Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Nan da nan ya sa aka tara masa duka hakimai da wazirai da fadawansa, ya karanta musu saƙon Sarkin Muminai, ya kuma nemi shawarar yadda za su ɓullowa wannan buƙata ta Halifa. Hakimai suka ce, "Allah ya ƙarawa Shugaban Muminai tsawon rai. Allah ya ba ka nasara, babu wanda ya cancanci ya jagorance ku a wannan tafiya kamar Sheikh Abdussamadu ɗan Abdulkuddusu Assamudi. Domin kuwa mutum ne mai tsananin ilmi, shahararre ne wurin tafiye-tafiye a kan tudu da teku. Ya sha gwagwarmayar rayuwa iri-iri, ya goge a kan sha'anin bokanci da aljanu, karewa da karau ma ana jita-jitar cewa babu ƙasar da bai sani ba duk faɗin duniyar nan, da mutanen da ke cikinta da al'adunsu. Ka aika masa babu shakka zai taimake ka a cikin wannan sha'ani."
Nan take kuwa Musa ya sa aka kira masa Sheik Abdussamadu, da ya zo ya yi gaisuwa ga Musa. Shi kuwa mutum ne tsoho, shekaru sun yawaita a kansa. Bayan sun gaisa sai Musa ya ce masa, "Ya Sheikh Abdussamadu, ka sani cewa Shugabana Halifa Abdulmalik ɗan Marwanu ya umurce ni da samo masa wani abu a cikin wata ƙasa, ni kuwa ba ni da ilmin wannan ƙasa, ban ma san wajen da ƙasar take ba. Ko za ka taimake ni in tafi tare da kai zuwa wannan ƙasa domin biyan buƙatar Shugaban Muminai? Na tabbata wahalarka ba za ta tafi a banza ba." Sarki Musa ya kwashe saƙon Halifa ya gaya wa Sheik Abdussamad.
Lokacin da Abdussamadu ya ji abin da Musa ɗan Nusairi ya nema gunsa sai ya duƙar da kai ya ce, "Na ji na amince. Na yarda zan taimake ka bisa ga biyan buƙatar Shugaban Muminai, Allah ya ƙara masa tsawon rai." Abdussamadu ya ci gaba da cewa, "Wannan ƙasa da kake magana ƙasa ce mai wuyar sha'ani. Akwai nisa sosai tsakaninmu da ita, sa'annan hanyar zuwa ƙasar cike take da haɗarurruka iri daban-daban."
"Menene nisan ƙasar?"
"Tafiyar shekara biyu ce da 'yan watanni," in ji Abdussamadu, "sa'annan za a haɗu da haɗari iri-iri bisa hanya, da abubuwan ban mamaki masu yawan gaske." Musa ya yi shiru yana sauraren Abdussamadu.
Abdussamadu ya ci gaba da cewa, "Bai kamata ka tafi ba har sai ka naɗa wani Wakili wanda zai ci gaba da lura da sha'anin mulki da kuma askarawa, ka san ƙasarmu tana tsakiyar magabta. Idan ka tafi babu wani Wakili mai kula da askarawa, Nasara na iya abka wa ƙasarmu da yaƙi. Ina ba ka shawara ka naɗa ɗanka a matsayin Wakili."
Musa ya amince da shawarar Abdussamadu, ya naɗa ɗansa mai suna Haruna a matsayin Wakili. Ya umurci hakimai da wazirai da askarawa su yi masa mubayi'a tare da rantsuwar ba za su yi masa bore ba. Suka yi rantsuwar bin sa da gaskiya. Haruna ɗan Musa saurayi ne wanda Allah ya yi wa wata irin zuciya sai ka ce dutse, bai san wani abu wai shi tsoro ba. Sadauki ne na gaske wanda shi kaɗai sai ya mai da runduna guda baya.
Bayan an gama yi wa Haruna mubayi'a sai Abdussamadu ya gaya masa nufinsu na tafiya, amma sai ya ce masa wata huɗu kawai za su yi su dawo. Ya kuma ce masa ba wata tafiya ba ce mai hatsari saboda duk bayan tafiyar wata ɗaya za su isa ga wani zango da aka tanadar musu abinci da ruwa domin hutawa. Abdussamadu dai ya nuna wa Haruna cewa tafiyar da za su yi ba wata mai hatsari ba ce, don dai ya kwantar masa da hankali. Amma yayin da Abdussamadu ya keɓe da Musa sai ya ce ya tanadar musu raƙuma dubu a lafta musu kayan abinci da gorunan ruwa. Musa ya riƙe baki ya ce, "Duk me za mu yi da waɗannan irin kaya niki-niki haka?"
