almuhaddith Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani. Wannan malami, duk littattafansa da suka
fito kasuwa, da kaset-kaset, ina bibiyar su, saboda fa’idoji masu yawa.
3. Sheikh Bakar Abu Zaid. Saboda kwarewarsa a wajen sarrafa littattafai.
Sauran su ne, Sheikhul Islam Ibni Taimiyya, da Sheikh Ibnul Qayyim, da Sheikhul Islam Azzahabiyy,
da Sheikhul Islam Ibni Kathir, da Sheikhul Islam Ibni Hajar Al-Asqalani.
Muryar Hausa24: Game da aƙidar malam?
Aqidata ita ce aqidar ahlussunnah wal jama’a. Ma’ana, imani da Alqur’ani da hadisan Manzon
Allah (SAW) a kan fahimtar magabata na kwarai.
Muryar Hausa24: Game da Wa'azi?
Tsarin wa’azi: Tsakatsaki.
Muryar Hausa24: ko Malam yayi Karatun Zamani?
Na ci gaba da karatu na zamani a Jami'ar Bayero, a bangaren jarida, Mass Comm. Wasu dalilai suka
tsayar da ni.
Na yi diploma a computer data processing.
Iyali: A yanzu ina da mata biyu, da kuma ‘ya’ya tara.
Muryar Hausa24: ko Malam yayi tafiye-tafiye domin gabatar da Wa'azi?
Daga cikin kasashen da na je domin wa’azantarwa, akwai Nijar, Togo, Ghana, Cote d’Voire. A
jihohin Najeriya kuwa, babu jihar da ban je ba domin gabatar da wa’azi ko karantarwa.
Wannan shine a taƙaice tarihin Malam Aminu Ibahim Daurawa.
Ku ci gaba da Kasancewa da shafin Muryarhausa24.com.ng domin samun Tarihi Daban-Daban mungode da ziyartar wannan Shafi mai Albarka.
Takaitaccen Tarihin Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria : Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Marigayi Sheikh Albani Zaria - Hotuna da Cikakken Tarihi
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com
Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng
Biography Of Mal. Aminu Ibrahim Daurawa by MuryarHausa24.com.ng

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Lokacin da yake ƙarɓar Lambar Girmamawa Daga Wakilan Ƙasar Sudan Saboda Namijin Koƙarin da Yake Wajen Yaɗa Ilimi da Tarbiya
Muryar Hausa24: Malaman da kayi karatu a wajen su?
Wadannan manyan malamai su ne:
1. Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
2. Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
3. Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
4. Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
5. Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
6. Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
7. Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a
wajensa.
8. Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
9. Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
10. Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
11. Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a
wajensa.
Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji
qansa da rahama!
12. Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa. Wannan malami, a
wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai
haquri da juriyar karantarwa.
13. Dr. Kabiru M. K. Yunus BUK, wanda na yi nahwu da lugga a wajensa.
14. Dr. Aminuddeen Abubakar, shugaban Da’awah, wanda na yi tauhidi da hadith a wajensa.
15. Dr. Ahmad Bamba BUK, wanda na yi hadith a wajensa. Wannan malami uba ne, kuma mai ba da
shawara.
16. Dr. Abubakar Jibirin, wanda na yi Kitabut Tauhid a wajensa.
17. Sheikh Abdulwahab Abdallah, wanda na yi Musdalahul Hadith, da Qadarunnadah (nahawu), da
Subulussalam (hadith) a wajensa.
Wannan malami uba ne, kuma mai ba da shawara.
Wadannan su ne malaman da na kwashe mafi yawan shekaruna ina zirga-zirga a tsakaninsu, wajen
neman ilimi.
Mal. Aminu Daurawa tare da Ma'aikatan Hisba ta Jihar Kano
Muryar Hausa24 : Ko Malam yayi Karatun Littattafai?
Akwai wasu malaman da suka yi mini tasiri a rayuwa, amma ta hanyar karanta
littattafansu da sauraren kaset-kaset dinsu:
1. Sheikh Muhammad bin Saleh Usaimin. Wannan malami ne, na kwashe tsawon shekara goma ina bin
littattafansa da kaset-kaset dinsa na audio da bidiyo. Na tasirantu da shi kwarai da gaske.
2. Almuhaddith Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani. Wannan malami, duk littattafansa da suka
fito kasuwa, da kaset-kaset, ina bibiyar su, saboda fa’idoji masu yawa.
3. Sheikh Bakar Abu Zaid. Saboda kwarewarsa a wajen sarrafa littattafai.
Sauran su ne, Sheikhul Islam Ibni Taimiyya, da Sheikh Ibnul Qayyim, da Sheikhul Islam Azzahabiyy,
da Sheikhul Islam Ibni Kathir, da Sheikhul Islam Ibni Hajar Al-Asqalani.
Mal. Aminu Daurawa a cikin Mota