ME KASANI GAME DA KYANKYASO...
1. Haƙiƙa kyankyaso yana cikin tsofin halittu wanda suka jima a duniya sosai, domin bincike ya gano cewa kyankyaso yajima a duniya tin zamanin dinosour (shekaru sama da dubu ɗaruruwa).
Wasu masana kimiya suna ganin kyankyaso a matsayin yajima a duniya sama da dinosours.
2. Aƙalla akwai nau'ikan kyankyaso (species) sama da 4,000 a duniya.
3. Kyankyaso yana iya kwana 30 (month) batare da yaci abinci ba.
4. Yana iya yin sati biyu batare da yasha ruwa ba.
5. Idan ka cire ma Kyankyaso kai (Head), to yana iya kwana bakwai batareda ya mutu ba.
6. Wasu daga cikin matan kyankyaso idan namijin kyankyaso yabisu (ya barbaresu) sau ɗaya to har su mutu sun riƙa yin koyi (Kwai) kenan batare da sun buƙaci namiji ba.
7. Ɗan adam bazai iyayin minti biyu batareda yayi numfashi ba, idan ɗan adam ya ɗauke numfashin sa na minti biyu batare da yayi numfashi ba to zai iya suma koma ya mutu baki ɗaya.
ME KASANI GAME DA KYANKYASO...
Amma shi Kyankyaso yana iya ɗauke numfashin sa na tsawon minti 40 batareda ya mutu ba.
8. Kyankyason da aka haifeshi a yau, a yau ɗin zai iyayin gudu sosai kamar babban kyankyaso.
9. Kyankyaso zai iyayin gudun kilo meter shida (3 mile) acikin awa guda.
10. Wasu nau'ikan kyankyaso a amurka ansame su suna matuƙar son shan giya.
11. Wasu Kyankyason suna iya gama girman su daga haihuwar su zuwa girman su a cikin kwanaki 36.
12. Kyankyason da yafi kowanne kyankyaso girma a duniya ansameshi yanada tsawon 6 inches (aƙalla rabin ruler irin na plastic ɗin nan kona katakon na wanda ake samu acikin math set).
13. Masana kimiya sunce, shi kyankyaso yana iya cin komai, shiyasa baya rasa abinci, yana cin ciyawa, ƙasa, da duk wani abinda ɗan adam ke ci.
Allah shine mafi sani.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng