Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Ashe wani dogon gini ne mai girma sai ka ce dutse, ginin an yi shi ne da baƙaƙen duwatsu aka shata siffarsa kamar fadar wani sarki. Ƙofar ginin ta ƙarfen Sin ce an goge ta da azurfa tana ta ƙyallin kashe ido. Daga jikin ƙofar shiga fadar an yi matattakalai kamar dubu waɗanda za a taka zuwa ƙololuwar ginin. Abin nan da suka ga yana tashi kamar hayaƙi daga nesa, ashe hasken kubbar da ke tsakiyar ginin ce da ke can ƙololuwarsa wadda aka yi da zinariya. Wannan kubba ita ce kamar hula ga ginin, tsawo da girmanta zira'i ɗari ne.
Musa ya yi mamaki matuƙar mamaki da ganin wannan gini a cikin dajin da babu kowa. Bayan Sheikh Abdussamadu ya ƙare wa ginin nan kallo, sai fuskarsa ta washe da farin ciki ya ce, "Babu Sarki sai Allah, babu shakka Annabi Muhammadu Manzonsa ne."
Musa ya dubi Abdussamadu ya ce, "Ya Sheik na ga fuskarka ta cika da farin ciki, me ka gani ne?"
Abdussamadu ya amsa, "Ya kai Wakilin Halifa, ka yi murna domin kuwa Allah ya tausaya mana, ya taƙaita mana wahala. Ka ga wannan wuri kusa yake da Birnin Tagulla. Daga Birnin Tagulla kuwa zuwa ga dutsen nan na baƙaƙen mutane tafiyar wata biyu ce."
"Ya aka yi ka san haka, ya Sheik?" Musa ya tambaye shi.
Abdussamadu ya ce, "Mahaifina ya taba gaya mini cewa mahaifinsa ya ba shi labari ya ce, wata rana suna tafiya sai makuwa ta kama su suka faɗo wannan wuri, daga nan sai ga su a Birnin Tagulla. Ya ce daga birnin zuwa dutsen baƙaƙen mutanen nan tafiyar wata biyu ce cif. Akwai hanya wadda ake bi daga rabin teku, a bisa hanyar akwai rijiyoyin ruwa domin sha da kuma wuraren yada zango. An ce waɗannan rijiyoyi da wuraren yada zango Shugaba Zurkallaini Askandariya ne ya gina su. Wai wata rana ne da ya fito da runduna tasa za su yaƙi a ƙasar Muritaniya sai ya ga hanyar duk hamada, babu ruwan sha. Shi ne ya giggina rijiyoyi da zanguna domin hutawar masu bi ga hanyar. Har yanzu kuwa rijiyoyi da zangunan na nan."
"Ya Sheik, Wallahi Allah ya hore maka ilmi," in ji Musa.
Abdussamadu ya ce, "Mu je ga wancan gini mu gani, domin shi gargadi ne ga masu hankali."
Musa da Abdussamadu da mutanensu suka nufi wurin wannan gini, suka tarar da ƙofarsa a buɗe. A jikin ƙofar an kafe wani allo da aka yi wa rubutu irin na Yunaniya, rubutun an yi shi da ruwan zinariya. Abdussamadu ya fara karanta baitocin da aka rubuta a jikin allo:
"Ka duba alamu na ƙarfinsu ne,
Da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai duka sun mace.
Kai mai karatu a nan gun tsaye,
Ka dubi sadaukan ga duk sun wuce.
Shiga daga ciki ka ɗau darasi,
Na mazan jiyan nan da duk sun mace.
Mutuwa ta riske su babu shiri,
Ta murɗe ta watsar kamar dai a ce.
Ba su taka doro na wannan ƙasa ba,
Kamar masu cin kasuwa sun wuce."
Yayin da Sarki Musu ya ji abin da aka rubuta ga wannan allo sai zuciyarsa ta yi taushi, har ƙwalla ta zubo masa don tausayi, ya dubi Abdussamadu da jama'a tasa ya ce, "Babu Sarki sai Allah wanda yake dawwamamme ba ya mutuwa har abada." Daga nan sai ya shiga cikin wannan fada, ya yi mamaki da irin kyawunta da kuma yadda aka ƙawata ta. Ya yi ta zagayawa cikinta yana kallon abubuwan mamaki har ya zo ga wata ƙofa, ita ma an kafa allo a jikinta rubutacce. Ya umurci Abdussamadu ya karanta masa abin da aka rubuta. Abdussamadu ya karanta kamar haka:
"A cikin wannan fada mutum nawa ne kake tsammani sun rayu kuma sun mace. Yi ƙoƙari ka bar wa 'yan baya abin gani, lokaci ba ya jira kafin ka farga ya tafi. Sun ji daɗi sun mori rayuwarsu cikin duniya, mutuwa ta ɗauke su ta maishe su ƙasa. Sun ci sun sha mai kyau lokacin rayuwa, sun mutu sun ruɓe sun zan abincin tsutsa."
Yayin da Musa ya ji abin da ke rubuce a jikin wannan ƙofa sai hankalinsa ya ƙara tashi, hasken da ke fuskarsa ya gushe, hawaye ya yi ta zuba daga idanunsa kamar ruwa. Ya dubi mutanensa ya ce, "Haƙiƙa Allah ya halicce mu domin wani sha'ani babba!" Suka ci gaba da zagayawa cikin wannan fada, amma ba su ga wani abu mai rai ba, ko kiyashi babu. Da suka zo tsakiyar wanna fada sai suka iske wata babbar rumfa wadda aka yi rufinta da siffar kubba. An zagayeta da 'yar ƙaramar katanga ginin dutse, tsawon katangar bai wuce zuwa gwiwar mutum ba. Akwai ƙofofi har guda takwas na shiga cikin wannan rumfa, kowace ƙofa an yi ta ne da sandunan sandal an kafe ta da madaurai na zinariya da azurfa. A cikin wannan rumfa kuma an jera kaburbura har guda arbamiyya. Dukkan kaburburan ginannu ne da duwatsu masu launin rawaya.
Sarki Musa ya matsa kusa ga waɗannan kaburbura, sai ya hangi wani kabari a tsakiyarsu wanda ya fi duk sauran girma, an kuma ƙawata shi fiye da saura. A bisa kabarin akwai wani babban allo na farin dutse, an yi rubutu bisa ga allon:
"Yaƙi nawa na yi? Askarwa nawa na kashe? Sau nawa na yi nasara? Sau nawa na faɗi? Wane irin abinci ne ban ci ba? Wane irin abin sha ne ban sha ba? Wace irin waƙa ce ban ji ba? Wace irin rawa ce ban gani ba? Waɗanne irin mata ne ban mallaka ba? Sau nawa ina yin umurni? Sau nawa ina yin hani? Fadoji nawa na mallaka? Gidaje fa, su ma nawa na mallaka? Na rusa birane na tara bayi da kuyangi, a cikin fadata suke duk zagaye da bangaye. Wannan duk a cikin jahilcina ne domin neman mulki da son tara dukiya. Ka yi tunani ya kai ɗan Adamu mai hankali, kar ka manta dole za ka sha daga kaskon mutuwa. Tana nan kusa tamkar ƙurar nan da ke kanka, kwaram ba zato ba tsammani sai dai ka ji ka a rami."
MAKALOLI MASU ALAKA:
Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (1)
Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (2)
KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN
Sarki Musa da mutanensa suka yi kuka, kuka mai yawa, yayin da dattijo ya karanta musu abin da ke rubuce a jikin allon da ke kan babban kabarin nan, suka ce a ransu, "Wannan duniya ba kome ba ce." Suka matsa ga rumfar nan, sai suka ga a jikin ƙofa ta farko an rubuta wani sako cikin baitocin waƙa.
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Fassar:
Ibrahim Malumfashi
Danladi Haruna
Bukar Mada
DUBA NA GABA: Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (4)
Za mu Ci gaba ranar Asabar mai zuwa da misalin ƙarfe tara na dare (9:00pm) INSHA ALLAH.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.