Malamai sun yi saɓani game da lokacin da aka wajabta Zakka, waɗansu sun ce an wajabta ta ne a Makka, saboda ayoyin Makka waɗanda suka yi magana a kanta, wasu kuma suka ce an wajabta ta ne a Madina, saboda ayoyin Madina sun fi bayyana wajabcin ta.
Bayar da Taimakon Ka Ga Mai Neman Taimako...
Masu magana ta biyu sun fi kawo
hujja mai ƙarfi, Inda suka ce musulmi a Makka daidaiwa ne, basu da tsari zartacce, ba su da hukuma, Ita kanta Zakkar ma ba ta da tsari wannan lokacin, watau ba ta da nisabi, ba a kuma ayyana waɗanda za a bai wa ba, don haka maganar da ta fi
rinjaye ita ce, an wajabta
Zakka ne a Madina, a shekara ta biyu bayan
Hijira.
(Duba fiKhuz Zakkat na Dr. Yusuful Kardawi, Juz’I na 1 sh:52-62.)
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.