A shafin facebook akwai wani abu da suka ɓullo da shi mai suna 'MEMORIES' wanda duk wani ma'abocin rubuta maƙala a kan shafin zai ga yana cikin zaman sa ba zato ba tsammani suna tura masa cewa: "We care about you and your memories", wanda shi kuma ba ya yin maƙala, idan ya danna maɓallin 'MENU' a ƙarƙashin sa zai ga wani maɓallin da aka rubuta 'ON THIS DAY' to anan wannan memories ɗin yake.
Nazari Aikin Mai Hankali...
Manufar sa ita ce tuna maka wani abu da ka yi a irin wannan ranar a shekarar data gabata ko kuma wasu shekaru da suka gabata, wani abin ma ka daɗe da mantawa dashi kwatsam sai kaga sun kawo maka shi.
Daga cikin irin waɗannan abubuwa da suke tuna maka abubuwa ne masu taɓa zuciya ƙwarai, wani ya sanya maka farin ciki, wani kuma ya sanya maka baƙin ciki, damuwa da takaici, wani kuwa mamaki da al'ajabi zai baka tare da tunanin wane dalili ne ma yasa ka yi shi a ya yin da baka iya tunawa don ka manta saboda daɗewar lokacin faruwar sa.
Shin wai kuwa Ka taɓa zama ka zurfafa tunanin ka akan cewa wannan abin da shafin facebook ya ɓullo dashi akwai wani darasi babba aciki abin lura da zai dawo dakai cikin nutsuwa da hayyacin ka?
To a taƙaicen taƙaitawa idan baka taɓa yi ba, ko kuma ka taɓa amma baka iya gano darasin ba to ka saurare ni da kyau akwai babban darasi abin lura da wannan shafi yake koyar dakai.
DARASIN KUWA SHINE "TASHIN ALQIYAMA DA KUMA HISABI!"
To fa kaga shi facebook abin da yake tuna maka duka bai fi na 'yan shekaru kaɗan ba amma kana mantawa da lokacin da kayi abin, to kuma ina ga ran da za a yi maka tariyar duk wani abu daka aikata a rayuwar ka baki ɗaya?
Sannan kada ka yi mamaki cewa shafin facebook ai ba dan addinin ka ya ƙirƙire shi ba kuma ba addini yake wa aiki ba don haka ta yaya za'a ce yana bayar da darasi mai kamanceceniya da tashin alƙiyama da kuma hisabi?
To anan amsar itace: "Shi Allah Ubangiji ne ga dukkan komai kuma mai rinjaye ne a kan dukkan komi, komai da kake gani a ƙarƙashin ikon sa yake kuma yana bauta masa ta hanyar daya sani ko ta wacce bai sani ba, akan yana so ko akan tilas, to hatta mai shafin facebook da shafin nasa a ƙarƙashin rinjayen Ubangiji suke shi yasa ma har ga shi nan kullum sai sun tunatar da bayin sa cewa akwai wata rana da za tazo musu irin wannan da za'a bijiro musu da ayyukan su da suka gabatar kamar haka don haka su shiryawa zuwan ta."
Babban abinda zai tabbatar maka da haka shine wata Ayah acikin AL-KUR'ANI da Allah ke cewa: "YAUMA YATAZAKKARUL INSANU MA SA-AA".
Wato akwai wata: "Ranar da mutum zai tuna abinda ya aikata." na ayyuka da shi ya riga ya manta ya aikata su saidai an taskance su awajen Allah acikin littafin sa wanda a wannan ranar zai gansu da idon sa ya tuna su sannan ya karanta littafin da kan sa yana faɗar duk abinda ya aikata a bainar taron alƙiyama kuma kowa sai ya ji.
Kaga ashe wancan abin da shafin facebook yake maka babbar tunatarwa ce game da abinda ke tafe gaba gare ka ko ba daɗe ko ba jima babu makawa.
Sannan har ila yau daga cikin irin waɗannan memories ɗin da shafin facebook kan nuna maka idan ka lura da kyau zaka ga sun rubuta cewa: 'ONLY YOU CAN SEE THIS'... (Wato kai kaɗai ne zaka iya ganin wannan abin).
Acan ƙasa kuma sai a sa 'SHARE'... Wato idan kana so wasu su gani sai ka raba musu su gani.
Shin shi ma wannan ɗin ko ka san akwai wani darasin abin lura aciki kuwa?
Idan baka iya ganowa ba to lallai da akwai! Darasin kuwa shine kamar haka:
Idan ka aikata aiki mai kyau to ba zaka taɓa jin wani ɗar ba don wanin ka ya gani ko ya sani, amma idan mumman aiki ne fa kana so wani ya sani? Amsar itace A'a, don ɓoyewa ma zaka riƙa yi.
To kuma dukkan wani ɗan Adam mai kuskure ne kamar yadda Annabi (S.A.W) ya faɗa acikin hadisi, to kuma bayan kuskure akwai tuba, inda su kuma Annabi (S.A.W) yace fiyayyu acikin masu kuskuren 'ya'yan Adam sune masu yawan tuba.
To shi kuskure aikata shi ba shine ke halakarwa ba, yin girman kai da ƙin tuba shi yake halakarwa kamar yadda in muka lura tsakanin Annabi Adam (A.S) da Shaiɗan (L.a) duka sun saɓa.
Shi Annabi Adam (A.S) ance kada ya aikata kaza sai ya aikata.
Shi kuma Shaiɗan (L.a) ance ya aikata kaza sai ya ƙi aikatawa, kunga anan duka sun saɓa umarni.
To amma bambamcin dake tsakanin Annabi Adam (A.s) da Shaiɗan (L.a) shine:
Shi Annabi Adam (A.s) bayan ya saɓa sai yayi nadama ya kuma tuba zuwa ga Ubangijin sa, sai aka gafar ta masa aka yafe masa laifin sa aka ɗaukaka darajar sa.
Shi kuwa Shaiɗan (L.a) sai yayi girman kai ya ƙi tuba, sai aka tsine masa, aka kore shi daga rahmar Allah, aka ƙasƙanta darajar sa.
To hakanan kai ma matsawar kana nadama da tuba daga laifukan ka to ana sa ran Ubangiji cikin afuwar sa da yalwar rahmar sa zai gafarta maka ya kuma suturce sauran bayin sa daga ganin ayyukan saɓon ka saboda faɗar Manzon Allah (S.A.W) acikin hadisin Abdullahi bn Umar (r.a) cewa: "Lallai Allah mai girma da ɗaukaka zai kusanto da mumini a ranar alƙiyama, sai ya sanya masa sutura ya kange shi daga sauran mutane, sai yace (dashi): bawa na! Ka san zunubi kaza da kaza? (daka aikata).
Sai (bawan) yace: Eh Ubangiji (na sani)!
Har sai ya tabbatar masa da zunuban sa, har bawan ya tabbar cewa lallai ya halaka, Sai Ubangiji yace: Haƙiƙa Ni na suturta maka su a duniya, kuma a yau na gafarta maka su, Yace: sai a mika masa littafin sa na hisabi (a hannun dama).
Amma kuwa shi kafiri da munafiƙi, za'a kirasu a tsakar bainar jama'a sai masu yin shaida su riƙa cewa: waɗannan su ne waɗanda su ka yi ƙarya wa Ubangijin su, ku saurara; tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai."
Duk wanda Allah ya tsine masa kuwa to baida wata makoma in ba wuta ba.
To anan darasin da shafin facebook yake nuna mana abin lura shine a dai dai sanda ya bijiro maka da wani abu da ka taɓa yi, sannan ya rubuta maka cewa "ONLY YOU CAN SEE THIS' to yana fa tuna maka cewa kamar yadda wancan hadisin ya faɗa to akwai fa wata rana da Allah zai keɓe wasu bayi nasa masu tuba daga laifukan su ya suturce aibin su daga sauran halittun dake filin alƙiyama ya zamo babu mai ganin abinda aka yi sannan ya gafarta musu ya kuma shigar dasu aljannah.
Sannan kuma a gefe guda akwai waɗanda za'a fallasa su a bainar taron alƙiyama daga ƙarshe a bisu da tsinuwar Allah zuwa wuta.
Saboda haka babbar mafita itace kayi ƙoƙarin aikata aikin da in aka bijiro maka dashi a ranar alƙiyama ganin sa zai faranta ran ka, ba wanda zai baƙan ta ranka yayi maka jagora zuwa wuta ba.
Saboda haka acikin dukkan komai da kake gani akwai ayah da hikima ta Ubangiji amma ga ma'abota hankali da tunani, su ne suke tsayawa su yi tunani cikin abubuwa na halittun Allah su gano ababen da kan ƙarawa imanin su ƙarfi da tabbata kamar yadda Ubangiji (SWT) ya faɗa a wata Aya cikin suratu Al-imran cewa: "Lallai acikin halittar sammai da ƙassai da saɓawar dare da yini wallahi akwai ayoyi ga masu hankali. Sune waɗanan da suke tuna Allah a tsaye da zaune da kwance kuma suke tunani acikin halittar sammai da ƙassai (suna cewa) ya Ubangijin mu baka halitta waɗannan don wasa ba tsarki ya tabbata gareka ka tsare mu azabar wuta."
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.