Wednesday, 11 March 2020

MENE NE TSARKI A ADDININ MUSULUNCI?

Tura Wannan Zuwa Ga
"إن الله يحب التّوّابين ويحب المتطهّرين"


Tsarki na nufin Tsafta

Amma a shari'ance tsarki na nufin tsaftace jiki daga hadasi babba da ƙarami da kuma dukkannin ƙazanta daga jikin ɗan adam da tufafinsa da wuraren yin ibadarsa.

Idan aka ce hadasi babba ana nufin: Dukkan abin da zai wajabtawa mutum yin wanka na tsarki saboda faruwarsa.

Kamar fitar maniyyi saboda jima'i ko saboda sha'awa, ko haila, ko nifasi.

Idan kuma aka ce hadasi karami ana nufin: abinda zai wajabta mutum wankewa ko goge wani sashi na daga jikin ɗan adam. Kamar fitsari, gayadi, jin rauni ko kwararar mugunya da  dai sauransu.

A lura cewa ibada bata inganta sai da tsarki.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: