Wednesday, 8 April 2020

Karanta Alamomin Gane Masoyi Na Gaskiya

Tura Wannan Zuwa Ga
Duk mace mai rufe jikinta, rufewa gaba ɗaya, a duk inda ta shiga, to duk wanda ya so wannan macen to ɗabi'unta ya gani ba siffar jikinta ba.


Masoyin Asali

Marubuci: Ibrahim Muhammad Abu Muh'd

An fi tsammanin soyayya ta asali a irin wannan wurin, domin ranar da ya aureta, idan ya ga siffar jikinta, sai yaji ya ƙara sonta, domin ɓoyayyen abu ya fi jan hankalin namiji.

Amma macen da ke bayyana jikinta, ko ta saka kayanda za su bayyana yadda siffar ƙirjinta ko bayanta, ko kwalliyarta suke, duk namijin da ya ganta yace yana sonta, sau da yawa wannan sha'awarta kawai ya ji, kuma idan ya aureta wata rana waɗannan siffofin dole su kau, a lokacin idonsa zai koma kan wata, domin ta gida kam
قد ذاق من غسيلتها ما ذاق

'Yar Uwata yakamata ki sani duk waɗanda kike bayyanawa jikinki duk suna ganin ƙirjinki, bayanki, kwalliyarki, waɗannan ko sunce suna sonki sha'awarki sukeji.

Musulunci ya yarda idan mutum ya zo nemanki da aure, ya kalleki babu lulluɓi.

A CIKIN GIDAN KU SAU ƊAYA BA KULLUM BA.

Akace idan ya je gidanku nemanki da aure, akace a cikin gidanku, akace sau ɗaya ba kullum ba.

Allah ya bamu Iƙon fahimtar gaskiya da aiki da Ita Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user