Dama Ce A Gare Ka...
Karƙashin ayoyinnan na suratu zumar tun daga inda ubangiji yake cewa manzonsa (S.A.W);
"Kace ya ku bayina da suke tafka mummunar ɓarna a rayuwarsu, kada ku cire rai daga rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubi bakiɗaya, Allah mai gafarane kuma mai rahama" har zuwa ƙarshen ayoyin.
Ya ƴan uwa a duk lokacin da muka tsinci kanmu a halin wata jarrabawa kwatankwacin ko irin wadda wannan 'yar dirama ta faɗa (MARYAM BOOTH), maimakon muyi ƙoƙarin kare kanmu ko gamsar da ƴan uwanmu mutane waɗanda suma ba ma'asumai bane, kamata yayi muyi ƙoƙarin neman gafarar Allah da yardarsa domin itace kaɗai hanyar da zamu tsira anan duniya da kuma gobe ƙiyama.
Idan mun haɗu da Allah, muna roƙon Allah ya gafarta mana zunubanmu ya lulluɓe mu da rufin asirinsa da rahamarsa Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.