dattijo ya karanta musu abin da ke rubuce a jikin allon da ke kan
babban kabarin nan, suka ce a ransu, "Wannan duniya ba kome ba ce"
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
rubuta wannan sako cikin baitocin waka:
"Abin da na bari na bar shi ne ba don na so ba, na afku cikin
tafarkin da duk mai rai sai ya bi shi. Na rayu cikin taƙama da
ɗaukar kai wai ni Sarki, in harɗe bisa karaga babu mai ikon
matsowa sai ka ce zaki. Kullum ina neman tara dukiya ba na bayar
da ko dirhami, wannan da zai iya kare ni daga shiga wuta mai
kuna. Har zuwa lokacin da kibiya ta soke mini zuciya, kibiyar
mutuwa daga Allah Sarki Ubangijin duka talikai. Yayin da mutuwa
ta zo sai na kasa tsare ta, duk isata da ƙarfin iko da ƙarfin
mulkina. Askarawana na tsaye ba sa iya kare ni, balle abokai ko
iyali ko dangina. Yayin rayuwata na manta da wata abu wai ita
mutuwa, na riƙa jin daɗi ina more rayuwata. Na riƙa cika jakunkuna
da kuɗi ina kullewa, kullum burina dinari ya ƙaru a kan dinari. Daga
mai jan raƙumi sai mai haƙar kabari, su za su fara sallama a
gidana bayan fitar rayuwata. Ranar Kiyama kai kaɗai za ka tsayu a
gaban Ubangiji, daga kai sai tulin kayan da ka je da su. Kada ka yarda wannan duniya ta ruɗe ka, ka kula da makwabtanka iyalinka
da 'yan uwa."
Yayin da Musa ya ji abin da aka rubuta a jikin wannan ƙofa sai ya
some don tsoro. Bayan ya farfaɗo sai ya tashi ya buɗe ƙofar suka
shiga daga cikin rumfar sai ya ga wani kabari wanda aka yi gininsa
da tsawo duk ya kere saura. A bisa kabarin an kafa allo na ƙarfen
Siniya, Abdussamadu ya matsa kusa ga allon ya fara karanta abin
da aka rubuta:
"Da sunan Allah wanda ba ya da farko ba ya da ƙarshe. Da sunan
Allah wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, wanda bai yi
kama da kowa ba, bai yi kama da komai ba. Da sunan Allah,
Ubangiji mai girma da ɗaukaka. Da sunan Allah wanda yake
dawwamamme, mutuwa ba ta riskar sa... Ya kai wannan mutum da
ka tsinci kanka a cikin wannan fada, ga gargadi zuwa gare ka: Kada
ka shagala da al'aumurran duniya, kada ka bari daɗin cikinta ya
ruɗe ka, kada kuma ka bari wahalarta ta zautar da kai. Ka sani
daɗin duniya ba mai ɗorewa ba ne, haka ma wahalarta ba ta
ɗorewa har abada. Duk abin da ka samu a cikinta tamkar bashi ne
ka karɓo, a kowane lokaci mai bashin nan zai iya karɓe abinsa.
Abin da duk ka gani cikin duniya tamkar mafarkin mai mafarki ne,
kai, tamkar gulbin hamada ne ga mai jin ƙishirwa. Shaiɗan ke
ƙawata maka duniya, kana ganinta tamkar wata aljanna, ba tare da
ka farga ba har mutuwa ta riske ka. Kada ka yarda da duniya
domin ita budurwar wawa ce, takan ɗaga mutum sama daga ƙarshe
idan ya sakankance da ita sai ta sako shi ƙasa. Kada ka yarda da
ruɗinta kada ka yarda da zugar shaiɗani.
Misalina rayuwata kadai ya ishe ka gargadi; na mallaki garke dubu
bisa dubu na dawaki, na mallaki babbar fada. Ina da mata da sa-
daka guda dubu kyawawan gaske kamar watanni, dukkaninsu kuma
'ya'yan sarakuna ne. Ina da 'ya'ya dubu dukkaninsu zakokan yaƙi
ne. Na shekara dubu ina mulki kamar ba zan mutu ba. Na mallaki
dukiya wadda ba ta da adadi kamar ƙasa, babu wani sarki da ya
tara irin dukiyar da na tara a lokacina. Na shagala da rayuwa har
ina ganin kamar ba zan mutu ba. Kwaram, babu zato babu
tsammani sai mai katse jin daɗi ta auka mini, mai raba ɗa da
mahaifi, mai raba mata da miji, mai raba tajiri da dukiya, mai toshe
gidaje da birane, mai ɗauke babba da yaro, mai raba uwa da jariri.
