Monday, 29 June 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (23) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
ƊABI'UN WASU

Haka Allah ke yin wasu sai dai ka yi haƙuri da su ba za ka iya canja su ba, amma kai da jinsu ka san akwai matsala, ba za mu ce ba za su ci nasara a rayuwarsu ba, amma tsakani da Allah ba sa jin daɗin nasarar koda sun same ta, misali: In mutum ya shiga neman aure zai taras da wasu ko sun cimmasa, wanda Allah ya ba wa nasara shi zai aura kansu, ƙalu-balen ya rage ga yadda za a zauna da matar, in suka zauna shiru cikin son juna ya yi nasara, in gidan ya koma fagen yaƙin basasa to bai yi nasara a auren ba tunda har lokacin zuciyarta na wani wuri akwai yuwuwar koma masa, kuma kwanciyar hankalin da ake nema ba zai samu ba.

Haka Allah ke yin wasu sai dai ka yi haƙuri da su...

MarubuciBaban Manar Alkasim

Kai oga a kamfani ko kanti ko gidan haya ka sani fa cewa wanda yake kawo maka kuɗin nan ba wani ƙarfin da kake da shi wanda ba shi da shi, amma Allah ya ba ka nasara a hannunka wanda shi bai da ita, kasancewarta a hannunka shi ya sa komai ya samu zai ba ka, sai dai ka gutsura ka ba shi, don haka ka lura da hidimar da yake yi maka ka yi haƙuri, na ga wani yaro sai buɗe wa wani tsoho wuta yake yi, yana ta zage-zage, amma tsohon ya sunkuyar da kai ƙasa ya kasa cewa komai, laifinsa ya yi barci a wurin aiki matar gida ta dawo ta yi ta horn bai sani ba.

Sai da suka wuce sannan baba ya fara magana a hankali yana cewa "Sai haƙuri Alhaji, wallah barcinnan bai jima da ɗauke ni ba, ba ma iya runtsawa da daddare saboda gudun sakaci a aiki" a ganina zai iya jawo hankalin baba ba tare da ya buɗe masa wuta ba, nan gaba ko dai ya kori shi a dalilin ɓacin rai ko baban ya haƙura, amma saboda sanin ɗabi'arsa baba ya ja bakinsa, yanzu nasara ake nema har a wurin aiki, musayar yawu ko ban haƙuri zai iya sawa a kore shi.

Kar ka taɓa azawa cewa masu irin wannan bala'in ransu na yi musu daɗi ne a lokacin da suke zage-zage, ai ba sa iyawa sai hankali ya tashi rai ya ɓaci, kenan zafin da za ka ji a lokacin da suke wulaƙanta ka su ma fa suna ji, sai dai ƙila nasu yakan ɗan yi saurin sauka kafin su ƙara yi da wani, duk wanda hakan ta zamar masa ɗabi'a ba ka da yadda za ka yi da shi, sanya nasara a gabanka, ka mai da ƙalu-bale baya, ka yi ƙoƙari cimma burinka, ba wani amfani ga yin faɗa da maigida ko musayar yawu.

Shi ma maigidan ya yi ƙoƙari ya duba al'amarinsa, in ya ga ya saki mace ɗaya, ya ƙara sakin wata, ko in maigida ya kori ma'aikaci ɗaya, ya sake iza ƙeyar wani lallai ya gane cewa ko ɓera na da sata to fa daddawa ma na da wari, da wahala a ce sam shi ba ya laifi sai wani, a kullum shi ne mai gaskiya, akwai mazan da ba su taɓa rabuwa da matansu ba, kullum cikin soyayya, kamar yadda ake samun ogogin da ba su taɓa korar kowa ba, ma'aikaci ko masu zaman haya kullum yabonsu suke yi.

Wanda ya ga ya mallaki komai amma koda yaushe yana cikin ƙunci sai faɗa da mutane to ya yi ƙoƙarin yaƙar abinda ke damunsa kar ya hana shi cin nasara, na taɓa barin gidan haya saboda masifar maigidan, kana gidan haya ne amma ba ka da ikon ka yi baƙi, kuma matarka ba ta isa ta yi hurɗa da wata matar ba, mutum uku sun bar gidan a gabana, ni ma a dole na haƙura na naɗe kayana na ƙara gaba, ban jima da barin gidan ba aka ce wasu mutum uku su ma sun ƙara gaba, cikinsu har da wanda ya zauna a ɗakina, watansa biyu kacal, mai gida na ta fuskantar matsaloli a lamuran sana'arta ta kasa gyarawa.

KAI MA ZA KA IYA

Me ke kawo mutuwar zuciya? Ko na ce shekararka nawa kana karen mota, shekara goma? Me ya hana ka zama direba? A shekarun da ka ɓata ɗin nan ka mallaki motar kanka kuwa? Amsar dai karen mota ne har yanzu, kuma bai ma gwanance a tuƙin ba, bai kuma roƙi wani ya koya masa ba, kenan bai yi tunanin zai iya zama direban ba, ya yanke ƙauna da cin nasara a rayuwa, in ba haka ba, akwai makarantun koyon tuƙi mai zai hana ya shiga wata makaranta? Ko yana jira ne ogansa ya koya masa, to in kuma ogan ya fi jin daɗin aiki tare da shi zai yi wahala ya so rabuwarsu, ya gwammace ya yi ta ƙara masa kuɗi don ya riƙe shi.

Ni gaskiya na fi ganin laifin direban saboda rashin motsawa, in kana haya ne  ai kana son ci-gaba me kake yi ba ka hau kan hanya ba? In haya kake yi me ka yi don ganin ka mallaki gidanka na kanka, wataƙila ma ka gina wasu ka zuba masu hayan? Akan sami masu karɓar mota a wurin direba su farauto masa fasinjoji su kawo masa, shi mai nemo fasinjojin mai ya hana shi samun motar da zai riƙa da tuƙar fasinjojin da kansa? Meye bai sani ba? Masu ba da motocin a yi musu haya ko tuƙin, ko garuruwan da za a riƙa kai fasinjoji? Jiya ake gaya min wani shahararren likitan fiɗa a Kano wanda aikinsa na farko shi ne miƙa wa likita kayan fiɗar, amma yanzu ya zama babba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (20) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (21) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (22) Cikin Sauki

A dai-dai wannan lokacin na tuna wani babban hakimi wanda na san shi lokacin da yake masinja, yanzu ga shi ya zama babba, duk wani da ka sani ya ci nasara a rayuwarsa akwai hanyoyin da ya bi, akwai wanda ya ce min yana sha'awar siyar da filaye ne, na ce ba zai iya ba, ya ce don me? Na ce ko masu sana'ar bai sani ba bare ya san ta inda zai ɓullo mata, nan take ya lissafo min kusan mutum biyar, na ce ka taɓa zama ko hira da ɗayansu? Ya ce a'a, na ce wurina za ka zo kana hirar bayan kana sane da cewa banda wata masaniya da mai sana'ar ma bare na ba ka shawarar da za ta taimake ka? Abinda zan iya kenan na karya maka gwiwa kuma na kusa yi ɗin.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user