KIN BIYAN BASHI BABBAN BALA'I NE!
Marubuci: Abbati Mai Shago Flg
Wasu kuwa ba sa jin tsoron cinye ƙananan kuɗaɗen da aka biyo su ta hanyar siyayyar da suka yi ko siyayyar da aka yi a wajensu, in aka biyo su wani kuɗi sai a amince musu da sunan za su bayar saboda mutumcinsu da ake gani, ashe ba haka abin yake ba sai su yi fuska su ƙi biya. Matsalar nan ma ba ta taƙaita ga manya kaɗai ba har zuwa yara; abin ban haushi sai ka jawo yara jikinka da sunan koya musu sana'a wacce za su riƙa samun kuɗin shiga tun kafin su girma ƙarshe sai su cuce ka.
Wasu manyan cuta a kan kuɗi haka ma wasu yaran, wannan ya sa tsoro ya shiga zuciyar masu abin hannu a kan in suka ɗora wasu a kan dukiyarsu za su wulaƙanta musu ita, hakan ya sa suka ƙi ɗorawa gudun kada a banzantar musu da abin da suka sha wahala wajen tarawa. Amma shawarata ga mutane masu abin hannu su yi haƙuri su nemi nagartattun mutane su ɗora su a kan kasuwancinsu, su koya musu yadda za su dogara da kansu ko su ba su jari.
In ka zama dalilin arzikin wani ba ka san iya ladan da za ka samu ba a wajen Allah, lallai akwai mutanen kirki waɗanda babu ruwansu da abin da ba nasu ba, suna tsayawa tsayin daka wajen kulawa da duk abin da aka ɗora su a kansa, ba su san ha'inci ba, ba su san mugunta ba, ba su san cin amana ba, abinda su sani kaɗai a nan shi ne ba a yi wa mutane jam'i duk lalacewarsu domin kuwa tabbas sai an sami na kirki a cikinsu.
Ka'ida ta ƙarshe; duk wanda ya ci kuɗin da ba nashi ba sai ya biya a ranar da ba shi da abin biya sai kyakkyawan aikinsa, zai kuma riƙa gamuwa da bala'i kala daban-daban a cikin kabarinsa tun kafin a tashe shi ranar biya, wannan ƙa'idar ce za ta tabbatar maka da cewa cin dukiyar mutane ba abin yi ba ne ga musulmi na ƙwarai!
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.
Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng