Sunday, 29 March 2020

Tun Farko Laifin Ka Ne Na Fara Yin Soyayya da Irin Su

Tura Wannan Zuwa Ga
Kana neman auren yarinya tun a waje bata girmamaka kuma bata jin maganarka to ta yaya kake tunanin zaka iya sarrafata idan ta shigo gidanka?

TUN FARKO LAIFINKA NE NA FARA YIN SOYAYYA DA IRIN SU..

Marubuciya:- Nafisa Alkali Baffa

Ka yi ƙoƙarin rabata da ƙawayen banza ta ki.

Ka hanata tsayuwa da wasu samarin tayi biris da maganarka.

Idan ta nemi buƙatar kuɗi ko kace babu zata dage sai ka nemo ka bata.

Bata ɗauki danginka da abokanka da muhimmanci ba.

Zuwa gidan biki ko walima ba ya wuceta.

Ta nuna maka karatun bokonta ko kuma aikinta ya fika muhimmanci wurinta.

Bata nemanka idan taji shiru kwana biyu sai dai kai ka nemeta.

Duk lokacin da tayi maka laifi bata iya ƙasƙantar da kai ta baka haƙuri.

Dazaran kayi mata laifi bata yi maka uzuri har sai ka gayyato wasu ƙawayenta ko abokanka sun shigo ciki sannan.

Haba ranka ya daɗe! Dama ita juma'ar da zata yi kyau ai tun daga laraba ake ganeta. Haka kuma icce tun yana ɗanyensa ake ƙoƙarin tanƙwarashi.

Yarinyar bata munafunceka ba domin halayyarta a fili yake kai kaji zaka iya saboda wani dalilinka da kai kaɗai ka san abinka.

Sai ta shigo gida ka cimma burinka akanta sai ka fara tunanin ba zaka iya ɗaukar rainin hankalinta ba bayan a can baya tayi maka irinshi dubu ka shanye.

Wataƙila Ita kuma wannan haƙurin da kayi da ita tare da kawar da kai da kayi akanta shi ya sa taji zata iya aurenka tunda ka fahimceta kuma a haka kaji zaka iya aurenta.

Sai bayan aure sai kace kai ai baka san waɗannan halayyar ba dole sai dai ta canza. Kuma wai kai dole so kake ta daina su lokaci ɗaya ta dawo yadda kake sonta wallahi ba zai yiyu ba. Idan kuma ka matsa to aurenka zai mutu kuma idan haka halinka yake to zaka yi ta aure ne yana mutuwa har a fara kiranka auri saki.

Ɗan Uwa, shawarar da zan baka ita ce idan kana neman auren yarinya to tun a waje zaka yi ƙoƙarin canza mata wasu ɗabi'unta waɗanda basu yi maka ba.

Idan bata jin maganarka kuma ka kasa shawo kanta to kawai kayi haƙuri da ita ka nemi wata ka aura domin ko ka aureta ba zaka iya juyata ba. Amma idan ka san da rainin hankalinta kuma ka aureta a haka to idan ka saketa daga baya wallahi baka yi mata adalci ba.

DA FATAN MAZA ZAKU KIYAYE!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user