Abdussamadu ya ce, "Ka sani cewa bisa hanyarmu za mu ratsa wata hamada mai zafi wadda ake kira Hamadar Sayarina. Tafiyar kwana huɗu za mu yi a cikinta, hamada ce wadda ba za ka sami ɗigon ruwa guda ba, babu wani abu mai rai dake cikinta, dabba ko ciyawa, saboda zafinta da bushewarta. Haka kuma akwai wata iska mai zafi da take kaɗawa a cikin hamadar, ana kiran irin wannan iska Aljuwaibu. Iska ce mai busar da duk wani abu da ke da damshi, idan aka zuba ruwa a jakar fata aka ratsa ta cikin wannan hamada da shi sai ya kafe don zafin wannan iska, dole sai dai a zuba shi cikin goruna."
Musa ya yi kasake yana sauraren jawabin Sheik Abdussamadu cike da mamaki. Da ya ji ya yi shiru sai ya tambaye shi, "Shin akwai wani Sarki kuwa da ya taɓa shiga wannan ƙasa da za mu tafi yanzu?"
Abdussamadu ya amsa, "I, Sarki Dariyusa na Askandariya da ke cikin kasashen Girka ya taɓa cin ƙasar da yaƙi har ya kafa mulkinsa a wurin."
Daga nan sai Musa ya shiga haramar tafiya, ya sa aka shirya masa raƙuma dubu, kamar yadda Abdussamadu ya buƙata, aka lafta musu abinci da gorunan ruwa. Ya zaɓi askrawa dubu biyu waɗanda za su yi musu rakiya, kowane cikin shirin yaƙi, tare da wazirinsa ɗaya, watau Dalibu ɗan Sahalu. Aka shirya wa Musa da Abdussamadu darbuka ɗaya wadda za su shiga, aka ɗaura ta ga wasu ingarmu biyu. Waziri da sauran askarawa kuwa suka hau dawaki. Suka yi ban kwana da 'yan uwa da abokai suka shiga daji suka fara tafiya. Suka yi ta wuce birane da garuruwa da ƙauyuka har suka shiga cikin surkuƙin dajin da babu komai sai itatuwa da dabbobi, daga nan kuma suka shiga rairayin hamada, bayan sun fita daga cikinta suka shiga wata ƙasar mai yawan duwatsu da tsaunuka dogaye. Sun haɗu da haɗari iri-iri wanda baki ba zai iya bayyanawa ba. Ba su gushe ba suna tafiya tsawon shekara guda.
Ran nan bayan sun kwana suna tafiya, can da gari ya waye sai suka iso ga wani wuri wanda Abdussamadu bai sani ba. Da ganin wannan wuri sai ya buga salati, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki."
"Me ya faru ya Sheikh?" Musa ya tambaya.
"Na rantse da Ubangijin Ka'aba mun ɓace hanya."
"Yaya aka yi haka ta faru kuwa, ya Sheikh?"
"Wallahi taurari ne suka rikice mini har na kasa gane hanya." Abdussamadu ya amsa.
Musa ya kara tambayarsa, "To, yanzu wane wuri muke nan?"
"Wallahi ban san ko wane wuri ne ba. Ban taɓa ganin wuri mai irin wannan yanayi ba, sai fa yanzu, balle in gane inda muke."
Musa ya ce, "Ai kuwa sai mu koma da baya, mu sake ɗauko hanyarmu ta asali."
Sheikh Abdussamadu ya ce, "Ai ba zan iya gane hanyar da muka fito ba."
Musa ya ce, "Idan kuwa haka ne, to, mu ci gaba da tafiya kawai. Yalla Ubangiji ya yi mana katari da komawa kan tafarki."
MAKALOLI MASU ALAKA:
Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (1)
Karanta Kayatacciyar Hikayar Butulci Kasha Mamaki
Karanta Kayatacciyar Hikayar Ali Baba da Barayi Alba'in (1)
Don haka sai suka ci gabaa da tafiya har zuwa lokacin sallar Azahar, yayin nan suka iso ga wani fili mai faɗi. Filin nan ya milla ya tafi shantam, babu kwari ko tudu a cikinsa, kamar dai ruwan teku a lokacin da yake kwance lafiya. Daga can ƙarshen filin inda idanunsu ke iya hangowa, suka hango wani abu dogo baƙi, wanda idonsu bai shaida ko menene ba saboda nisa. Suka ga kamar wani farin hayaki na tashi daga tsakiyar wannan abu yana shiga cikin sararin samaniya.
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Fassar:
Ibrahim Malumfashi
Danladi Haruna
Bukar Mada
DUBA NA GABA: Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (3)
Za mu Ci gaba ranar Lahadi mai zuwa dai-dai wannan lokaci (ƙarfe 10:00 PM, na dare), In Sha Allah.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
0 comments:
Post a Comment