Monday, 6 April 2020

Karanta Kadan Daga Cikin Manyan Kurakuran Neman Aure A Wannan Zamani Da Samari Keyi

Tura Wannan Zuwa Ga
RASHIN NEMAN MAI KYAWUN DABI'AH

Babban abin da ya kamata ka fi mayar da hankali a kai shi ne, neman mace mai kyawawan ɗabi’u, wacce za ka iya zama da ita don Allah, wacce za ta kai ka tudun-mun-tsira, ba wacce za ta kama hannunka ku tsunduma cikin wuta ba.

Tun Farko Laifin Ka Ne...

Marubuci:- Kamaluddeen Kmc

YIN ƘARYA

Ƙarya tana daga cikin irin abubuwan da ke zubar da mutuncin mutum wajen wacce zai aura. Ka ga matashi yana yi wa yarinya ƙarya, ai shi mai arziki ne, idan ta aure shi ta huta. Ya riƙa karɓar aron abubuwan duniya don ya ruɗe ta. Wannan shi ne mataki na ƙarshe a rashin Wayewa, dafatan masu irin wannan halin za su faɗaka su daina.

ROWA

Dukkan mace tana son kyauta, ya zamana hannun saurayi a buɗe yake. Duk da ba a ɗora sharaɗin aure kan yin kyautar kuɗi ba, amma Manzon Allah (S.A.W) ya faɗi cewa, “Zuciya tana jawuwa bisa son wanda yake kyautata mata, sannan tana ƙin wanda ya munana mata”. Kenan ashe kyauta za ta iya taka muhimmiyar rawa a wajen neman aure.

Sau tari wasu mazan sukan gabaci mace, su riƙa nuna tsanin wayewarsu ta zamani. A ganinsu wannan ne dalilin da zai sa su karɓu wajen Mace. Sannan a hakan kuma saboda rashin wayewar tasu, babu abin da za su fi mayar da hankali a kai illah neman wacce wai take da wayewar Zamani.

JAHILCI

Jahilci na daga cikin abin da ke sawa ka samu matsala da wadda kake nema, musamman ma idan ta gano kai jahili ne, to ai ka gama yawo! Don Mace na son namiji mai ilimi duka biyu, wannan zai sa ta soka.

KAZANTA

Tana daga cikin abubuwan dake sa ka rasa ƙima a wajen Mace saboda gaskiya mata na da tsabta yadda ya kamata, saboda haka ba sa son namiji ƙazami. Abin alfaharin Mace ne ta nuna ka a gaban ƙawayenta ka yi wanka mai kyau, ka haɗu!

SHISHSHIGI

Yana ɗaya daga cikin kuskuren da maza ke tafkawa wajen matar da zasu aura. Ka ga namiji ya fiye tambayoyi ko kan halin gidansu , mahaifiyarta mahaifinta, ko ya dinga yi mata tambayoyin da ba su zama dole ba.

Lallai wannan na saka ka rasa ƙimarka wajen macen da za ka aura. Binciken halayen gidan su ba laifi bane, amma tsananta binciken ne laifi. Domin duk wanda aka tsananta masa bincike to ba zaiyi wahala yatsira koda kuwa a lahira ne.

Waɗannan kurakuren na taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen aboki ko abokiyar zama. Da fatan za mu amfana.

Allah ta'ala yaƙara shiryamu baki ɗaya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user