RUWAN DA AKE TSARKI DASHI
Amma idan aka ɗebo ruwa daga kogi ko rijiya ko famfo sai aka ji yana wari to wannan ba za'ai tsarki da shi ba, ba za'a yi alwala da shi ba, ba za'ai Wanka dashi ba.
Haka ma ba za'ayi tsarki da ruwan da wani abu mai tsarki ya canza ɗanɗanonsa da kamanninsa ba, kamar ruwan da aka zuba koko a ciki ko nono ko zuma, da makamantansu, shi wannan ruwan sai dai ayi amfani dashi a abinci, amma ba za'ai amfani dashi a ibada ba.
Amma duk ruwan da najasa ta canza kamar fitsari ko kashi suka zubu a ciki to ba za'ai amfani dashi ba, ta kowace fuska.
Idan ruwa ya zama ɗan kaɗanne sai najasa 'yar kaɗan ta zubu a ciki, to ta rabashi da tsarki koda kuwa siffofinsa guda uku da aka ambata a baya basu canza ba.
Amma idan ruwa mai yawa kamar cikin duro sai najasa 'yar kaɗan ta zubu a ciki kamar ɗigon fitsari, to bata rabashi da tsarki ba.