Mara tausayin talaka don talaucinsa, mara tsoron sarki da tajiri don
ƙarfinsu.
Ka sani ya kai wannan mutum, mun rayu cikin wannan fada cikin
tsauraran matakan tsaro da jin daɗin rayuwa, ba mu ankara ba har
Ubangijin sammai da ƙassai ya turo mana jekadiyarsa, ita ce
mutuwa. Ta shigo ta same mu a cikin wannan fada ta riƙa daukar
mu da biyu-biyu kowace rana. Askarawa ba su tsare ta daga gare
mu ba, dukiyoyinmu ba su fanshe mu daga wurinta ba. Mutane da
yawa daga cikinmu suka mutu, muka zama tamkar muna cikin
tekun mutuwa ne. Yayin da na ga haka sai na kira mai rubutu na
umurce shi da rubuta baitoci ɗauke da gargaɗi a jikin dukkan
allunan da ka gani cikin wannan fada, domin na baya su karanta
masu hankali daga cikinsu su hankalta kafin lokaci ya ƙure musu.
Ka sani ya kai wannan mutum, na mallaki rundunoni ta sadaukai
masu ƙarfi har runduna dubu bisa dubu. Kowace runduna akwai
sadaukai dubu, mahaya dawaki, kowane sadauki ya shiga sulke da
buke da kwalkwali bisa kansa, a hannunsa na dama yana riƙe da
takobi tana walkiya, a hannunsa na hagu yana riƙe da mashi da
garkuwa, a gindinsa ya soke wuƙaƙe da kibau. Yayin da na ga
mutuwa ta far mana tana ɗaukar mu da biyu-biyu kowace rana, sai
na yi tsawa ga askarawa, "Me ya sa ba za ku yake ta ba, kuna gani
tana kashe mu ɗaya bayan ɗaya." Sai suka amsa mini, "Ta yaya za
mu yi yaƙi da hukuncin Ubangiji, wannan da yake da fada wacce ba
mai gadin ta, Sarkin da ke mulki ba tare da fadawa ba."
MAKALOLI MASU ALAKA:
Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (1)
Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (2)
Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (3)
Daga nan na ce a kawo mini dukkan dukiyata. Aka kawo mini
manya-manyan sundukai dubu bisa dubu na zinariya, da wasu dubu
bisa dubu na azurfa, da wasu dubu bisa dubu na lu'ulu'u, da wasu
dubu bisa dubu na sauran jauhari iri-iri. Aka tattaro garke-garke na
dabbobi iri daban-daban. Na ce wa askrawa, "Ku bayar da wannan
dukiya dukkanta a matsayin fansar rayuwata." Suka amsa mini, "Ba
mu da wannan iko." Na ƙara cewa, "Ku bayar da ita a ƙara mini
kwana ɗaya a duniya." Suka ce mini, "Ba mu da wannan iko. Wake
da ikon karkatar da hukuncin Ubangiji?"
Na saduda na tabbatar da ranar mutuwa askarawa ba su hanawa,
dukiya ba ta amfani, 'ya'ya ba su kare ta, abokai ba su tare ta.
Mutuwa ta ɗauke ni, na zama kaskantacce bayan a da na kasance
madaukaki a cikin jama'ata. Aka sanya ni a rami aka mayar da
kasa bisa kaina, bayan da na kasance ni ke yawo bisa kanta. Ya
kai mai karatu, ko kasan mai yi maka wannan gargadi? Ba kowa ba
ne face ni dake cikin wannan kabari. Sunana Sarki Kush dan
Sahaddadu dan Adi Babba.".
DUBA NA GABA: Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (5)
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Fassar:
Ibrahim Malumfashi
Danladi Haruna
Bukar Mada
Za mu Ci gaba ranar Asabar mai zuwa da misalin ƙarfe tara na dare (9:00pm) INSHA ALLAH.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Fassar:
Ibrahim Malumfashi
Danladi Haruna
Bukar Mada
Za mu Ci gaba ranar Asabar mai zuwa da misalin ƙarfe tara na dare (9:00pm) INSHA ALLAH.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.