MUGUJI YIN AUREN SHA'AWA..
Mu dai kawai muntashi muntaras da iyayen mu sunyi aure, yayun mu sunyi aure , abokan mu suma sunata aure, don haka muma yakamata muyi auren nan kar abarmu a baya. Haka zakaji matasa sunata faɗi, saboda an ɗauki aure kamar wani al'adace ta mutane kuma abin a more aji daɗi.
Hakan yasa dayawan mutane wanda sukayi aure batareda ilimin yadda zasu tsarkake niyyan su gameda aure ba; wanda hakan yasa bayan sunyi auren sai suka tarar da rayuwan babu daɗin da suke tsammani, sai kaga suna cewa ai aure zaman haƙuri ne kawai acikin sa, babu shakka aure zaman haƙuri ne ko ka faɗa ko baka faɗa ba wannan sananne ne a gun wanda yasan hikimar aure a addinan ce.Yanzu halin da ake ciki matasa munkoma auren 'yan mata ne saboda kyawun surar su, ko kuma kyawun dirin da Allah yayi musu, wanda hakan yana ɗaya daga cikin auren sha'awa kamar yadda malamai sukayi bayani.
Matasa na auren mace ne (representable) irin wanda idan suka nunata a dangi za'ace dasu kai gaskiya matar wane ta haɗu, ai wane ya iya zaɓe da sauran su. Saboda yabi kyawun surar jikinta ko fuskarta wanda wannan abune mai gushewa cikin ƙanƙanin lokaci.
Dayawan maza idan suka auri mace don kyawun dirin ta, ko kyawun fuskarta zaka taras bayan anyi auren zai dawo daga baya zaizo baya ganin wannan kyawun nata sosai, saboda yau da gobe kullum yana ganin fuskar harma zaizo yazamana kyawun baya masa tasiri, sannan maza mun kasance muna fita waje dole zakaga wanda tafi matarka kyawun diri ko fuska. Idan dama abinda yake birgeka kenan to sai kaga fa kai yanzu ita wannan na wajen itace tafi birgeka saboda tafi taka ta gida, sai kaga mutum yafara nemen mata, shiyasa wannan yana ɗaya daga cikin manyan dalilin dasuke sa maza su riƙa canzawa matan su bayan anyi aure.
Zakaga namiji rimi-rimi a waje kafin aure saikaga yana lallamin ta kamar me, amma daga zaran ta shigo cikin gidan sa zai fara canza mata ahankali-ahankali, saboda yasami abinda yake buƙata, don haka ko ayanzu kasuwa ta watse ɗan koli yaci riba, sai kaga yana ƙuntata mata iri-iri na yau da ban na gobe daban, Meyasa? Saboda ba don Allah ya aure ta ba, yabi zaɓin san ransa ne, amma bai ɗauki auren a matsayin ibadah ba. Duk wanda ya ɗauki aure a matsayin ibadah kamar yadda ya ɗauki sallah da azumi ibadah to babu shakka zakaga ya kyautata niyyar sa sannan zaka taras dashi yana ƙoƙarin kyautata wa matarsa.
Amma duk wanda yayi aure don sha'awa saboda aji daɗi ahuta, to babu shakka zaka taras dashi daga baya zaizo yana wulaƙanta matar sa saboda buƙatar sa tabiya, yanzu kuma tazama masa kamar nauyi (responsibility) ne, sai kaga yana canza mata halayen sa kamar yadda hawainiya take canza kalar fatar jikinta idan taso akuma lokacin da taso. Allah (Ta'ala) shine mafi sani.
Ya Allah ka tsaremu da auren sha'awa bisa jahiltan hikimar aure a muslunci, ya Allah ka gyara mana zukatan mu kabamu ikon kyautata niyyan mu Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.