Friday, 3 April 2020

Ka Tuna Da Wannan Kafin Ka Bari Rayuwar Duniya Ta Rude Ka

Tura Wannan Zuwa Ga
Kada ka bari Kyalkyalin duniya ko kuma abinda kake samu acikin ta ya ruɗe ka yasa ka manta da (LAHIRA) in da ainihin gidan ka yake.

Kada Ka Bari Wannan Tsohuwar Ta Yaudara Ka...

MarubuciIbrahim Nuhu Imam Rimi

Duniya wata tsohuwa ce Maƙaryaciya kuma Mayaudariya mai sifar tsofaffi amma kullum ado take irin na yara.

Waɗanda kyawun adon ta ya ruɗe su zato suke yi kamar zata yarda ta aure su su zauna da ita zama na har abada.

Soyayyar ta yasa sun mance da Lahira in da ainahin gidan su yake sun kauda kai daga gare ta babu mutuntawa ko kyautatawa.

Sun manta cewar wannan mayaudariyar tsohuwar tayi zamani da iyayen iyayen su tayi zamani da Kakannin kakannin su, ta samu nasara akan su da dama daga cikin su ta yaudare su ta hallakar dasu irin hallakar da babu ranar fanshewa.

Son Allah da kuma Son wannan tsohuwar mayaudariyar basu haɗuwa cikin zuciyar mutum guda kamar yadda ruwa da wuta ba zasu haɗu cikin ƙwarya guda ba.

Manzon mu (S.A.W) shine kaɗai wanda duniyar bata isa ta kai masa tallen kan ta ba kwarjinin sa yafi ƙarfin idanun ta shi kuma bai kalli in da take ba, ballan tana ya ganta.

Sahabban sa da sauran Magabata na ƙwarai, sunfi duniyar wayau da hankali idan ta miƙo musu wani abu don neman yaudarar su, su kuwa sai su karɓa su miƙa wa lahirar su da haka suka tanadar wa kan su babban masauki acan.

Mu kuwa a wannan zamanin yawancin mu neman wannan shagalalliyar tsohuwar muke yi ido rufe.

Wasu ma duniyar ta ɗauke su ta gama yaudarar su ta jefar dasu ta tsere amma sun ta shi sun bita a guje suna neman ta ko ta wane hali sai sun same ta.

'Yan ƙalilan ne daga cikin mu masu Hankali!

'Yan ƙalilan ne daga cikin mu masu Tunani!

'Yan ƙalilan ne daga cikin mu masu Sani!

'Yan ƙalilan ne daga cikin mu masu aiki na Ƙwarai!!

Ya Allah ka sanya mu cikin 'yan ƙalilan ɗin nan.

Ya Allah ka ganar damu sharrin duniya da halayen ta ka azurta mu guje mata ka yarda damu ka gafar ta mana laifukan mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user